45-46

958 53 5
                                    

SAINA AURI MIJIN NOVEL*

                                     🤴🏻

       *NA*
            *UMMYN YUSRAH*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

_*Inayima d'aukacin al'umman musulmai barka da gabatowar watar Ramadan. Allah yasa muna da rabon gani, ya karb'i ibadunmu yasa muna daga cikin bayin sa 'yantattu.*_

🔚💃🏻🕺🏻

            *45~46*

Sai daf magriba su Asmyy suka iso gida. Kai tsaye gidansu ta wuce, su Inna Lantai kuma sukayi gidan su Meenah.

Suna shiga sauran mutanen da suka rage sukayo kansu suna musu sannu. Kan tabarma suka zazzauna, Baaba Sharai tace

"Kubamu ruwa da abinci don Allah kafin k'ishi da yunwa suyi ajalinmu."

Wata daga gefe tace

"Habba Baaba! Kawai k'ishirwa da yunwa ta wuni guda kawai sai tai ajalinku?"

"Iyy kai! Ai a irin wannan yanayin da muka shiga ba sai bindaga ce zatai ajalin kaba iya yunwa ma ta isheka."

Wata daga gefe tace

"Yunwa kuma! Munan muna ta k'orafin kun daga kai amarya kun samu gidan mak'o kun mak'ale, kunata dagargazar gara, yanzu kuma kyace yunwa?"

Wanni kallo ta bita dashi irinna yarinya bakisan komai ba d'innan.

Abinci da ruwa aka kawo musu, sunci sunyi k'at sannan suka jero sallolin dake kansu.

Bayan sun nutsu akaso jin labarin amarya da muhallin da aka kaita.

Nan Lantai ta kwashe labari kaf ta fad'a musu, mafi yawansu daka kalli muskokinsu zakasan murna suke da hakan, suna ala k'ara maganin mai kwad'ayi.

Umman Meenah dake jinsu ta tausaya ma rayuwar 'yar tata matuk'a, ta kuma yi musu fatan samun sukuni da addu'ar Allah rabosu da wannan jejin su fito gari.

*GIDAN ALHAJI MUTARI*

Zaman su Marka da amarya ba yabo ba fallasa, sai dai abun da ba'a rasa ba, tunda hausawa sunce "Hali zanen dutse."

Meenah sati guda da kaita ba miji ba dalilin shi, tun bata iya cin abincinsu har ta koya, don taga yunwa na barazanar aikata k'iyama.

Gaba d'aya yanzu nadama ya shigar mata, da kaganta bazakace Meenah 'yar fara 'yar gayun daka sani ada bane, fatar da aka k'one shi da man haske duk ya fara dishashewa, kaya kala biyun da tazo dashi, dashi take gwagwar maya.

Babban damuwar ta ina kayan da aka taho mata dashi, har yau ko tsinke bata gani ciki ba. Wani abun haushin ma ashe yana da mata harda yara uku.

A daren ranar data cika sati ranar Yahuza wanda abirni akece ma (Yasir) a birni ya dawo. bayan ya rabama yara oyoyo yayi d'akin uwargidan shi, yad'au tsawon lokaci kafin ya nufi d'akin amarya Meenah.

Tana zaune ta gama cika, k'iris take jira ta fashe.

"Assalam! Amarya bakya laifi, kin ganni sai yau! Ya zaman kad'aici da bak'in ta?"

Nan fa ya k'ara tunzura Meenah. Mik'ewa tayi cikin zafin rai tace

"Dole kace haka mana! Azzalumi, mak'aryaci, mayaudari. Ka raboni daga garinmu cikin 'yan uwana da dangina ka kawoni wannan sunkurun jejin, toh wallahi ka kwana da shirin ba zama zanyi anan........"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 02, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now