🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾
🌾 *(OUR PROVINCE)* 🌾
*Na Aysha Sada Machika*
*1*
Wani zamani can baya a wani yanki dake Arewacin k'asarnan, anyi wani gari mai suna *DULME.*
Gari ne daya tara d'umbin manoma, mafarauta, makiyaya, masinta, mak'era, masak'a da maharba.
Sannan kuma gari ne da mayu sukayi yawan gaske, sune ma likitocinsu a lokacin, Babu Addini mai k'arfi sai tsaface tsaface dakuma Ruwa da suke bauta mawa, suna kiran ruwan da suna (Abun bauta *ZUBA*).Amma saidai Al'adar garin sai wanda ke cikinsa, ko wad'anda ke cikin ma abun yana damunsu saidai babu yadda suka iya.
Sarkin garin DULMI wato *DIYARA* ya kasance Azzalumin Gaske yanada mata barkatai, ina nufin masu tarin yawa, saidai bashi da d'a ko d'aya. Al'adar Garin ne, duk ranar da Sarki ya haifi d'a Namiji daga Sanda yaron nan yakai shekara goma za'ayi bikin kashe sarkin a nad'a yaron tare da red'e fatar jikin Sarkin a shanya ta bushe abama sabon Sarki fatar domin yin shinfid'a kan kujerar mulkinsa, Allah kad'ai yasan tarin Fatar dake shinfid'e a kan kujerar sarautar don haka suke tun kaka da kakanni.
Sarki Diyara baya barin matansa su haihu, da zarar sun samu ciki zesa aje a kashe su, hakan yasa basa bari su samu ciki don suna son rayuwarsu, kosun samu ma sukan je wurin boka ko matsafiya ayi masu tsafi a zubar dashi.
Baya barin duk wata kyakkyawar yarinya data taso a garin, daya ganta zai maidata matarsa, kasancewar su basusan wani abu waishi d'aurin aure ba, saidai anasu auren shine, mace da Namiji zasu je wani keb'ab'b'en rafi nanan acikin garin Dulme, suyi zindir su shiga ciki suyi wanka ga mutane zagaye dasu ana shewa da ihu na tayas murna, sun yarda cewa wanda duk ya shiga ruwan nan be fito ba to ba abokin rayuwar d'ayan bane, ma'ana babu alkhairi acikin auren, Sarki ne da zuriyarsa kad'ai basu irin wannan auren saidai a d'ebo wannan ruwan rafin a basu su sha amma basa shiga.
Idan Sarki Diyara yaga yarinyar da tayi masa ze aiki wasu daga cikin manzonnin sa (y'an aike) da abun hannu mekyau zuwa ga iyayen wannan yarinya, da sun gani sunsan yana nufin yaga y'arsu yana so, memakon murna saidai su fashe da kukan bak'inciki domin auren azzalumi Sarki Diyara ba alkhairi acikinsa, kuma gashi babu yadda za'ai suk'i amincewa.
Sarki Diyara yanada wani gawartaccen boka ko nace matsafi me suna Zuruqum, suna kiransa da *Zuru*, Sarki Diyara baya aikata komai saida izinin Zuru, ya yadda da duk abunda Zuru ya duba masa.
Duk lokacin da ruwan sama ya sauko kaf mutanen garin Dulme, tsofaffi da yara, maza da mata zasu fito suyi sujada suna gungunai (surutai, suna rok'on buk'atunsu ga abun bauta Zuba), ruwannan yana dukansu amma haka zasu kafe suna rawar sanyi har ya d'auke, idan kuma bame d'aukewa bane da wuri harsai shugabannin matsafa Zuru ya basu izinin tashi.
Lokacin damuna lokacine da mutanen garin da yawa suke rasa rayukansu sanadiyar shiga ruwa da suke yanai masu d'anbanzan duka, amma acewarsu, sadaukarwa ce suke, duk wanda ya mutu a wannan yanayi ubangijinsu yana alfahari dashi kuma sunyi kyakkyawan k'arshe.
Sarki Diyara yakai kimanin shekaru sittin da wani abu (60+), amma duk da haka be dena kai hari ga k'ananan yaran garin ba, yara-yaran mata da be wuce yayi jikoki dasu ba, Sarki Diyara indai fa maganar matane to lallai besan iyakan wanda ya kwanta dasu ba, gashi baya wuce sati biyu yana kwanciya da koma wacece ze jingine ta gefe, tayita zaman bauta, ita da bayin gidan babu maraba.
Saidai abun mamaki duk yadda mutanen garin Dulme sukeda tsauri ga addininsu da al'adarsu, hakan be hana su samun saniyar ware ba.
******
*Arkisaaya* wanda mutane ke kira da *Saaya*, matashin saurayi ne me jini a jika wanda baze wuce shekaru 28 ba, dogo ne na mutunci, kunsan irin zubin mutanen da, a hausance mukan kirasu da "k'irar samudawa", Kyakkyawan gaske ne, saidai be cika haske ba kuma beda duhu.
Miskilin ne ajin farko, zaka dad'e zaune da Saaya kayita zuba shikam saidai ya bika da ido, idan kayi abun dariya sai yad'an murmusa batare da hak'oransa sun bayyana ba, kafin kaga abunda zesa Saaya magana gaskiya sai an tona.
Mahaifiyarsa mai suna *Annu* sai mahaifinsa *Manay* mak'era ne, suna zaune gida d'ayane tare dashi, a lokacinsu babu wani sunaye na girmamawa da suke amfani dasu wurin kiran mahaifansu da na gaba dasu, kowa da sunansa suke kiransa, sai mai sarauta ne kad'ai suke kira da " Maigirma"
Saaya beda tsoro ko kad'an, mutun ko aljan babu abunda ke tsorata sa, yanada wata iriyar baiwa, baiwar itace ; duk wani mugun abu daze tunkaro Saaya baya samun nasarar iskesa sai sunyi sab'ani kokuma idan ya zo yak'i samun ganinsa, Saaya be yadda da ubangijin da kaka da kakanninsu suke bauta ma ba wato ZUBA, hakan yasa duk lokacin da suka fara bautar ze koma d'aki yayi kanciyarsa ya lullub'e yanajin d'umi abunsa, Annu da Manay babu yadda basuyi ba don ganin sun tankwara sa amma abun yaci tura, kaf garin suna masa wani irin kallo na daban, wai marar addini, Annu da Manay suna son Saaya sosai kasancewar shi kad'ai suke dashi a duniya.
Idan Manay na wasa da Saaya yadda kasan abokai, haka shima Saaya be had'a kowa da iyayen nan nasa ba, sai budurwarsa wadda suke mak'otan juna me suna *Fauwa*, suna son juna suna zuba soyayya iya soyayya, saboda girma irin na Saaya, idan Fauwa taje d'ibo ruwa, haka yake binta ya d'aukota yakuma d'auko ruwan, baya direta ko ina sai gida.
Fauwa Mahaifinta ya rasu sai Mahaifiyarta kad'ai ta rage da yayyenta maza biyu da k'aninta namiji d'aya, kaf garin nan an sheda babu wasu masoya kamar Saaya da Fauwa.***********
*NAHIYAR MU*
Sarki diyara ne zaune bisa kujerar mulkinsa wadda tasha ado da fatu (fatocin) sarakunan da suka shud'e.
Fadar cike take kamar kullun, amma kowanne yana bakin aikinsa, shigowar Zuru yasa kowa ya tashi yabar wurin, hadimai kuma suka juya baya.Sarki Diyara cikin isa da k'asaita yace "meke tafe dakai? Sarkin matsafa na garin Dulmi...Zuru"
Zuru ya gyara zama sanna ya fara magana kamar haka,
"Abun bauta Zuba ya taimakeka yakai wannan gagarumin sarki na sarakuna gaba d'aya, ka dad'e kana mulki yakai mai girma Diyara, nazo ne na sanar maka ranar da ta fi dacewa ayi shagalin *Dulmirah* (wani biki ne da suke kowace shekara, kamar yadda muke bikin zagayowar shekara, mak'era su fito suyi wasan su, y'an bori dadai sauransu)".Zuru ya cigaba da cewa "Abun bauta ze saukar da rahamar sa a wannan babbar rana, saidai kuma...."
"Saidai me?" Sarki Diyara ya tambaya.
"Zakayi tsintuwa a wannan rana, amma tsintuwar me d'auke da had'ari dakuma barazana" Zuru ya k'arasa maganar kansa k'asa.
"Wane hukunci ka yanke game da hakan?" Sarki Diyara ya sake tambaya a tak'aice.
Zuru yace "Zuba ya taimake ka, bana tinanin wannan yak'in ze hau takobi na saidai zamu sake dubawa"
"Lallai ka duba sarkin matsafa" inji Sarki Diyara.
*************
"Abun bauta Zuba ya taimakeka yakai masoyina" Fauwa ce ta k'araso inda Saaya yake zaune yana jiranta"
Saaya ya mik'e yana murmushi ya janyota jikinsa gami da had'a goshinsu idanuwansa cikin nata, murya k'asa-k'asa yace "abun bautarku be isa ya taimakeni ba, ni kad'ai ke iya taimakon kaina"
"Aikai dama haka kake kullun" Fauwa ta fad'i haka gami da janye jikinta.
Suka nema wuri suka zauna, gabansa ta zauna bayanta na gugan k'irjinsa, shi ko ya saka hannuwansa ya tare gefenta yanata wasa da y'an yatsunta.
"Saaya inaso nafi kowace budurwa kyau ranar Dulmirah, saboda banaso wata ta d'auke hankalin masoyina, shiyasa zanci ado saboda kai"
Murmushi kawai yayi batare da ya sake cewa komai ba.
Fauwa ta cigaba da magana,
"Saaya ranar Dulmirah inaso karka matsa ko ina ka zauna tare dani, domin duk duniya babu abunda kemin dad'i sama da kasancewarka kusa dani, waima me zaka shirya mana ne a ranar?"Shirun da taji yayi ba tare da ya amsa ba yasa ta d'ago kanta ta kallesa, murmushi ya sakar mata.
"Tambayarka fa nake amma kayi shiru" inji Fauwa.
"Fau wasu lokutan ina zuwa wurinki ne kawai don na ganki nakuma saurari zazzak'ar muryarki, bawai don ki saurareni ko kiyiman tambayoyi ba"
Bayan da Saaya ya lumfasa sai ya cigaba da cewa "Fau bani da buk'atar shiri indai kina tare dani, na rantse miki da girman Iyayena bazan tab'a bari a rabani dake ba"
Fauwa tayi murmushi har saida hak'oranta suka bayyana tace "Masoyina Saaya wannan rantsuwar kullun sai na jita daga gareka, amma abunda ka manta shine, anta da jini basu tab'a rabuwa, ka dena tinanin rabuwa dani, koko don kaga *Kuyal* (babban yayanta) baya sonka? Bawai baya sonka bane ak'idarka ce baya so, ka daure kabi abun bauta Zuba, itace hanya madaidaiciya kuma shine abunda kaka da kakannin mu suka bauta mawa har gushewar su".
Saaya bece da ita komai ba, sai yatsunta daya cigaba da shashshafawa...........
YOU ARE READING
NAHIYAR MU...{Our Province}
Historical FictionRayuwar maguzanci awancan shuɗaɗɗen yanayin...