.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
*YARONAH K'ADDARATAH*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆• ゚ ☆
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨ *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆• ゚☆
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://
maryamsbello.blogspot.comWords can’t ever explain how much I love you *Miemiebee* wannn shafin naki ne ke kad'ai ban had'aki da kowa ba, kiyi yaddah kikeso dashi, no need for long essay you know I so much love you.
Amma fa ina d'anjin haushin yadda batoul take wahalar mana da Muhsin # BE CAREFUL WITH MY HEART, dan Allah a d'an sassauta mana.
*Don't be a silent Reader tell me how you feel or think about my Novel*
Follow me on wattpad @beelkeey Shuwerh
Episode 6
March, 2018
*******TWO HOURS LATER*******
Maryam na zaune abin duniya duk yayi mata zafi Kareemah ta shigo d'akin, cikin tausaya wa tace " Maman Waleeyd kizo inji Abban Waleeyd " gaban tane ya fad'i amma ta daure ta mik'e suka fita.One seater ta samu ta zauna ta sunkuyar da kanta k'asa " Abban Waleeyd gani ", ta fad'a da rawar murya.
" Nace bangan ki bane ko ya? Maryam wai yaushe kika koma haka ne? Yanzu kiyi min laifi ko hak'uri bazaki bani ba saidai ki shige d'aki " fad'a ya shigayi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ita kuwa banda hawaye babu abinda takeyi dan tama kasa magana.
Farouq da Usman ne suka shigo, duk sai sukaji abin wani iri dan basu saba ganin hakan a tsakanin iyayen nasu ba, Kareemah dake cikin farin ciki, cikin kissa take ta bawa Muhammad hak'uri amma shiko kamar zuga shi takeyi.
Usman ne ya k'araso gurin Mummy'n su ya rik'e hannun ta yace " Mummy mai akayiwa Babban Daddy? "
Takardun kawai tai masa pointing da hannu dan tama kasa magana, " lahh Mummy wannan ai takardun danaga Waleeyd yana yayyagawa d'azu ne, bari kiga ragowar dana d'auke na b'oye dan su bai yaga ba na kwace " da gudu Usman ya mik'e ya nufi d'akin Mummy'n tasu bai dad'e ba sai gashi ya fito rik'e da about 7 papers a hannun sa.
Muhammad gaba d'aya jikin sa yayi sanyi, jin da yayi dagaske ne Waleeyd ne ya yaga, hannu yasa ya karb'a ya shiga duddu bawa , d'agowa yayi cikin sanyin murya yace da Maryam " mai yasa kika ajiye a k'asa? "
" Wallahi Abban Waleeyd akan Cupboard na d'aura kuma kasan konima sai nayi d'age tsayi na yake kaiwa ", ta fad'a cike da damuwa.
Shima abinda yafi d'aure masa kai, ya za'ayi tsayin Waleeyd yakai nan.
Shiru yayi bai kuma cewa komai ba, sai itace tace " Daddy'n Waleeyd dan Allah kayi hak'uri ", wani irin farin ciki mara misaltuwa ne ya kama shi dan yanzu a duniya gani yake kowane irin laifi kai masa indai ka kirashi da Daddy'n Waleeyd to ya hak'ura har abada.
YOU ARE READING
YARONAH K'ADDARATAH
Fantasy_its about a boy loved by his great respectful and happy family, hated by his step mother who totally change him into something different and made his precious life misarable_