CHAPTER ONE.

4.2K 382 4
                                    

Zeenarth's POV.

Zeena! Zeena!! Zeena!!! Wai kima inane, inata faman kiran ki kin min baza!!! Maza ki fito kizo kikai markaden wakennan kafin ranki ya baci,. Innan zeenarth ke ta faman kwada mata kira....

Zeena tace: Inna ganinan fitowa fa!!! Kayan ne yaki shigana wlh...

Inna tace: to dole ne sai wannan din kadai zakisa, bafa nason shiririta, kin fito ne ko sai na karaso dakin nan...

Zeena ce tafito sanye da riga da skirt na atamfa, Kayan duk sun kode gashi ya mata kadan sosai, hanunta rike da dark green hijam, shima duk tsakiyar kan sa ya koke ya yi fari sabida kodewar da yayi..
Tace: Inna ganinan nafito fa dan Allah kiyi hakuri...

Inna ta kalle ta sama da kasa taga yadda kayan jikin tan ya matse ta sosai saka makon jimawar da sukayi a duniya har ya fara dan gale mata sosai, nan take tausayin tilon yar tata ya kara kamata.
Inna tace: maza dauki waken nan ki kai gidan kulu, kice mata tayi mana yauma sai ta daura kudin akan bashin sauran da take binmu, sannan kice mata ina gaisheta da jiki...

Zeena tace: to Inna, sannan ta sanya hijabin ta wanda ya sauka mata har kasa ta dauki bokitin markaden waken suyan da Inna ke awaran dare dashi na sayar wa, ta fita...

Zeenarth yarinya ce duguwa siririya, tanada kiran jiki mai kyau sosai dan zubin Coca-Cola gareta. Fara ce, mai dogon hanchi wanda ya sauko har saman bakin ta, tanada kyau daidai misali, sannan Tana da gashi irin nasu na Fulani wanda yazubo har gadon bayanta, long story short zeenarth dai mai kyauce son kowa kin wanda yarasa..

Zeenarth yarinya ce yar kimanin shakara sha 17yrs, tana ss2 a makarantar secondary na mata dake nan garin Kano, Zeena yarinya ce mai hazaka da kwazo, Allah ya bata baiwar daukan abu da sauri, komai ka nuna mata ko ka koya mata to kafin kace me ta haddace she ta iya, hakan yasa ake ji da ita sosai a school dinsu, da ma unguwar su. Duk inda Zeena ta zauna to tabbas kafin ta tashi sai tayi masoya sosai a wajen, sabida hankali da basirar ta uwa uba kyau, yarinya ce mai saurin tsayawa da shiga rai...

Akullum Zeena burinta shine tayi karatu ta sami aiki domin ta tallafawa innan ta... Zeena yarinya ce mai son gayu, da kwalliya, hakan yasa ta keson duk wani dan gaye, ta kuma ci alwashin in ta kammala makaranta to zata nemi ko aikatau ne domin ta samu daman karantar dream course din ta wato fashion design, dan babban burinta shine ta zama cikakkiyar fashion designer, don tayi aiki a babban company'n nan wadda ya shahara a garin Kano dama kasa she daban daban, wato "A. A. Fashion design Empire". Tajima tana mafarkin kanta a matsayin ma aekaciya a company din. A kullum Addu'ar tashine Allah ya bata ikon kammala karatun ta...

Sallama ta yi hade da shiga wani dan akurkin gida wanda baifi fadin daki daya ba, kulu dake zaune a kofar dakin ta, ta amsa mata hade da fadin a'a zenatu kece?.

Zeena tace Eh nice baba kulu, nakawo markaden wake ne...

Kulu tace to sannu ajiyeshi nan mazaki je ki leka waje ki kiramin idi yazo yamiki...

Bayan an mata markaden tafito gidan kulu dauke da roban waken a kai, ta nufi hanyar gida, tafiya take ta hango wata budurwa tasha ado ta sanya doguwar riga na atamfa kayan yayi matuwar kyau da tsaruwa, kafarta sanye da wani hadadden takalmi high heels mai shegen kyau, tana tafe tana nazarin matar hankalin ta yatafi kan budurwar nan sosai, dan ita mutum ce mai son gayu, sabida haka idan taga mutum yayi kyau bata iya resisting sai ta tsaya ta kare masa kallo cike da sha'awa...

Bata ankara ba taji tabugi wani abu mai taurin gaske nan take roban kanta ya fadi ya zube akan abin da ta yi Karo dashi din, da sauri ta dago kai dan taga dame tayi karo haka mai shegen tauri, atunanin ta ko gini nema,. Bakinta ne ya bude, idanuwan ta suka fiffito waje, sanadiyar abinda tagani a gaban ta wanda ta kasa tan tance gaskene kodai buguwar da yayi ne har ya fara taba mata kanta ne..

Wani kyakkyawan saurayi ne mai kyan sure da kira tsaye gabanta yanata faman kakkabe jikin sa da ya baci da markaden waken,. Sanye yake da black suit da black cover shoe, idonsa sanye da black shade mai matuwar kyau...

Kana ganin shigarsa kasan kudin sunyi kuka a wajen, Bayansa wasu Katti uku ne, suma cikin suit, sai wasu samari biyu a gefen sa..

Zeena hankalin ta yakai kololuwal tashi, bata san sanda ta sa hanu ta fara kokarin share masa ba, wadannan karti uku na bayan sane suka yo kanta da zafin nama, daya daga cikin su ya fisgeta ya yardata kasa, nan take tasa kara mai karfi, saka makon zafin faduwar da taji...

So what do you think about this book so far. Hope you're enjoying it..

20 votes and I will continue..

Thanks for your time.

BAI SAN DANI BA (THE GIRL HE NEVER NOTICED) Donde viven las historias. Descúbrelo ahora