.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
*YARONAH K'ADDARATAH*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆• ゚ ☆
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨ *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆• ゚☆
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆® *REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://
maryamsbello.blogspot.comWords can’t ever explain how much I love you *Rafee"at D\dikko* wannn shafin naki ne ke kad'ai ban had'aki da kowa ba, kiyi yaddah kikeso dashi, no need for long essay you know I so much love you.
*Allah ya k'ara miki basira da zak'in hannu, ya tsone idon mak'iya akan ki, up up forward never backward insha Allah**Don't be a silent Reader tell me how you feel or think about my Novel*
Follow me on wattpad @beelkeey Shuwerh
Episode 5
March, 2018
*******THE NEXT DAY*******
Ya kama Saturday d'in k'arshen month, kuma a k'a'idar Abbah ya ware wannan rana a matsayin ranar da wannan family mai albarka suke meeting dan tattauna matsalar su.K'arfe 10:00 am kowa ya hallara a falon Abbah, bayan kowa ya zauna a mazaunin sa, Abbah ya bud'e taro da Addu'a sannan yayi bayanin abinda za'a tattauna akai azaman nasu na yau.
Mubarak ne ya d'aura da bayanin kud'in auren Auwal, Sulaiman da Mahbub da za'a kai gobe idan Allah ya kaisu da rai da lafiya.
10:45 am Abbah ya lura da Babban yaya tunda aka zauna baice komai ba, har 11:00 am ta cika aka sallami yara zaman ya dawo na manya kad'ai.
Abbah ne ya kalli Muhammad yace " Babana lafiya kuwa? naga tunda muka zauna banji kace komai ba, kuma da alama kanada magana abakin ka " gaba d'aya 'yan uwan nasa zuba masa ido sukayi suna jiran suji mai zaice.
Ibrahim ne yace " lafiya kuwa Babban Daddy? "
Kallon Abbah Muhammad yayi yace " Abbah dama inason in sanar dakai inaso gobe idan ankai kud'in su Sulaiman, nima za'a wuce katsina dan nema min auren wadda zan aura ".
Gaba d'aya d'akin kallon kallo aka koma, baga mazan ba baga matan ba, sannan kuma suka mayar da kallon su kan Maryam dan ganin yanayin datake ciki, sai dai kowa ya cika da mamaki ganin kwata_kwata bata damu ba .
Itakuwa baiwar Allah daurewa Kasai takeyi dan ita kad'ai tasan yadda takeji a zuciyar ta, Maryam nada tsananin kishi amma tayi k'ok'arin b'oyewa ne saboda cikar burin uban 'ya'yan ta Abban Waleeyd.
Shiru d'akin yayi na tsawon 5 minutes, ganin shirun yayi yawa Abbah ya katse shirun da cewa " Babana baka duba halin da Maryam take ciki ba, anya idan kayi mata abokiyar zama yanzu bazai zama matsala ba, duba da juna biyun dake tartare da ita ",
Nasir ne yayi karap ya karb'i zancen " Abbah gaskiya ko ita Maryam d'in ta yarda ba yanzu ba, haba ai in akai haka ba tausayi a lamarin ",
Cikin d'aga sauti Muhammad yace " to sarkin tausayi, an fad'a maka bada goyon bayan ta na tsari maganar bane ".
YOU ARE READING
YARONAH K'ADDARATAH
Fantasy_its about a boy loved by his great respectful and happy family, hated by his step mother who totally change him into something different and made his precious life misarable_