PART 31-35.

1.6K 72 0
                                    

💠💠 *RAYUWAR WANI......*       
             _{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_

                  💠💠
                     🌹

*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *25/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*~_________________________~*
  *ADDU'AR SANYA TUFAFI.*

_ALHAMDULILLAHIL-LAZIY KHASANIY HAZAS-SAUBA WARAZAK'ANIHI MIN-GHAIRI HAULIN MINNIY WALA QUWWATA..._

          *_~#HISNUL MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*


*℘ąɠɛ 61↔62*

Cikin sauri ta shiga wanka,ta shirya....
Har zuwa lokacin LITTLE bata shigo ba......
Tana fitowa daga wanka ta d'auki waya coz bata son tafiya ita d'aya,tun tasowarsu har kawo yau d'aya bai tab'a fita ba tare da d'aya ba.....
Kira ta dannama LITTLE,tana mamakin ya akai ta jima haka a gurin FAROUK,ita da ba a son ranta ta zauna ba.....
Murmushi tayi,kafin cikin sautin da ba kowa zai iya fuskantar me tace ba ta furta
   ''Ana so ana kaiwa market,su LITTLE an iya gulma,bari tazo zamu had'une''.....

**************

''Daga d'ayan 'barin kuwa LITTLE ana tsaka da zuba love kiran JIDDAH ya shigo wayanta dake hannun FAROUK,mik'a mata yayi,tasa hannu biyu ta amsa.....

Cikin sauri ta d'aga tana fad'in
    ''CWEETY ya ne?''.....

''Kefa muke jira MAMMY tasa mu shirya zamuje taron DADDY airpot,tun d'azun nake zuba idon ganinki''.....
Ta k'arasa tana sauraron abunda LITTLE zata fad'a......

''Eyyahh ganinan zuwa ki kammala shiryawa kafin na k'ariso''.....

''OK'' Kad'ai ta fad'a tayi hanging up na kira....

Cikin sauri take komai har ta kusa gama shiryawa amma shiru LITTLE en bata shigoba.....

Sake kiranta tayi,tana d'auka kuwa JIDDAH tahau fad'in
    ''Amma dai baza kiba ko ?
To ba driver zai kaimuba,YAH BOSS ne,kuma kina sane da yanda ya tsani jira''....
Tana gama fad'an nata uzurin ta sake katse kiran,ko bari taji me LITTLE en zata fad'a bata yiba......

Cikin wani rantsatstsen tsadadden lace sea green mai yarfen storns pink ta kammala shirinta,plat en shoe taja tasa pink colour shima,had'e da yalwataccen vail,tayi rolling nasa bisa kanta.....
Ko tsayawa d'aura head tie en batayi ba tayi waje.....

Dai² zata sauka daga stairs en ta hangosa ya hard'e kan sofa,tun d'azun sai faman duba agogon dake d'aure bisa tsintsiyar hannunsa yake na rolex......
'Dagowa yayi ya dubi hanya,jin sanyayyen k'amshinta dake nufosa....
Ko k'arasa sakkowa bai bari yia mik'e cikin takunsa na isa ya nufi hanyan fita....

Da ido ta rakasa,maimakon ta bisa saima hanyan bedroom en MAMMY da ta nufa....
Knock!Knock!!
  Kafin ta murd'a handle en k'ofan ta shiga,da sallama....

MAMMY na tsaka da duba magazine ta amsata,cikin sakin fuska ta kalli JIDDAH dake ta faman doka smile,uwa wacce akama bushara.....

''Sai tafiya kenan?''
Tayi tambaya tana mai kallonta...
''Ehh MAMMY buh LITTLE fa bata shigoba har yanzun kenan babu ita zamu tafi?''.....
Idonta uwa zai zubda ruwa ta k'arasa maganan....

RAYUWAR WANI.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now