25-26

618 45 0
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Wannan shafin nakane, santalelen saurayi, mai zubin Mazan novel*

*Saifullah Lawal Imam ('Dan Imamu) or (Comrade)*

_Ina masu neman mijin novel ku garzayo ga 'Dan Imamu, mata hud'u zan auramai rana guda, kedai ki tabbatar kina da kirar matan novel._



          *25~26*

Lokacin dana tashi naga an sukemin riga, 'yan k'irgen dangin nawa duk an mammatse minsu, jan rigata nayi na d'au mayafina na yafa na fita ina Allah ya isa, ba kowa a d'akin haka na fita.

Yamma hata farayi, gurin kayan talla na, na nufa ban sami wacce naba ajiyar ba, gaba na ne ya shiga lugude, idona ya kawo ruwa, ina tunanin kardai guduwa tayimin da talla na, indai hakane bansan irin azabtuwar dazanyi gurin Innata ba.

Don ita sam batasan asara ba, akwai wani rana dana maida mata abinci bai k'are ba, ranar na azabtu da duka da zagi, har tamaula takeyi dani tsabar duka, wai naja mata asara, meyasa ban kai har dare ba inya k'are in dawo mata da kud'in ta.

Saida ta k'irga abincin na naira d'ari biyu ne, tace duk randa na sami kud'i sana biya ta, kuma ko afatar bakina, ma almajirai zata bada, inkuma shirya fita da koko anjima.


Ina kuka ina tuna dama ba itace mahaifiya taba, uwar da bata damu da rayuwar 'ya'yan taba, burinta kawai mu nema mata kud'i, koda kwana mutum zaiyi da talla a waje ba damuwar ta bane, damuwar ta kawai, akawo mata kud'i kuma kar a dawo mata da komai, sai kud'i.

Har sha'awar yaran mak'otan mu nake, sukam basu talla, daga makarantar boko data allo sai gida, mahaifiyar su na sana'a amma a gida ake saye, idan ko naga suna sallah har sha'awar su nake, don nikam rabon danai sallah ma na manta, tunda muna hada-hadar cinikayya abakin kasuwa da tashi, ai ba zancen sallah, toh koda nazo yin sallarma bansan me zan fad'a ba.


Itama kanta Innar tamu saita had'a salloli uku ko biyu kafin takeyi, da dare kuwa, kafin mu dawo talla tayi bacci, asuban fari kuma an tashi, sai an gama had'a wuta an d'aura girki akeyin sallah.

Abu kaman wasa tun ana latsani ina k'i, har nazo nazama inakai kaina don inajin dad'in abun da sukemin, talla na kuwa nan danan yake k'arewa.

Idan nafita tallan dare kuwa sai lokacin da akaganni, Baban mu baida ikon magana don daya fara Innarmu zata hayayyak'o mishi.

Shekaru na tafiya girma na k'aruwa min, ina k'ara gogewa a harkar, ga rashin kunya, kamar bayan daya goyi shege, duk girmin mutum idan yamin ba dai-dai ba, nakan mishi wankin babban bargo.


Inada shekara sha biyu, wata Hajiyar birni mai d'iban yara takaisu aikatau, tazo d'iban yara, nan Innata tace in shirya in bisu.

Haka ta kwashemu mu goma, ta taho damu, ina mota ina kukan rabuwa da garinmu, wanda bansan tsawon lokacin dazan d'auka ba kafin nazo ganin gida.

Awannan lokacin na k'ara jin haushin Inna ta nason kud'i, ita sam bata damu da wani irin hali da rayuwa yaro zai fad'a ba burinta kud'i da abun duniya.

Tunda muka shigo birni aka rarrabamu gidajen masu kud'i, don aikatau, tundaga lokacin muka rabu da junan mu.

Gidan wata Hajiya aka kaini aiki, ma'aikaciya ce, ita da mijin ta da yaran ta biyu, duk wani aikin gidan  ni keyi, girki kuwa sai taga dama, mafi yawan lokaci sayowa akeyi, gashi bata fiya zama a gariba.

Idan tana gida kuwa ba k'aramin aiki nake shaba, kuskure kad'an kuwa zata kama jibgata kamar jaka, hatta bahaya idan tayi saita k'irani nazo nayi fuloshin.

Kai na bautu iya bautuwa, awannan gidan na fara sanin d'a namiji, don duk iskanci na a k'auyen mu baya wuce, ruguma da shafe-shafe, sanadiyar rashin zaman matar gidan yasa mai gidan ya sami daman shak'e ayarsa dani, duk dare zai d'irkamin wani k'waya wai na hana d'aukar ciki, yayi shagalin sa ya cikani da kud'i yayi gaba.

Abu yazama na ko tana gari, zai biyo dare yayi na kud'in sa yayi gaba, tunda d'akinsu d'aya ba d'aya da ita bane, kowa da d'akin shi, acewar ta baya barinta tayi ishashshen bacci idan suna d'aki d'aya.

Wani rana da daddare ya lab'ab'o zaizo, matar tashi itama ta fito daga d'akin ta, ta tsaya ganin ikon Allah, hannu yasa zai murd'a mabud'in d'akin kawai yaji magana daga sama tana tambayar ina zai shiga, kame-kame ya shigayi, can yace mata ruwan zafi yakeso inzo in dafamai, ya duba duk fulas d'in gidan babu.

Tace ita meye amfaninta dazai zo d'akin 'yar aiki cikin dare, nan taita mishi masifa, washe gari kuwa tace in had'a yanawa-ya nawa inbar gidan.

Direba tasa ya kaini gidan matan data kwasomu, tace ya gayama ta dattijuwa takeso.

Kwana biyu da korata aka kaini gidan da kika sameni, yanzu haka shekaruna biyar a gidan, nanma da yaron gidan muke shek'e ayarmu ba tare da uwar ta sani ba, shiyasani a wannan makarantar, bankoyi firamare ba, amma inada da takardar shaidar firamare, nanma danai jarqbawar k'aramar sakandare aji biyar aka kaini, wani rana naje d'akin shi zamu sha shagalinmu, kwatsam saiga Hajiyar shi nan ta korani wai nazo har gida ina lalata mata yamu, dama andad'e ana gayamata tak'i yadda.

Yanzu haka ina shirin komawa k'auyen mu, tsawon shekarun dana b'ata ba abun kirkin dana tara, bokon ma zaiyi wuya in k'atasa.

Nace
      "Sannu da k'ok'ari, bashi tara kud'i ba kinyi asarar mutuncin ki."

"Bari kawai, abun na cimun rai burin, iyayenmu masu turomu wani gari da sunan aikatau ba k'aramin kuskure suke tafkawa ba, basusan wani irin rayuwa mukeyi ba, burin kawai mu aikatau mu turamusu da kud'i."

"Allah kyauta. Amma inda hali ki bari ki k'arasa karatun ki, inyaso saiki koma."

"Ai wajen zamanne aiki! Yanzu ma wata baiwar Allah ta bani mazauni, na gaji da bauta, dana nemi wani aikin."

"Saiki rok'eta ta barki zuwa ki zana jarabawar ki, idan kuma nayi sure kafinnan, sai kidawo gida na kina mana aiki."

"Humm!" Kawai tace don tasan magana ta watsa mata.




     *UMMYN YUSRAH*

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now