🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*YARONAH K'ADDARATAH*👩👦
*Written By Beelkeey Shuwerh*✍🏼
® *REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://
maryamsbello.blogspot.comWords can’t ever explain how much I love you *Fatima Ibrahim rimi*, thank you for everything, thank you for being that one great special person to me. I love you eternally i dedicated this page in special honour to you! Don’t thank me you deserve more and more!_
*MUCH LOVE MY PARTNER IN CRIME*
Follow me on wattpad @Shuwerh Beelkeey22
Episode 2
January, 2018
~Kobi takanta beyi ba ya juya ga police d'in da suka shigo, cikin daka tsawa yace " bazaku iya fitar dashi bane? Ni infitar muku dashi? " DSP ne ya kalli Uncle Abdallah yace " takarda tazo mana daga Alhaji Bukar ce wa besan da Waleeyd acikin abinda ya faru b..... " da sauri Uncle Abdallah ya katse shi dacewa " inshi ya hak'ura mu bamu hak'ura ba dan haka kutafi dashi kuyi masa hukunci dai_dai da abinda ya aikata", handcuffs suka saka masa sukai waje dashi~
Cikin wani irin yanayi ta mik'e da nufin rik'o Waleeyd, da azama Uncle Abdallah ya fincikota yai mata wani irin rik'o ta yadda bazata iya kwatan kanta ba dan yasan a haukan ta tsab zata bi Waleeyd, fizge_fizge ta farayi kamar me shirin tada aljanu seda sukazo fita ya juyo ya kalleta yana mai tausaya mata sannan suka fice, suna fita ta sulale k'asa sumammiya.
Suna fitowa harabar estate d'in wata iriyar kunya ta kama Waleeyd sakamakon 'yan uwansa daya gani maza da mata, kowanne ka kalla yana cikin tashin hankali da damuwa sunkuyar da kansa yayi dai_dai lokacin da suka had'a ido da Ayman da Sayf, wajen jami'an tsaron dasukai dan dazo suka nufa da nufin sashi a mota.
Ayman da Sayf ne sukai saurin k'arasowa inda suke banda hawaye ba abinda suke, rik'o hannun Waleeyd Ayman yayi yace " Waleeyd wai me yake damun ka? Meyasa kowa ya bud'i baki sedai yace Waleeyd? Me kake so ka zama ne? Ka duba yadda iyaye da 'yan uwan mu suke cikin tashin hankali duk ta dalilin ka", rasa ma me zaice yayi kawai yayi shiru ga tsananin damuwa dake addabar zuciyar sa ganin sunaji suna gani za'a tafi da d'an uwan su shiko Sayf ma ko magana ya kasa, murmushin k'arfin hali yayi yace " Ayman bazan gaji da baku hak'uri ba akan abinda nake jawo muku".
Kai kawai suka gyad'a masa kamar k'adangaru sannan Sayf yai k'arfin halin cewa " insha Allah zamu saci hanya muzo ", bai sake cewa komai ba police suka sashi a mota suka tafi.
*AT HOSPITAL*
Naseeyr International Hospital shine sunan dana gani a saman asibitin, da sauri aka wangale musu k'aton gate d'in suka shiga direct parking space suka nufa sukai parking car d'insu, da sauri doctors da nurces suka turo gadon d'aukar marasa lafiya aka d'aura Mummy aka nufi emergency ward da ita dan ceto rayuwar ta, about 7 doctors ne suka rufa a kanta dan she is in critical condition.Sadeeyq se zagaye d'akin yake banda innalillahi wa'innah ilaihirraji'un ba abinda yake mai_maitawa duk kwarewar sa a aikinsa yau ya kasa.
Likitoci nata mamaki kasancewar Sadeeyq Babban likita da akeji dashi a k'asar nan, Dr Ahmad ne ya k'araso inda Sadeeyq yake yace " haba Dr Meyasa kasan matsalar dake damun Mummy amma ka kasa k'ok'ari gurin kawar da duk wata damuwa dazata sa ciwon ta ya tashi? " shikam Sadeeyq banda hawaye babu abinda yakeyi dan ya kasa cewa komai, rarrashin sa Dr Ahmad ya shigayi yana kwantar masa da hankali.Faruq na zaune a harabar asibitin abun duniya duk ya ishe shi yaga shigowar motar Babban Daddy, da sauri yaga an fito da Abbah lifeless an nufi emergency dashi, kamar zautacce ya koma gurin su Sadeeyq yace " ya Sadeeyq ga Abbah can an kawo shi besan inda kansa yake ba".
Dafe kai Sadeeyq yayi zuciyar sa nawani irin rad'ad'i, dakyar ya samu ya saita kansa yai d'akin da'aka kai Abbah yana zuwa ya tarar shima likitoci sun had'u akansa dan bashi taimakon gaggawa, kallon Babban Daddy da Daddy Mubarak yayi da rinannun idanun sa dasuka chanza launi yace " Daddy ina Waleeyd? sun tafi dashi? " wani dirty look Babban Daddy ya watsa masa dan inda abinda ya tsana yaji be wuce sunan Waleeyd ba, Daddy Mubarak kasa cewa komai yayi se binshi da ido azuciyar sa yace " Allah sarki d'an uwa me dad'i " sannan ya shiga addu'ar Allah ya kare masa Waleeyd d'insa a duk inda yake.
Jiki a sanyaye ya koma d'akin da aka kwantar da Mummy, yana isa ya tarar da Farouq, Uthman da Aleeyu zaune jugum_jugum kallon tausayi yabi su dashi aransa yana sak'awa yanzu ace duk wannan matsalar dake damun su akan Waleeyd ne, ga mahaifiyar su kwance rai a hannun Allah babu tabbacin zata tashi, ga grandpa d'insu jigon wannan zuri'a tasu me albarka a kwance.
Window d'in d'akin da aka kwantar da Mummy ya lek'a ya hangota kwance ansamata oxygen se drip, guri ya nema ya zauna ya dafe kansa dake barazanar tarwatse wa.
*WAI SHIN ME YAKE FARUWA DA WANNAN FAMILY'N?*
*MEYE SILAR WANNAN TASHIN HANKALIN?*
*SANNAN KUMA WANENE WALEEYD?*
*ASALIN LABARI*
Alhaji Ahmad Muhammad company shahararren me arzik'i ne kasancewar ya rik'e muk'amai da dama na gwamnati, ciki harda ambassador dayaiwa Nigeria a America haifaffen gari Kano ne unguwar galadanci, shikad'ai Allah ya bawa iyayen sa hakan yasa ya tashi cikin gata da kulawa hakan baisa iyayen sa sun kasa bashi tarbiya ba, a garin kano yai karatun sa na primary da secondary bayan ya kammala iyayen sa suka turashi k'asar Cairo dan yin university.Yana matakin degree Allah ya yiwa iyayen sa rasuwa a had'arin mota, lokacin da labari ya same shi bak'aramin tashin hankali ya shiga ba, haka ya dawo Nigeria akai zaman makoki dashi sedai kwata_kwata an kasa gane kanshi saboda yawan kuka and one more thing ko abinci bayaci, shi kuwa bakomai ne yake sashi hakan ba se tunawa dashi kad'ai iyayen shi suka haifa gashi suma Allah ya karb'i abinsa.
Saida yai wata shida a Nigeria sannan aka samu ya koma dan cigaba da karatun sa, amma kafin ya tafi seda dangin mahaifin sa suka nuna masa tarin dukiyar da mahaifin sa yabar masa sannan suka sama masa wanda zai cigaba da kular masa da dukiyar, haka ya tattara ya koma.
Anan ya had'u da Bilkisu 'ya ga Alhaji Sani Muhammad, shak'uwa ce me k'arfin gaske ta shiga tsakanin su harta kai bayan sun kammala karatun su sukai aure, inda aka d'auke shi aiki a k'asar dayai karatu dan ya fito da sakamako me kyau, shekarar su d'aya da aure Allah ya albarkace su da samun d'a namiji inda ranar suna yaci Muhammad (Babban Daddy) sunan baban Ahmad, haka rayuwa taci gaba da tafiya.
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah inda yanzu gashi Bilkisu haihuwarta uku, alokacin ne Ahmad ya turawa lawyer'n sa design na art d'in estate d'in yakeso saboda burinsa yaga duk 'ya'yan sa sunyi aure aciki bayaso kowa ya fita.
To kasancewar a America suka d'akko ma'aikata yasa cikin shekara d'aya da wata biyu komai ya kammala inda ya tattaro ya dawo k'asar sa ta haihuwa wato....................
*'Yar Gatan Mhiss_B_Hal ce*💞
YOU ARE READING
YARONAH K'ADDARATAH
Fantasía_its about a boy loved by his great respectful and happy family, hated by his step mother who totally change him into something different and made his precious life misarable_