01

797 49 4
                                    

*ƘADDARARREN AL'AMARI*

© *Rahma Kabir*
          Mrs MG

Wattpad @Rahmakabir.

2020

*_Bismillahir Rahmanir Rahim_*

_Duk kan Godiya ya tabbata ga Allah Ubangijin mu, shi kaɗai ne ba shi da Abokin tarayya. Tsira da Aminci su k'ara tabbata ga fiyayyen Halitta Monzon tsira s.a.w, tare da Ahalinsa da Sahabbansa._

_*Alhamdulillah da Allah ya k'ara bani dama na zo muku da sabon littafina mai suna ƘADDARARREN AL'AMARI.*_

*Gabatarwa*
_Wannan littafi k'agaggen Labari ne, domin mu ilmantu kuma mu d'auki darussan dake ciki. Idan labarin yazo d'aya da labarin ki/ka to ku yi min Afuwa. Labarin yana k'unshe da kalubale, tsantsar tausayi, rikici, damuwa, wahala, ƙunci, rashin ƴanci, cin zarafi, rikitacciyar soyayya.

*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, dan Allah a kiyaye_

*Sadaukarwa*
_Ga group d'ina Sirrin 'ya mace. WhatsApp._

*01*

Da misalin ƙarfe Huɗu da rabi na yammacin la'asar, rana ta yi sanyi iska na kaɗawa. Gidan Marigar Malam Ashiru ya kasance cikin unguwar talakawa, ɗan ƙarami ne yana ɗauke da ɗaki uku ciki ɗai-ɗai, guda biyu kwanan ya kwaye sakamakon iskar ruwan sama daya yaye su, ɗaya ne kawai mai kyau, sai toilet guda ɗaya yana haɗe dana wanka da bayan gida, babu kitchen sai duwatsu guda uku dake tsakar gidan da aka jera da alama nan ne madafa, sai rijiya daga gefe an sanya masa babbar taya da marfin fale-fale. Wasu yara ne su uku suke rayuwa a cikin wannan gida, zaune suke bisa wata yalolon tabarma a tsakar gidan, Babbar ita ce mai suna Safnah shekarunta sha takwas, sai mai bi mata Muslim ɗan shekara sha biyar, sai ƙaramarsu Muneera ƴar shekara sha biyu.

Mumira ce ta zabga hamma har sai da ta fidda kwalla saboda azabar yunwa daya addabi cikinta.

"Anty Safnah wai dan Allah yau mai zamu ci ne? wallahi ni fa yunwa nake ji, kuma ga shi ba mu da komai da zamu ci, ya kamata muje gidan Kawu Bala"

Muneera ta yi maganar tana shafa cikinta tare da runtse ido kwalla ya sauka kuncinta.

"Muneera ya kama ta ace zuwa yanzu kin saba da wannan yana yin da muke ciki, tunda ba yau muka soma wannan rayuwar ba. Kawu Bala yana iya ƙoƙarinsa a kanmu, shima ba ƙarfin ne da shi ba, dan haka bai kamata mu rika matsa masa ba. Kuna kallon yadda nake faɗi tashi wajen niman aiki, amma dana fara nake samun matsala"

Safnah ta bata amsa cike da damuwa a fuskarta.

"Anty Safnah ki rabu da Muneera ta sani take tambayarki ai, ni ina ganin bari naje na yi bara, ƙila mu samu abincin da zamu ci"

"Muslim karka fita, bari ni naje wurin mai saida abincin nan, inta aike ni ko na yi mata wanke-wanke kila ta bani abinci a madadin kuɗin da zata biyani, sai na kawo mana mu ci"

Safnah Tana kaiwa nan a maganar ta sai ta miƙe jiki a sanyaye, ta jawo wani koɗaɗɗen hijab a igiyar shanya ta sanya, sannan ta sanya silifas ɗinta wanda ya siɗe ya yi rami.

"Muslim in na fita ka rufe gidan, ka ja ruwa a rijiya ka cika farar roban cen ka kai mana ɗaki, zan dawo yanzun nan Insha Allah"

"Anty Safnah Allah ya tsare ya kiyaye hanya"

Muslim da Muneera suka haɗa baki wajen yin maganar lokaci guda.

******
Safnah, Muslim, Muneera Ƴaƴane ga Baffa Ashiru da Inno Aishatu, Asalinsu Fulanin Gombe ne, Malam Ashiru yana aikin gidan Gona a nan Kaduna, dalilin da yasa kenan ya dawo da Iyalinsa nan Kaduna tun Safnah tana ƙarama. Alhajin da Baffa Ashiru ya ke yiwa aiki, shi ne ya siya masa ƙaramin gida a nan Unguwar Badarawa.

ƘADDARARREN AL'AMARIWhere stories live. Discover now