PART 46-50.

2.2K 88 3
                                    

💠💠   *RAYUWAR WANI......*       
             _{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_

                  💠💠
                     🌹

*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *24/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU'AR BU'DE SALLAH.*
_BAYAN AN YI IK'AMA_

  _SUBHANAKALLAHUMMA WABI-HAMDIKA,WA-TABARAKSMURABBIKA,WATA'ALAA JADDUKA,WALAA-ILAHA GHAIRUKA_

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*
  🎂🎂🎂
        🎊🎉🎊

  🍻🍻🍻
  *HAPPY BIRTHDAY DEEZOH*

💃💃💃
    _May it be the best day of your life thus far, & may your happiness grow with each passing day through the many many birthdays that surely are ahead of you._
🎁🎁🎁🎁🎁🎁

   _Once again happy bufday sis *KHADIJA SALEEHU.*_
🌹🌹🌹
       🎂🎂🎂

💃💃💃💃

*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*


*℘ąɠɛ 91↔92*


    Rayuwarsu mai cike da tsafta haka suka ci gaba da gudanarwa, babu wani abu da yake hanasu nunawa juna soyayya da kulawa ko da kuwa a gaban waye..
 
  Yau tunda suka tashi take ta faman zuba masa SANGARTA shi kuma sai biye mata yake,duk abunda take yana biye mata..
  Tana kwance saman jikinsa,ta d'ago fuskanta uwa za tayi kuka,ta kalle shi,shima itan yake kallo yana jiran jin abunda zata fad'a
 
''YAYANAH!''

''UHMM!Ina saurarenki HAYATEEYNA''

''Allah na gaji da zama guri d'aya,nifa tunda nazo ko bakin get ban tab'a zuwa ba,bare nasa ran zuwa naga MAMMYNA,kuma kai kullumfa sai ka je''

Dariya yasa mata,ita ko ganin yana son waske zancen tasa masa kuka

''Allah ni ka kaini naga MAMMYNA,in ba haka ba kuma''...

  ''In ba haka ba me?''
Ya tambaya yana sake mata dariya

Kuka sosai take tana bugun k'irjinsa,shi ko ya dad'a matseta a jikinsa,fuskanta ya rik'e,idanunta sai fidda hawaye suke
  Harshensa yasa yana d'auke duk wani layin hawaye dake fuskanta,k'arshe ya dire cikin bakinta,jin haka yasa kukan nata tafiya babu shiri,idanunta a kansa..

  Biye masa tayi sai da suka gama jagwalgwala juna,sannan yayi sama da ita yana tsokanarta,ita ko ko kulashi tak'i yi,haka yaita janta da fira iri² amma tak'i sakin jikinta..
  Wanka ya mata,abunda kullum tare suke amma yau saboda tana fishi tak'i kula shi,tsaf ya shiryata shima ya shirya,kayan da ya d'auko musu su suka sa ta kalle shi,bakinta da alamar tambaya,amma saboda tana fushi da shi ta k'i yin magana sai kumbura fuska take..
Duk wani motsi da take yana kallonta,sai da ya gama sannan ya d'aukota har packing lot ya direta,yana k'ok'arin bud'e motern ta bud'e baki da k'yar tace

''Wai ni YAYA ina zamu ne,naga ba kace min zan rakaka ko ina ba''

Murmushi kad'ai yayi ya bud'e motar ya sata,shima ya zagaya ta d'ayan b'arin ya zauna,har ya fice daga gidan bai ce mata komai ba,sai da suka d'auki hanya sannan ya juyo ya kalleta,sai faman cika take..
Kansa ya d'auke yana fad'in
  ''Yau kuma YAYAN ba naki bane?''

RAYUWAR WANI.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now