Zenarth's POV.
Suman tsaye tayi saka makon jin saukar husky voice din sa a dodon kunnen ta, ido ta zuba mai tana kallon sa har yabar layin da dan banzan gudu, shaf ta ma mata da kanta da inda take, ta manta da zogin da mazaunan ta suke mata saka makon faduwar da tayi a k'asa, ta nutse kogin tunanin...
Zuciyar ta ce keta faman bugawa tamkar zata tsaga kirjin ta ta fito, kallo daya kawai tayi masa, ya tsai da dukan tunanin ta, ji take tamkar ta tashi ta bi bayan sa, tabbas yau tayi gamo... Ke! Ke!! Ke!!! Da Allah malama dake fa ake magana!
Firgigit tayi ta dawo daga doguwar tunanin wannan bawan Allah da bata sanshi ba...M'ik'ewa tayi da sauri tana kad'e jikin ta, bata ankara ba taji anjefeta da wani abu, sauri tayi ta daga kai ta Kalli wanda ya jefetan sannan ta maida kallon ta ga abin da aka jefetan dashi wanda ya fad'i a k'asa, bunch din five - five hundreds ne, tai saurin ja da baya ta maida kallonta kan mutumin da ya jefetan, sannan tace meye wannan kuma?
Kallonta yake cike da k'yama yace idon ki baya ganine, gashi an biyaki asarar da aka miki maza ki ba ma mutane waje, kina tafiya kamar tinkiya baki kallon inda kike bi...
Ido cike da k'walla tace a'a kubar kayan ku ni ba sai kun biyani ba, ae tsautsayi ne, Kuma nike da laifi.. Ta sunkuya ta dauki robar markaden ta, ta juya ta nufi gida abin ta...
Mamaki da takaici ne yacika Usman (secretaryn Aryan na nan Nigeria) lallai wannan yarin yar da abin mamaki take, bai taba tsammanin a rayuwan yanzun nan a kwai macen da zaka bata kudi taki karba ba, duk da wannan din yarinya ce sosai bata da wani shekaru masu yawa bisa dukan alamu, karasawa yayi ya dauka hade da tabe baki ya shiga Mota yaja suka bar wajen...
Zeenarth na isa gida ta aje robar ta fad'a kan innan ta, tana maida nunfashi.. Inna dake zaune bakin k'ofar d'akin ta tun dazu tana zaman jiran autar tata, tace yau naga iskanci a nan, ina kika kai min waken kika dawo min gida da roba ba markad'e...
Zeena tana mai da nunfashi tace wlh innata bari nayi, nan ta kwashe duk abin da ya faru ta fad'awa inna.. Salati innan ta saki tana tafa hannu tace hande miyatti Allah am, bingel ge'el a fadd'a tayam wlh (yau na gode Allah na yarnan bazaki kasheni ba wlh) yanzu d'an jarin nawa Kika barar, to yau zanga yacce zamuyi a gidannan, kullum ina miki fad'a a kan rashin mai da hankalin kinnan a kan abu amma kinkiji, yauto gashi kin kashe mana dan jarin namu kin huta, maza tashi ki bani waje ja'irar yarinya kawai...
Zeena kuma k'ara mak'alewa jikin Innan ta tayi tana fad'in Dan Allah innata kiyi hakuri wlh tsautsayi ne bazan k'ara ba inshaAllah zanna maida hankali..
Inna tace to in banyi ba ya zanyi dake iye, ni tashi ki bani waje dan Allah..
Zeena tace to amma sai kince kiyi hakuri tukunna.. Inna tace to naji nayi sai ki tashi min ajiki ae ko...
Zeena ta mi'ke tana murmushi ta shige d'akin ta...I know it's short. Please manege 👏👏👏
ŞİMDİ OKUDUĞUN
BAI SAN DANI BA (THE GIRL HE NEVER NOTICED)
RomantizmHe's rich, she's poor, he have it all, she have nothing, he's a multimillionaire, the CEO of A.A FASHION DESIGN EMPIRE, she's just a girl with big dreams.. They meet by accident, she loves him so much, she's the girl he never noticed, she dedicated...