21-22

623 45 1
                                    

*SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


*Wannan shafin gabad'ayan shi sadau k'arwace ga masoyan wannan novel, inayinku irin sosai d'innan*❤🤝

*A k'ara hakuri dani, lafiya ce tamin k'aranci👏🏻*

           *21~22*

Soyayya fa ta kankama sosai, tsakanin Meenah da Yasir, daidai gwargwado yana sake mata bakin aljihu, har sabuwar waya ya sai mata, kati kuwa bai yankewa a wayar ta.


Ummah dake tsakar gida tana aiki ta k'wala mata k'ira ta fito, tace

"Mutum kullum a d'aki kamar mummunan amarya, zoki shiga kicin kiyi girkinnan, don naga son jikin naki gaba-gaba yake, zanga yadda zakiyi a gidan ki."

K'orar kicin d'in na kalla, naga wani bak'in hayak'i na bulbulowa daga ciki a zuciya ta nace

"Toh! Kuma inzanyi auren sai inyi a irin wannan gidan? Ace na taso cikin talauci kuma in auri talaka, in koma gidan talauci! Allah sutura, duk karanta *Novel* d'ina ban tab'ajin talakawan cikin  sun k'are rayuwar su a talauci ba, don haka nima bazan k'are rayuwa ta a talauci ba."

Umma tace
     "Bakiji me nace bane?"

"Naji Ummah."

Maganar zuci
     Ai indai na kuskura na shiga wannan hayak'in ba k'aramin wari zanyi ba, meyuwama yau saina dishe na fara bak'i.

Shahadar k'uda kawai nayi na kutsa, tsugunawar nayi ina hura wutar, nayi iya iyawa ta yak'i kamawa ga hayak'in daya gama cikamin ido, dama yaya, ban isa inshi ga haske in bud'e fuskata ba dole saina kare ta da mayafi, ace ga azahar hayak'i bana iyaba, ai take na fara tarin k'arya harda d'auke numfashi.

Ummah kamar bazata kulani ba, ganin tarin nawa sai gaba yake yasa ta lek'owa, ganina a durk'urshe na fita hayyaci na yasa ta shigowa ta kamani ta fiddoni sai sannu take jeromin, niko sai wani narkewa nake ina tari numfashi na sama-sama kamar mai asma ta shak'i k'ura.

Zaunar dani tayi acan gafe ta tafi d'ebimin ruwa, tana juyawa na kwashe da dariya k'asa- k'asa, ina hango ta fara tarina ina rik'e k'irji.


Ruwan ta bani nasha kad'an, tarin yad'an lafa sai dai har yanzu ban saki numfashi na dai-dai ba.

Rik'eni tayi, takaini har d'iki na tace

"Ki kwanta, inaga hayak'in iccen ne da kika shak'a don akwai zafi, barinje in yi girkin."

ina rik'e da k'irji nace
 
"Ummah dakin bari, idan ya fad'amin zanzo inyi."

"Aah! Ki kwanta kawai idan Dauda ya dawo sai kuje kyamis a dubaki."

"Toh Ummah."

Tana fita a d'akin na gyara kwanciya.

*Gidan Alhaji Muntari*

Zancen aure ya kankama gadan-gadan, duk abunda ake Marka bata da labari tunda dama bamai zuwa wajen ta.

Hali kuma yananan saima abunda ya k'aru.

Ana saura sati biyu aure da daddare Alhaji Muntari, suna zaune da yara a falo suna kallo ya tura babban ya k'ira maman tasu a d'aki, don sam bata tab'a zama cikin su, acewar ta damun ta suke.

Saida ta d'au lokaci mai tsawo kafin ta zo.

Akan hannun kujera ta zauna a d'ad'are, irin fad'i zancenka gaba zan k'ara d'innan.

Kud'i ya mik'o mata  dubu ishirin, da murna ta karb'a, nan ya fara mata bayanin ta sayi abunda take buk'ata, kuma nanda sati biyu za'a kawo mata amarya.

Wani irin tambul naga Marka tayi, da gudu na nufi firjin su don d'auko gorar faro na b'alle murfin na tuttud'a mata, irin na 'yan novel.

Tunda nayi tambul nayi- nayi, in suma na gagara yar d'auke numfashi na nayi na 'yan mintuna amma na kasa, azuciya ta nace

"Toh! Inaga sumanma baiwa ce, tunda 'yan novel suna suma yafi a k'irga."

Nidai na gama duba faro babu duk firjin, sai fiya wata haka na d'auko na dawo, turus nayi ganin Marka zaune tana rarraba ido kamar taci kud'in k'awata Dambu.




*Ayi hakuri da wannan👏🏻*

*Ummyn Afrah*😘

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now