31-32

610 41 0
                                    

SAI NA AURI MIJIN NOVEL*

                                        🤴🏻

               *NA:*
                     *UMMYN YUSRAH*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


*Wannan shafin naki ne, Sanah s Matazu, ina godiya matuka Allah yabar zumunci.🤝🏻*


         *31~32*

Marka ta gama shirin ta tsaf don zuwa gidan su Aminiyar ta Zulai, ko sallama bataima abokiyar zaman nata ba tayi gaba.

Tafe nake gaba d'aya jiki na a sanyaye  yake, ga wani fad'uwar gaba da nake ji, dana tuna irin rabuwar damukayi, da korar dana mata, nasan taji zafi sosai, badon haka ba da tasake zuwa, don mun saba fad'a bama d'aukan lokaci kuma muke shiryawa, fad'anmu na k'arshe shine ranar aure na, tunda suka kawoni suka tafi ban k'ara ganinta ba, sai ranar da tazo muka sake fad'a, kai gaskiya Zulai akwai hak'uri, din duk mai zama dani saiya shirya, yayi hak'uri da halina.

Ni kaina yanzu halin nawa na fara gajiya dashi, don bai jamin komai ba sai aikin danasani da nadama.

Haka harna isa gidan zuciya ta na sak'e-sak'e, da sallama ta na shiga gidan, mahaifiyar Zulai na gani a tsakar gidan, kallon mamaki ta bini dashi sannan tace

"Marka!! dama kina duniyar nan? Lallai zaman gidan miji yayi da......"

Kafin ta k'arasa na katse ta da cewa

"Ina kwana Innah?"

"Ummm! Lafiya Zule, ya maigida da yaran? Ya bayan rabo kuma?"

"Lafiya lau Innah."

"Toh, Madallah."

" Innah Zulai na nan kuwa?"

"Yanzu ko ta fita, amma batai nisaba, tunda aka fara shirye-shiryen bikin nan bata samun zama, shiga ki jirata."

"Toh Innah."

Shiga d'akin nayi nazauna kan wani kujera guda d'aya dake d'akin, k'arema d'akin kallo nayi, duk da d'akin 'yammatane sun gyarashi tsaf gwanin sha'awa, ba wasu tarkace ciki, ga wani iska da kamshi dake kawo ma hancina ziyara.

'Dakina na tuno yadda na fito na barshi ahargitse, rabona da in gyarama zan iyace na manta, gawani tsami dake tashi, kana kunna Lanka zai maka maraba lale da zuwa.

Garama gidan da d'akin girki da band'aki suna samun gyara, tunda aka kawo min mai aiki.

Haka naita sak'e-sak'e, iskar fanka na kad'awa, ni'imar d'akin na min dad'i, har wani nishad'i na keji, nanfa na cire 'yar galen dana yafashi a kafad'a, na sake gyara zamana, don gyangyad'i ne ya fara d'ibana.

Sallamar da akene tayi sanadiyar farkawata daga baccin daya d'aukeni mai d'an karan dad'i, tsaye take a bakin k'ofa  tana min kallon mamaki, sannan tace

"Toh! Da alamu yau b'atan hanya kikayi ko?"

" 'Batan hanya kuma?"

"Eh man!"

"Ba b'atan hanya nayi ba, nazo biko ne."

"Biko! Wayayi yaji?"

"Ke man!"

"Ai ba yaji nayiba, korata akayi."

"Hakane! Natuba, na gane laifi nayi amin hak'uri."

"Ba komai, ya wuce ai, ya yaran?"

"Suna lafiya."

"Hakan akeso, ya amarya naji ance anmiki 'yar uwa."

" 'Yar uwa! Hummm! Wannan ta wuce 'yar uwa, tazama mai gidan."

"Toh! Garin yaya hakan ta faru? Zancen na zama ne, koromin insha."

Nan ta kwashe komai ta gaya mata, dogon numfashi taja sannan tace

"Kishiyar ce kika d'auketa a 'yar aiki? Kishiyar kika sakarma da dukkan ragamar gidan ki? Hak'ik'a kinyi babban kuskure, kuma dukkan abunda ya faru ke kika jawa kanki, lokacin danake gidanki saida nai miki magana kan yanayin gidan da yadda zaki gyara zamanki da mijin ki, amma wani tunanin banza da hofi, gashi yanzu kin zama 'yar kallo kin zama borar cikin gida, wacce tazo daga bayanki ta k'wace ko na gidan."

"Hummm! Bari kawai, nazama abar tausayi cikin gidan, idan kinga yadda Alhaji yakeyi zaki zaton ba cikin hankalinshi yake ba, kai inagama asiri ta mishi."

"Hahahaha! Kinban dariya wallahi, wai asiri, babu asiri ko kad'an karki manta namiji nason, kulawa, kikeyi, tsafta, kula da cinsa, shansa, muhallinsa, dukiyarsa, duk dai wani abu daya kamata, idan ya samu hakan toh fa kingama sayenshi, ciki ki gayamin wanne kikeyi? Nasan amsan babu ce, toh  kinga yasamu mai mishi dole ya susuce, don haka kiyi k'ok'arin nemo hanyar gyara,  tunkan wankin hula yakai ga dare."

"Tayaya zangyara? Gaba d'aya kwakwalwata ta tsaya can ta daina aiki, kiban mafita don Allah, abaya nayi wauta, yanzu kam nayi nadama."

"Hummm! Dole ki koma ki gyara duk kuren da kikayi cikin gidanki, ki nemi yafiyar mijin ki, ki zauna da kowa da zuciya d'aya, sannan ki kula da kanki."

" Ta yaya zan kula da kaina?"

"Ta hanyoyi da dama bq tare da kinje kin sayi kayan gyara da zaki illata kanji ba, mata yawa na sayen Mayan gyara wajen mutanen da basusan same suke had'asuba, da munji tallan magani ance Nada kyau burinmu mu saya Muna muyi amfani dashi, batare da samun illar da zai manaba, June shawannan sha wancan, kusa wannan, kusa wance bamu damu da illar da zai manaba, ko yama mazajen mu, burin mu kawai mu budge miji, idan mun burge shi kuma mukazo, daga baya muzo mu  sami Matsala wa gari ya waya? Akwai abubuwan dazamu had'a da kanmu, akwai na musulunci musu inganci bila adadin, don haka kiyi k'ok'arin amfani dashi, zaifi miki."

"Don Allah ki gayamin, don bansan komaiba."

"Zan fad'a miki, muje muyi sallah tukunna."




_Amin afwa da kurakiren da za'a gani ciki,👁 ke ciwo._

*UMMYN YUSRAH*

SAI NA AURI MIJIN NOVELWhere stories live. Discover now