17-18

693 38 1
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Wannan shafin nakune 'yan gruop d'in Mermue Novella, naji dadin koment naku, Allah yabar kauna, ana mugun tare🤝❤*


            *17~18*

Umma dake tsaye k'ofar kicin sake k'wala ma Meenah k'ira tayi a karo na biyu, fitowa tayi tana mutstsuke ido alamar bacci take.

Sanda ta fito sam ban ganeta ba, don gaba d'aya ta tashi daga Meenah bak'a ta koma Meenah fara.

"Gani Ummah."

"Yawwa! Zonan ki k'arasa min girkinnan na riga na zuba wake, idan yad'an sulala, kiyima shinkafar wanki mai kyau, saboda akwai k'asa sosai, sai ki duba. Ga barkono ki daka, man ki soya, zan shirya in fita gidan su Badi muyi aikin bikinta, karsuga banzo ba suji ba dad'i sunda sun aiko min."

"Toh."

Kaida kaji amsawar kasan baikai zuciba.

Nafi minti biyar tsaye a k'orar kicin, ina nazarin ta ina zan fara, don wani irin hayak'i ne ke fitowa daga ciki, wato wannan uwar hayak'in zan shiga kenan, aiko idan nai wasa yau saina rine.

_Sake k'are mata kallo nayi inga yadda za'ayi ta rine, don kawai tayi girkin lokaci d'aya, ai mugun mamaki ne ya kamani, ashe da fari kallon tsoro na mata, yanzune namata kallon k'urullah._

_Sunan wani abun jeji wai Zebra, ashe fuskarce fari tas, sauran jikin bik'i k'irin, hatta hannayen ta, wanna ita ake k'ira da kala biyu_🤣

Haka na k'utsa kai ciki don ba yadda na iya, gaba d'aya tunanina ya koma kan *Novel* da wuya 'yan birnin cikin *Novel* kaga suna aiki da itace, sai dai a k'auye, shima kuma yaran k'auyen *Novel* ko kad'an basu dawwama cikin talauci, k'arshe birni suke zuwa su auri maza masu kud'i da mulki, ko kuma 'yar talakan *Novel*, wani abun haushima wai shinkafa da wake, garau-garau ko d'an ganye babu.

Nasha bak'ar wahala da itacennan ga kicin a tak'ure, ga hayak'i ga zafi, hawaye da majina kam na zumbar dasu ba iyaka.

Allah sarki *Mutanen Novel* komai naku dabanne, ko kudame kuke girki ohho, gashi cikin k'ank'anin lokaci kunyi girke-girke sama da goma, ni d'ayama nafi awa ina fama, ahakanma wai anragemin hanya.

Ban kumajin k'arin haushiba saida na gama girki, nazo rabon abinci, kwandon kwanukanmu ko na 'yan k'auyen *Novel*  bai kaiba.

Wasu tarin tarkacen kulolin robane, da wani tsohon kwanon silba waishi cika duba, sai 'yan tsirarun kofi, cokali da wata wuk'a itama har mak'ota aronta suke, wannan kayan takaici dame yayi kamane kam.

Tunanina ya k'ara lulawa kicin d'in *Novel* sukam babuce kawai babu a ciki, bayan na gama na kaima kowa d'aki na ajiye, tunda bamu da falon cin abinci.

Da yammaci lis, bayan na gama aikin na share gidan na d'au wanka na ina jiran dawowan Ummah har yanzu bata dawoba, so nake inma Matar Manya yau dirar mikiya, gashi Ummah shiru, ga wayata ba data balle in bata lokaci, d'arin da nake da kuma Napep nakeson shiga.

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now