PART 16-20

2.1K 77 1
                                    

💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_

💠💠
🌹

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*INA KUKE ONLINE WRITER'S 🔎, ARADU WANNAN PAGE NA MALLAKA MUSHI KYAUTA,SABODA K'AUNAR DA NAKE MUKU,BAN RAGE KO GUDA DAGA CIKINKUBA,INA ADDU'AH DA FATAN UBANGIJI YA HA'DA KANMU,BAKI 'DAYA......🌏 FATAN ALKHAIRI GAREKU Y'AN UWANAH MARUBUTA....* 📝📚


*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*

*℘ąɠɛ 31↔32*


Boss kam yana shiga,toilet ya nufa,banyan yayi wanka,ya zura kayan shan iska,ko ta kan abinci baiba,yabi lafiyar gado cike da mafarkai iri² masu dad'i.........

Ganin an barsu su biyun mamy na kitchen,itama little ta bi bayan jiddah da ta tsufa a sama......
Kwance ta tarar da ita, ido rufe kamar mai bacci,magana tayi taji shiru,ganin hakan yasan ba bacci takeba,tab'ata tayi,nanma bata kulataba,sai ido data bud'e tana kallonta,tare da d'aya gira d'aya...........
"Ke yanzu ya zamuyi Boss ya dawo,kinga muna tsaka mai wuya,ga wani uban warning da ya ajiye mana,dole mu shiga hankalinmu,idan ba hakaba,zai mana babu dad'i", little ta fad'a face enta da alamun damuwa............
Banza jiddah tayi mata,sai ma idonta da sake kullewa kamar mai jin bacci.......
"Ke wallahi matsalace da ke,idan wannan banzan miskilancin naki ya motsa,uban kowama yi masa kike", cikin jin haushi little tayi maganar,ganin tak'i kulata yasa ta mik'e ta bar gurin zuciyanta fal haushin iskancin jiddah.......
Kome ta tuna,tana kwancen tayi saurin mik'e wa, har sai da little en ta kalleta,amma ko a jikinta haka ta mik'e ta fice daga d'akin,sauka tayi ta nufi kitchen, mamy ce ita da baba Laure suna aikin had'a dinner,shigowa tayi tana taimakawa har suka kammala...........

Dai² lokacin ana kiran Maghreb Boss ya sakko daga da niyyan tafiya Masjeed,zaune ya samu little a parlor ta kafawa TV.ido tana kallon drama,kallonta kad'ai yayi lokacin da yake k'arasa sakkowa.........
Fitowanta kenan daga kitchen d'auke da Warmer's, ta nufi dining area,ajiyewa ta shiga yi,kamar kullum.........
Kallonsa ya kai kan little,zaune take tana watching drama,a hankali cikin takunsa ya iso gabanta,duk hankalinta na kan abunda take,kunnenta ya kama ya ja.......
"Autch!!! Ta fad'a tana dafe gurin,tana bashi hak'uri,amma yak'i sake mata kunnen,saima murd'ewa da yayi,kamar ya samu kayan wanki............

Mamy da fitowanta daga kitchen zata je yin sallah ta gansu a haka,kai ta jijjiga,tana fad'in "me yene haka kam,kai babu daman ku zauna lafiya,sai kace wasu Tom n Jerry,sake mata kunnen da kake murd'awa,kar ya fice,koma ina masallaci zaka ka tsaya nan sai an idar da sallan", tana had'e face...........
Sakin mata kunnen yayi,had'e da sakar mata wani mugun nock a tsakiyan kai,dafe gurin tayi,ta sake sakin wani k'aran.........
Sunkuyawa yayi yana fad'in "ko ki rufemin bani ko yanzun na karyaki,dan uwarki kina zaune a nan,kin barsu da aiki ga bayinki,dole su gama su baki kici ba?.........
Allah ya bakin sa'a in sake ganin ki a nan kina zaune su suba aiki kiga yanda zanyi dake,Allah saina mugun sab'a miki,ko tunanin sallah bakiyiba bare taimaka musu,kinzo kin hard'e k'afafu,ke ga hakima koh,me yasa y'ar uwarki ita bata zo ta zaunaba,saboda bats son ta hutane ko kuwa? To Allah bakinta sa'a na dawo na tarar dake a nan a zaune,kiga yanda zanyi k'wallo da ke,sha³"...............
Yana gama bambamin fad'an nasa yayi hanyan fita jin an tada sallan,ya k'ara sauri,haushi duk ya ci ka shi,da bai biyewa shashancin wannan yarinyarba da bai makaraba,haka ya k'arasa masjeed en...........

Jiddah dake cikin kitchen ta fito tana dariyar mugunta,harda zama saboda d'aci da taji,tana Allah k'ara wa little, hawayen dake sakkowa daga idonta,suka k'ara k'aimi wajen zubowa,tana fad'in "Allah sai ya sakamin,mutu ba abunda aka masa amma sai bak'in mugunta, daga dawowansa,amma ya dawo kamar wani dodo zaisa ayita shayin masa magana,ta ci gaba da surutanta,tana share face enta..........
Jiddah da ta saki bani tana kallonta,tana ta faman sakin magana,ta ce "maza ki je ya shigo ya ji me kike cewa,wllh kin dai san ba k'yaleki zaiba,zaiyi k'uli² dake ne,garama ki sawa bakinki linzami,yarinya"..........
Ganin tak'i yin shiru sai magana take fad'a duk wanda yazo bakinta, gashi an idar da sallan,juna tak'i yin shiru, yasa jiddan cewa "woooo!! Ga Boss nan shigowa", ai da gudu little ta b'ace daga parlor, d'aki ta shige,nanma bara tsayaba sai a toilet, ta kulle k'ofan.......

RAYUWAR WANI.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now