13-14

776 41 0
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Tuba nake dajina shuru da akayi na kwana biyu👏🏻*

*Wannan shafin sadaukarwa ne gareku, Mazajen novel*😹
*MD Asnanic*
*Jameel Nafseen*
*Ramadan Mubarak*
*AnaM Dorayi*
*Saeefullah*
*Hafiz koza Shugabanmu na nan....*🙊
*Mr Zain*
*Dr. Khamal*
*Deeny Boy*
*Mukhtaar M Nafseen*

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*
*Agobe insha Allah nake k'ara shakara guda cikin shekaruna, ina buk'atar addu'o'o daga bakunan ku masu albarka👏🏻*

*2/3/2018*

               *13~14*

Abun duniya duk sun taru sun min yawa, 'yar kud'in dazan sai manda zan shafama ya gagare ni, ga wasu manyan k'uraje da suka fara b'atamin fuska.

Mik'ewa nayi na nufi gidan su Asmyy, rabona da gidan tun wani rana dana shiga ta min magana kan indaina shafe-shafe b'ata fuska yake, gara nabar asalin kalata yafi, nasan kawai hassada ce taga tana da haske shiyasa take k'yashin taga nayi fari.

Ina shiga na samu Asmy a falo suna kallo, bayan mun gaisa tace

"Matar mijin novel yau kuma an tuno damu ne?"

"Ummm! Kullum kuna raina bana samun zama ne, kinsan muna shirye-shiryen jarabawar gama makaranta, idan na tafi tun safe sai yamma nake dawowa, ba lokaci shiyasa."

"Ayyah! nayi zaton fushi kike ai, don naga tun ranan dana miki magana kan shafa mai naga kin daina zuwa."

"A'ah! Ainama daina shafawa, kingama yadda ya b'atamin fuska."

"Gaskiya kam kinga yadda ya miki kuwa?"

"Wallahi kuwa! Nama rasa mezan shafa ya mutu, na goga lemon tsami amma yak'i mutuwa."

"Ai tun farko ke kika b'ata fuskar ki, inada wani maganin k'uraje muje d'akina in baki."

"Aiko nagode! Akwai wanima da aka gayamin, yana da kyau sosai, naira d'ari biyu da hamsin, rashin kud'i ya hanani saya."

"Muje in baki ki gwada, in bai miki ba saiki ki sai wancan d'in."

Haka na bita a baya, ammafa zuciyata cike take da haushin ta, nida zata ban kud'in saita had'ani da wani mai.

Haka na karb'a harda k'arin 'yan tsummoki, godiyar da baikai zuci ba nayi, na dawo gida.

Gaba d'aya dabarata ta k'are, gashi ba dama inyi k'aryar ance akai kud'in wani abun makaranta, yanzu Yaya 'Danladin nan zai kwashi k'afar shi kamar na d'an tsako yaje makarantar ya tambaya.

Kai! Ni kamarma sun tsaneni agidan wallahi.

Ai duk randa na *Auri Mijin novel* Yaya 'Danladi da Yaya Dauda zasuga walak'anci tunda ni suke ma haka, gawannan 'yar rainin hankalin kuma yanzu wasan b'uya muke, tunda nace zani gidan su.

Da sallama Alhaji Muntari ya shigo gida, hannun shi d'auke da 'yar bak'ar leda, shuru yaji ba amsa afili yace

"Yanzu haka tana can, tana shegiyar karatun novel d'in nata da baik'arar ta da komai."

Cikin gidan ya shige, ba kowa har yaran basunan, d'akin ta ya shige, aiko tana mik'e kan kujera tiri sita, ga littafi a gefen ta da alamu ta gama karance shine ta koma kan na waya.

Gaba d'aya imanin ta yanaga waya, inaga za'a iya sungumar tama ai waje da ita bata sani ba, don tariga tayi nisa.

Sake rattaba sallama yayi.

"Lahhh! Alhaji ka dawone?"

"Ban dawoba, fatalwa tace tafara yowa gaba."

"Toh! Yau kuma da bak'ar magana aka dawo?"

"Wai don Allah sau nawa zan miki magana kan barin gidannan haka? Kin baro cikin gida ba kowa kin k'ule a d'aki kamar gidan ba mutane, wataran har a shigo a kwashe kayan gidan kaf kina nan kina karatun da baida wani amfani, kema kanki inbaki wasaba harda ke za'a had'a."

"Kai kullum baka fatan alheri, yo aiko bacci nake hakan bazai tab'a faruwa dani ba."

"Ina yaran suke?"

"Suna mak'ota."

"Yanzu fisabilillahi akan karatun littafin soyayya saiki rink'a korar yara mak'ota! ace kullum magana d'aya meyasa bazaki zauna dasu ba? kinsan da wasu yaran suke wasa ne? daga yau kinyi na k'arshe idan hakan ya kuma faruwa ranki zaiyi mummunan b'aci."

"Uhmmm! Yau dai da sababi kazo, gara dai inbarma d'akin, idan ka gama na dawo."

Tana ficewa ya zube kan kujerar, ya d'aura hannayen shi a ka cikin b'acin rai yace

"Wai wannan wace irin matace? Ko kad'an batasan ta tausasa kalamanta ga mijin taba, kadawo aiki kana buk'atar hutu da nutsuwa amma sam batasan hakaba, hatta da wankan yara sai dai mak'ota su musu, aikin gida sai dai a tara yaran unguwa suyi, d'an kud'in cefanen rabi a sayar data yake tafiya, kai! dole inyi k'ok'arin d'aukar mataki."

Bayan ya rage kayan jikin shi, ya nufi babban falon gidan, can ya samita tana ta sana'ar tata.

Ficewa yayi daga gidan, ya aiki yaro mak'otan ya k'ira mishi yaran.

Suna fitowa da gudu suka rungumi Baban nasu suna murna, suna mishi oyoyo, k'aramar ya d'auka ta macen shi kuma na mijin ya rik'e hannun shi suka shige gira, suna ta bashi labarin abunda ya faru da basunan yara gaba d'aya sunfi sabawa da uban nasu kan uwar.

Babban yace

"Baba yau su Haule suna wasa dasu Hinde harda cire wandonsu, wai zasuga kalar gaban kowa."

Take wani fad'uwar gaba da zufa ya keto mishi, lallai wannan babban sakacine na uwar su, dolema yayi k'ok'arin d'aukar mataki, tun kafin wankin hula ya kaishi ga dare.

Yace

"Haulen Baba ashe kinason bulala kenan ko?   Ko mutuwa kikeso kiyi?"

"Aah Baba kalya fa yakeyi, banda ni cu Cinde ne."

"Harda ita Baba, danace zan fad'a maka shine ta mayar."

"Rabu da ita, inace kinason mutuwa?"

"Aah Baba."

"Toh duk randa kika sake mutuwa zakiyi kinji ko."

Nan ta shiga kuka tana fad'in ta daina, bazata k'ara ba.

Har suka shiga gida tunanin mafita yake, gaba d'aya ya rasa abunyi, kuma dole ne ya samo mafita, zaije ya nemi shawara gun Hajiyar shi tunda ance mai neman shawara baya b'ata.

Suna shiga ya d'auko ledan bisko da cakulatin daya kawo musu ya basu ya wuce ciki, harara tabi bayan shi dashi, taja d'an k'aramin tsaki.

Hayaniyar yaran, yasa ta dawo da hankalin ta garesu tace

"Ke kawo ledar in gani."

Wurga musu tayi tace

"Aikin banza, baza'a tab'a sayo ma mutum abunda zai motsa baki ba sai dai a k'are kan yara, ku tashi ku bishi ciki ni karku dame ni."

Sum-sum-sum suka wuce don mugun tsoron ta sake.


SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now