37-38

643 40 4
                                    

*SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

🤴🏻

*NA:*
*UMMYN YUSRAH*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*37~38*
Mungama shirin komai da dare, jira kawai muke azo a d'auki amarya, har wajen taran dare shuru, mutane 'yan kai amarya harsun fara tafiya gidajen su, Goggo Asabe ce k'anwar Abbah tace in k'ira wayarshi inji ko lafiya mutane sun taru, shuru har yanzu basu zoba, k'iran wayar nayi nasata a sifik'a yadda kowa zaiji, yana d'auka ya fara magana kai dagajin muryar tashi kasan bacci yake, hak'uri ya bani na rashin zuwa d'aukana da ba'ayi ba, wai mantawa yayi bai gayamin ya canza ra'ayi ba, wai ayi wuni da komai a gidanmu don baison azo a b'ata mai gida.

Kafin na bashi amsa, caraf Inna Lantai ta amshe wayar ta fara zazzagamai ruwan masifa, bai bari takai k'arshe ba ya datse wayar.

Kasak'e kawai tayi da waya hannu, tana fad'in lallai wannan yaron akwai d'an iska ga rainin hankali, wurgomin wayar tayi tana fad'in

"Zaki sani! Ina ke gwanar kwad'ayi ko? Kinje kin kwaso mana yaro mara kunya, saiki fara shirin zama dashi, din tunda na ganshi nasan bashi da mutunci, daga ganima arzik'in k'arya gare su, tunda kince kinji, kin gani, kyaje can ku k'arata, mudai namu mu kaiki mu ajiye kine mu dawo."

Haka tai ta sababin ta, har 'yan kai amarya suka watse, niko sam banga laifin Shiba, don nasan baison a b'ata mana gida ne, don yace ba k'aramin kud'i ya kashe ma gidan ba, bai kumason k'azan ta, waya ko daya tsinke nasan baison hayaniya ne, don nasan yanzu sai ya iya haddasa mishi ciwon kai.

Munyi wuni washe gari, bak'in da sukazo har sun tattara shirginsu sunyi gaba, acewar su rowar gidan amarya ake musu, mutane k'alilan kawai suka rage.

Washe gari tun safe yamin waya mu shirya da mutum biyu ko uku, zai turo mota a d'auke mu zuwa k'arfe goma.

Nan aka wakilta Inna Lantai saga b'angaren Ummah, sai Baaba Sharai daga b'angaren Abbah, sai Asmyy daga b'angaren k'awaye.

Kafin mota ta iso mungama shiryawa, tare sukazo da motar d'iban kaya, wata k'atuwar akori kura, kayan dana raina sai naga tsaf sun d'auke moton, don ba laifi na sami gudumawa sosai.

Nidai kallonsu nake a zuciya na, ina ku gama lodawa inje in jibge a d'akin bak'i.

Nasiha sosai Abbah da 'yan uwanshi sukamin, Umma dama tamin tun jiya, haka muka fito ina kukan rabuwa da gida, ina murnar tafiya gidan gayu.

Ahankali na bud'e mayafina na k'yallara ido don ganin kalar motar da akazo d'auka na cikin shi, gaskiya motar ta had'u ba k'arya, sai walwali take da d'aukar ido, ko had'uwar motar ma aka gani nasan na kafa tarihi, don bata gama yawaita a gari bama.

Da bismillah na shiga motar 'yan rakiya dake k'ofar gida sai d'aga mana hannu suke harmuka k'ule.

Titi d'od'ar muka hau, hanyar da zatayi wajen gari damu muka d'auka, a zuciya ta nace, wato su masu kud'i sam basu son hayaniya, sai sun sami k'arshen gari suyi ta tamfatsa gidaje abunsu.

Ban farga da dogon tunanin da nake ba saida naji Baaba Sharai na fad'in ina zai kaimu, ko dama gidan ba'a gari yake bane, nanfa naga mun fita gari ashe! Toh ina muka dosa?.

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now