19-20

666 46 0
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Na dawo fa. Nagode sosai da addu'o'inku, jiki Alhamdulillah*

*Akullum nakan sami sallamar mutane ba iyaka, ina murna da farin ciki da hakan, azotona tarin masoyanane, murnan kan koma idannaga cewar, ba masoyana bane masoyan littafina ne, inama zakusoni domin Allah badon littafina ba danayi murna sosai da samun masoyan k'warai😭*

*Don Allah narok'eku duk maison littafinnan daga farko ta nema cikin group👏🏻*

                  *19~20*

Tace "Meeenah!"

"Naam. Y kk."

Jiki a sanyaye tace

"Lafiya, ga kujera ki zauna, barin k'arasa aiki na."

Juyawa Meena tayi taga ba 'yar rakiyar ta, ta arce.

Ina zaune Summy ta gama wanke-wanke, ta dagasu ta kaisu ma'ajiyin su, ta share wajen, sannan muka nufi d'aki.

Nidai har hanzu ban farfad'o daga mamakin dana kwankwad'a ba.

Wai Matar manya 'yar aiki ce, duk wannan girman kai da kwarkwasa da iyayin ashe a 'yar aiki ta tsaya, gaskiya Allah yasoni an kawoni, da nayi abun hawa da d'ari na dako bansan abun yiba.

Ni adole nazo dangwalar arzik'i, shegiya harda wani Mommy na keban kud'in mai, koma d'auke-d'auke take musu waya sani, shiyasa ashe muke wasan b'uya da ita idan an tashi a makaranta.

Duk wannan zance a zuciya ta nakeyin ta, lokacin sumi ta fita.

Shigowa tayi hannun ta d'auke da kofin roba da ruwa a ciki ta ajiye min.

A zuciya ta nace ji tsiya! Fiya watar ma ta gagara sai ruwa a kofin roba, gashi ko sanyi babu, inda novel ne da yanzu an jeremin abun motsa baki sama da hansin.

Haka na d'auka nasha da hakuri, Summy tace

"Wai ya akayi kika gane gidan mu?"

Dariya ta kamani a zuciya, wai gidan mu, gidan masu gida dai.

nace

"Tare mukazo da ke ai, binki nayi a baya."

"Kin kyauta."

Nace

"Asheke 'yar aiki ce?"

tace

"inji wani muna fukin?"

"Haka aka gayamin."

"Sharrin mutane ne, kishiyar Baba tane take ganamin azaba, ta maidani kamar baiwa."

Nace
        "Malama nafasan komai, har alak'ar dake tsakaninki da yaron gidannan, don nagani da idona."

A zabure tace

"Kikaga me?"

"Yana rungume dake. Ko k'arya nayi?"

Dogon numfashi taja sannan tace

"Toh saime? Don Yaya ya rungume k'anwar shi sai wani abu ya faru? Nifa banson muna furci."

"Ba wani munafurci, ke nifa badon ina k'aruwa dake ba da saina tona asirin ki a makaranta, ko wannan girman kan naki zai ragu, mutum bad'an gidan uban kowa ba sai girman kantsiya."

"Ke! Banason rashin mutunci, kinzo har gidanmu kina gayamin maganar banza."

"Gidan muta ne dai, wayasan daga wani k'auyen kikazo, irin kune 'yan aikin cikin novel masu aure mazan gidan ko yaran gidan, kekam ai sai dai a kwashi rabo a kore ki don bamai auren ki."

"Ke! Bafa nason d'iban albarka."

"An miki d'in! Ni ai Allah ma ya soni, danayi kud'in nape da asiri na ya tonu, ni nazo cin arzik'i ashe mutum ma ci yake."

"Kwad'ayayyar banza, indai baki zauna a matsayin da kike ba, kina tare da aiki, inba gulma da munafurci ba, meye zaki bini a baya kiga gidan mu, har wani kinzo cin arzik'i sai kici tunda ke kika tara, kizo ki fitar mana a gida kuma."

"Hehehehe! Gidan masu gida dai, zan fita basai kin koreni ba sarkin k'arya 'yar gidan Mommy, duk randa nayi aure kizo kici arzik'i yarinya."

Haka muka rabu baram-baram. Tundaga ranar ko mun had'u a makaranta kowa sabgar gabanshi yake.

Alhaji Muntari zaune gaban mahaifiyarshi, inda ya kwashe komai ya fad'a mata game da Marka, tace

"Kai! Amma yarinyar nan ta shayar dani mamaki! Ban d'auka abun nata yakai har haka ba, saboda halinta fa yasa 'yan uwan ka suka daina zuwa gidan ka."

"Wallahi Hajiya na rasa yadda zan b'ullo wa lamarin."

"Wannan mai sauk'i ne, ga 'yar gidan Baffan ka 'Dayya Saude, kasan ta fito daga gidan miji dalilin rashin haihuwa, duka-duka shekararsu uku ne da auren amma dangin mijin duk sun tsangwameta, ga yarinya mai hankali da tarbiya, tunda akwai halin k'ara auren kawai kaje ku dai-dai ta, nasan zata kulama da komai naka."

"Toh Hajiya. Amma ina tsoron auren danginnan ina ba matsala."

"Kai dai kayi zato na alkairi, da yaddar Allah zakayi alfahari da zab'in."

"Insha Allah, zanje zuwa jibi."

"Allah ya kaimu."

"Ameen. Barin wuce gida."

"Toh agaishesu."

"Zasuji insha Allah."

Kamar kullum yauma falo ya iske ta sai aikin chatin take a waya, bai kula taba yayi wucewar shi ciki, ya rage kayan jikin shi, sannan ya dawo falon, tambayar ta yayi yaran tace yanzu suka fita mak'ota, fita yayi yasa akayo k'iran su.

Abinci ya d'auko ya zuba musu, tun kafin ya kammala zuba musu, suka fara wurga lomomi, tamkar wunin yau basuci abinci ba.

Yace
        "Marka yarannan basuci abinci bane?"

"Sunci mana! Me kagani?"

"Kiga yadda sukeyi, kamar sun wuni basu ciba."

"Sunci, gulmane kawai irinna yara."

"Hummm! Allah kyauta."

Mik'ewa tayi ta nufi ciki don tasan zuwa anjima zasu iya haurawa.

Shikam loma biyu yayi ya hak'ura da ci, don gaba d'aya ba d'and'ano.


         *UMMYN YUSRAH*

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now