7-8

804 50 1
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


*Wannan shafin naka ne, Kamala Minna, duk mai neman Mijin novel tazo ga Kalama😍😹*


*Real me Dambu na gode da feji, kici gaba da daga kwalabe amma na maltina, kici gaba da watsa kafso amma na amoxil, Ummyn Yusrah da Labeeb na tare dake*❤🤝


            *7~8*

Tsawon sati biyu kenan, ina shafa maina, amma ba wani canji ko kad'an, nanfa na fara tunanin dubu na, da alama nayi asarar tane.

Zaune nake a aji, ana darasi amma sam hankali na baya wajen, tunani na inda zan sami kud'in sayan wani man.


Gashi duk samarin da suke zuwa guna na kore su, don sam basu kama k'afar za'bi na ba, wani abun haushi ma wai saurayi inzai baka kyauta baya wuce 'yar dubu biyu,  ko mezaka saya da dubu biyu ohho.

Tunowa nayi da *Mijin novel* masu kyautar miliyoyin nairori ba tare da akawunt dinsu ya girgira ba, habba ni ai sai *Mijin novel*.

Maganar da akemin ne ya dawo dani daga duniyar tunanina, sake maimaita maganar tayi, azaton ta banji me tace bane.

"Don Allah barin zauna."

Matsa mata nayi ba tare da nayi magana ba, sabuwar d'aliba ce amma tafine gogewa don ko a ajinma ba kowa take kulawa ba.

Muna zaune naga ta bud'e jakar ta ta ciro wani d'an roba kamar gidan makilin, ta tatso abu saiga mai ya fito, ta mutstsuka ta shafa a hannun ta da fuskar ta, sannan ta mayar ta d'auko hoda ta shafa.

Nidai kallon ta kawai nake da gefen idon, tunda idona yakai kan d'an man data shafa naji ina buk'atar sanin ko na menene, can na kasa hak'uri nace

"Don Allah ko kina da man baki ki sammin."

Batai magana ba tasa hannu cikin jakar ta ta d'auko min, garin jawowa abunda nake son tambaya ya fad'o, saurin d'aukowa nayi kafin na mik'o mata saida na karanta sunan man, naga ashe irin namu ne, mik'a mata nayi taban man leb'en na goga.

Can dai na kasa hakuri nace mata

"Don Allah wannan man naki yana aiki sosai kuwa?"

Wani kallo tamin tana yamutsa fuskar data gama haske da mai, arai na nace wai! wannan badon hasken ba da bazata ganuba don muni, ita wai adole yanga take a hakan.

"Wani mai kuma?"

"Wanda kika shafa, akwai  wanda na siya har guda biyu dubu d'aya gashi har ya k'are baimin komai ba, shine nakeson canzawa."

"Manne kika sai na dubu d'aya? toh wannan d'ari biyu da hamsin nake sayanshi, kuma kinga ya karb'e ni, wani aiko basilin ya shafa yana mai bilicin, ki gwada sayan wannan ko zai miki."

"Zan gwada idan nasami kud'i."

kalon mamaki tamin sannan tace

"Kina mace kice d'ari biyu da hamsin ta gagare ki."

"Eh man! Wanakeda dazai bani?"

"Baki da saurayi ne."

"Duk na korasu, basu wani motsi."

"Lallai da sauran ki, barin baki wanda na ke amfani dashi ki gwada inada wani."

Tundaga ranar muka k'ulla k'awance da Safiyya (Matar manya) zama da ita yasa na koyi abubuwa da yawa kamar sanya breziya mai acuci, sanya wando biyu ko uku kafin sanya siket don k'arin mazaunai, k'arin gashi, salon tafiya, canza murya.

Nan danan na fara kilewa, gashi man ya karb'eni, maimakon yasani fari sai yasani ja, hakan ma nagode.

Shigowa nayi gida a gajiye, ga rana ga gajiyar hanyar makaranta, Yaya dauda dake zaune shida Ummah suna hira nazo giftawa na mishi sannu kallo ya bini dashi, harna wuce yace

"Amina zonan."

zuwa nayi na tsugunna, kallo ya gama k'aremin sannan yace

"Kema kin fara shafe_shafen zamani ne, naga kin fara ja kamar gauta."

Gabana ne naji ya buga, nace

"Ni! bana shafa komai, iyakana basilin."

"K'arya kikeyi muna fuka wannan jan naki bana basilin bane, kina nufin ban san kalanki bane kome?"

Ummah tace

"Yauwa! aigara ka tuhume ta, nima danai maganar hasken ta k'aryatani tayi."

"Ai Ummah ke kike barin ta, ai wani iskancin nata harda rashin duka, wuce muje d'akin naki inga irin man."

Mik'ewa nayi jiki ba kwari, ina gaba yana bina a baya har muka shiga d'akin, nidai yau nasan kashina ya bushe, idan yaga mannan.

Kai tsaye kan 'yar durowar kayan kwalliya na ya wuce, ya fara duddubawa, babban wautar daniyi shine rashin zubar da robobin man da suka k'are, yace

"Kince baki shafa komai! wannan waye ya shafa eye?"

"Um.. um..um tsintosu nay........."

Marin daya kwad'amin shiya katse min magana da nakeyi, ban ware da zafin marin ba ya kaimin naushi saida na zube a wajen, ya sake kaimin duka da rarrafe nayi k'orar d'aki, ina isa na mik'e nayi tsakar gida a guje, d'ebo robobin ya biyu ni waje yace

"Kalla Ummah! tsabar ta raina mana hankali tace bata shafa komai."

Sake caf koni yayi ya rufeni da duka kamar Allah ya aikoshi, yana cikin jibgata yaya 'Danladi ya shigo, yanajin ba'asin zance ya rufeni da duka shima, Ummah dake gefe tana ku k'ara mata.

Saida sukamin lilis suka tatse man tsaf ak'asa suka k'ona robobin sukayi gaba.

Mik'ewa nayi ina d'ingishi ina Allah ya isa.

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now