*YARONAH K'ADDARATAH*👩👦
*Written by Beelkeey Shuwerh*✍🏼
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://
maryamsbello.blogspot.com*Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah, cikin Ikon da yardar Allah Nakuma dawowa acikin sabon littafina mai suna YARONAH K'ADDARATAH INA fatan zaifi HERBEEYBTEEY DAD'I dah FAD'AKARWA.*
*Ina mai baku hak'uri kan informing naku danayi a k'arshen HERBEEYBTEEY na cewa zan kawo muku MAKAHON SO, saboda wasu 'yan matsaloli da aka samu yasa zamu fara da YARONAH K'ADDARATAH,ku biyoni dan jin wannan labari me tab'a zuciyar me karatu nasan insha Allah zakuji dad'in shi.*
*Ayi karatu lafiya*
Dedicated to my1 and only *Asmeey #the real pure pinkey* kinfi kowa son novel din nan❤ dan haka na sad'ukar miki da shi gabaki d'aya, kiyi yanda kike so da shi babu mai taka miki burki😄 Allah ya k'ara miki basira da kwarin ido Amin summa Ameen!!🙏🏻 I wish I can show you how much I love you, Beelkeey Shuwerh Love's you plenty HABIBTY ❤.
↗Pls ban yarda ayimin editing novel bah duk wanda yayi nabar shidah Allah akula pls
↗Allah knows best so bawanda yawuce gyara kuma babu Wanda baya kuskure Note that pls
↗ Banyi copying KowA bah kuma banah forcing KowA yakaranta Wanda xai iya yakaranta Wanda baxai iyaba yabari babu dole.
↗ don't be a silent READER tell me how you feel or thinks about my novel.Follow me on wattpad @Shuwerh Beelkeey22
Episode 1
January, 2018
Falon yayi tsit bakajin komai se k'arar fan kai kayi tunanin bakowa ciki, sedai da kalli fuskokin mazauna falon zaka gane dalilin shirun da falon yayi.
Cikin kakkausar murya Babban Daddy ya fara magana " lokaci yayi dazanyi maganin fitinar dake addabar wannan zuri'a tamu me albarka, ban tab'a tunanin a rayuwata zan haifi YARON dazai zame min fitina ba, Waleeyd da mutunci na amma cikin d'an k'ank'anin lokaci da samun ka kasa ya zube, baka kyaleni ba baka kyale 'yan uwana ba, a yau zan yanke hukunci indai nina haife ka kuma nakeda iko dakai bazan bar d'an uwana ko d'aya ya shiga cikin wannan rigimar daka d'akko ba".
Ya juya ga Maryam cikin tsananin fishi yace " nagaji idan ma da had'in bakin ki Waleeyd yake duk abinda yai niyya to yau zan kawo k'arshen abun, inaso ki sanar dashi da kanki dan yafi d'aukar maganar da mahimmanci bani bashi na cire shi a sahun 'ya'ya na, yaje indai duniya ce zai gani".
Tunda ya fara maganar se yanzu Waleeyd ya d'ago a firgice, cikin kid'ima da tsananin rud'ani ya matso ya rik'e k'afar Babban Daddy yace " Daddy kayi hak'uri dan Allah, inaso duk abinda nai ya k'are kaina, wallahi ba Mummy ce take sani ba kuma nima wallahi bansan lokacin dana keyi ba".
In akwai kalmar da Babban Daddy ya tsana be wuce wannan kalmar da Waleeyd ya fad'a ba ta k'arshe, ya bud'e baki zaiyi magana, maganar ta mak'ale a mak'oshin sa sakamakon fad'uwar da Maryam tayi, cikin tsananin firgici Sadeeyq ya mik'e yai kan mahaifiyar tasu,kan ya k'arasa Farouq ya rigashi jijjigata ya shigayi hawaye nabin cheaks d'insa yana fad'in " dan Allah Mummy ki tashi " ganin bata motsi ya juya yana kallon Waleeyd da jajayen idanun sa yace " Wallahi Waleeyd kaji na rantse ka kashe mana mahaifiya bazamu yarda ba, haba Waleeyd for Godness sake me kake so ka zama a rayuwar ka? Wallahi inhar duk abunda na mallaka zai k'are inhar mahaifiyata ta rasu bazan kyale ka ba " Sadeeyq ne yace " Farouq ba magana zamu tsaya yiba kamota mukai ta asibiti" da hanzari sukai waje da ita suka sata a mota suka tafi.
Waleeyd na zaune yana wani irin matsanan cin kuka me cikeda cushewar numfashi Babban Daddy ya daka masa tsawa yace " bazaka tashi ka tafi wajen jami'an tsaron dake jiran ka ba...... " shigowar Mubarak a firgice yasa Babban Daddy dakatawa da maganar da yake yi, fad'i yake " Muhammad waye ya sanar da Abbah halin da ake ciki? gashi can ya fad'i ciwon sa ya tashi ".
Cikin tsananin tashin hankali da firgici Babban Daddy ya fice a falon Mubarak ya mara masa baya.
Kallo d'aya zakai wa Waleeyd ka hango matsanan cin tashin hankali dan yana matuk'ar k'aunar Grandpa d'in nasa sam baya k'aunar abinda zai tab'a masa shi, ta baya yaji an dafa shi koba'a fad'a masa ba yasan Shuwerh'n sa ce dan inba ita ba, ba wanda zai kulashi a wannan yanayin, juyowa yayi yai murmushin k'arfin hali sedai ya kasa cewa komai sakamakon ganin yadda face nata ya koma tsabagen kuka, jikin sa ta fad'a tana kuka me tsuma zuciya sannan ahankali ta bud'i baki da 'yar muryar ta data disha she tace " Why Sweetheart? Why? Why always you? Meyasa? Meyasa? zuciyata bazata iya d'auka b...... " kasa k'arasawa tayi sakamakon wani irin sabon kuka daya kub'uce mata.
D'agota yayi ya rungume tsam ajikin sa wane za'a kwace masa ita cikeda tsantsar so da tausayin ta yace "kiyi hak'uri Shuwerh na nima bansan ya ake nakeyin hakan ba, I just use to found my self doing, I don't know exactly how? and when? nakeyi ba ki tayani da addu'a Sweetheart duk tsanani sauk'i nanan zuwa" ya sake matse ta sosai ajikin sa.
" Sweetheart na bazan iya bari su tafi dakai ba, duba fa kaga police kusan.......... " saukar marin dataji ne yasata kasa k'arasa maganar data keyi, runtse ido Waleeyd yayi zuciyar sa nawani irin rad'ad'i, tana d'agowa taga Abdallah da sauri ta sake k'ank'ame Waleeyd.
Waleeyd ya kalla cikin daka tsawa yace " tashi kafita su tafi dakai tunda rayuwar daka zab'awa kanka kenan " wata irin gigitacciyar k'ara ta saki tace " Uncle dan Allah karku bari su tafi dashi, I can't do without him, my life is nothing with out him he is the key to my happiness, I begged of you Uncle save him" ta rik'e k'afar Uncle Abdallah tana kuka na fitar hankali numfashin ta har sama_sama yakeyi.
Kobi takanta beyi ba ya juya ga police d'in da suka shigo, cikin daka tsawa yace " bazaku iya fitar dashi bane? Ni infitar muku dashi? " DSP ne ya kalli Uncle Abdallah yace " takarda tazo mana daga Alhaji Bukar ce wa besan da Waleeyd acikin abinda ya faru b..... " da sauri Uncle Abdallah ya katse shi dacewa " inshi ya hak'ura mu bamu hak'ura ba dan haka kutafi dashi kuyi masa hukunci dai_dai da abinda ya aikata", handcuffs suka saka masa sukai................
*'Yar Gatan Mhiss_B_Hal ce*💞
YOU ARE READING
YARONAH K'ADDARATAH
Фэнтези_its about a boy loved by his great respectful and happy family, hated by his step mother who totally change him into something different and made his precious life misarable_