ƘADDARARREN AL'AMARI

1.8K 92 22
                                    

***Safnah Ashir***

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

***Safnah Ashir***

***Muslim Ashir***

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

***Muslim Ashir***

***Muneera Ashir***

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

***Muneera Ashir***

*ƘADDARARREN AL'AMARI*

© *Rahma Kabir*

Wattpad @Rahmakabir.

*SHINFIƊAR LABARIN*
Labarin ya yi nitso ne akan wasu marayu su uku. Rayuwar ta zo musu a cikin bahagon yanayin da basa iya gane dai dai da rashinsu, duk sanadin ƙunci maraici, ba su da mafaɗi balle su samu wani jagora da zai rika tsawatar musu.

Safnah ita ce babba ta zamewa ƙannenta uwa da uba bango abin jinginawarsu, su kaɗai suke rayuwarsu cikin rashin gata. Duk da Safnah tana da ƙarancin shekaru amma ta zage akan niman na kanta. Tana yin rayuwa a cikin gurɓatattun mutane, amma duk da haka bai sa hayayyarta ta sauya ba, a haka ta shiga uwa duniya dan samun hatimin nasara. Duk abin da mutane suke faɗa a kanta, bai taɓa tasiri a ranta ba domin zuciyarta ta riga ta bushe, za ta iya yin komai muddun zai sada ta da gumin halak ɗinta, duk saboda ƙannenta su ji daɗin rayuwarsu.

Haƙiƙa marayu suna da haƙƙoki a musulunci masu girman gaske,
domin idan maraya ya samu haƙƙinsa na tarbiyya mai kyau da ingantacciyar rayuwa, to hakan yana da tasiri mai girman gaske a cikin al-umma, idan kuwa aka wulaƙanta maraya ya tashi cikin rayuwa ta tsanani mara kyau, to lallai zai iya zama hadari a cikin al-umma. don haka Al-qur'ani mai girma ya bada cikakkiyar wasiyya da kulawa ga marayu, ta hanyar kula da tarbiyyarsa, mu'amalarsa, da kiyaye dukiyarsa, kar kuma a kuskura ayi masa wani abin da ba alkhairi ba.

Akwai ƙalubale da dama a cikin wannan tafiyar, ababen ban mamaki zasu faru. Safnah zata kasance mai jure ƙunci da wahala duk dan ƙannenta su yi alfahari da ita, ta yadda ba zasu yi kukan maraici ba.

Shin ya rayuwar waɗan nan marayun zai kasance?

Haƙƙar Safnah tana cimma ruwa kuwa?
*******

Akwai wani abu a tare da shi, da ya zame masa babban naƙasu a cikin rayuwarsa, kuma a duniyarsa yana da gata, uwa da uba duk suna raye. Akram ya taso cikin babban ahali, kuɗi da mulki, sai dai kash duk da wannan daula da yake ciki, akwai abin da ya rage masa jin daɗin duniya.

Shin wannan wace matsala ce ke tattare da rayuwar Akram?

Wannan shi ne *ƘADDARERREN AL'AMARI*, mai kuɗi ko talaka duk Allah kan iya jaratarsu, ta ko wani irun fuska duk dan ya gwada imaninmu. Kuma wani *ƘADDARERREN AL'AMARIN* a zane yake cikin kundin ko wani bawa, sai dai yana zuwa a fuska daban-daban, sai wanda Allah ya nufe shi da cin nasara shi ne zai iya jure duk kan ƙaddarar da ta tunkaro shi.

Kamar yadda ƙaddara take haɗa wasu iyalai biyu a wata uwa duniya, wanda hakan ya zame musu babban ƙalubale a cikin rayuwarsu, akwai babban tashin hankali, tsantsar tausayi, rikici, damuwa, wahala, ƙunci, rashin ƴanci, cin zarafi, rikitacciyar soyayya.

Samun warwaren zaren labarin, yana tafe cikin gundarin littafin ƘADDARERREN AL'AMARI. Kamar yadda muka sani dai tafiya mabuɗin ilimi ne. To ga shi dai na zo muku cikin wani sabon salon tafiyar, sai ku natsu ku bini a sannu a hankali, lallai akwai wani ɓoyayyan ilimi da zaku iya samu ku adana shi a cikin kundin zuƙata, ƙila zai iya muku amfani a rayuwa. Alƙalami na shi ne zai kasance jagorar tafiyar, sai ku kasance tare da ni, Insha Allah 2020.

_*YANA NAN TAFE*_

*Rahma ce*

ƘADDARARREN AL'AMARIWhere stories live. Discover now