10

344 38 1
                                    

*ƘADDARARREN AL'AMARI*

© *Rahma Kabir*
         Mrs MG

Wattpad @Rahmakabir.

10

Bayan sun zauna a bisa tabarka a nan tsakar gidan, Muslim ya kalli Safna cike da kulawa.

"Anty ina kika hadu da wa'innan Matan?"

"Sun zo wajen hajiyar da nakewa aiki ne shi suka rage min hanya."

"Amma anty gaskiya ba mutanan kirki bane ji kayan jikin wannan mara dan kwalin, ni basu kwanta min ba"

"Kai muslim meyasa daga ganin su zaka yanke musu hukunci? babu kyau mummunar zato, bana son haka kuma ai musulmai ne, daga yau bama ga su ba karka kara kulla haka a ranka babu kyau"

"Anty Kiyi hakuri insha Allahu bazan sake ba, yanzu ya zamuyi da kudin nan kinga ran nan kawu yayi fada sosai akan abinda muka yi da kudin da aka baki"

"Karka damu zan aje kudin duk ran da yazo zan nanu masa sai mu nima shawarar yadda za muyi dasu, nasan zai fahmce ni, sannan ma yanzu muna da sauran kayan abinci ai"

"Hakane Allah ya mana jagora"

Duk suka amsa da Ameen.

*****      *****

Washe gari

Haka safna ta shirya da wuri ta tafi aiki, tana isa ta samu suma basu dade da bude shago ba, ta gaishe da hajiyar ta amsa fuska sake cike da fara'a, tana kara jin kausar Safna a ranta, lallai ta kara tabbatar da cewa ita haske ce a rayuwarta.

"Safna ai yau daga ni har ke bamu ga ta zama ba, yanzun nan zamu tafi kasuwa dan yi miki siyayya, kisan Haj. Najwa bata son kazanta dole zaina siya miki kaya masu kyau da tsada, ita duk haka yakewa ma'aikatanta akwai kirki, in dai kika kwantar da kai zaki samu alkhairai sosai a gunta"

Murmushi kawai safna tayi dan ko a jiya ma ta tabbatar da kyautar Najwan data basu dubu goma, dan haka babu musu suka yankaya karuwar central.

Kamar yadda Najwa ta sanya NEPA su maida wutarsu Safna haka kuwa aka yi, dan karfe tara na safe da mintuna suka dira a kofar gidan, basu tsaya yin sallama ba suka soma kiciniyar hada guntuwar wayar da tayi saura wacce da jimawa duka yanketa suka jona da wata mai kyau suka dane falwaya suka mayar musu da wuta, nan take hasken kwan dakinsu dana tsakar gida ya kawo, Muneera ta tashi sai tsalle take tana fadan yeee an kawo wuta, shi kam Muslim da gudu yayi kofar gidan dan ya ga nepan, yana fita ya tsaya yana kallonsu suna kokarin sanya lada a bayan mota, bai yi wani mamaki ba dan dama jiyan anyi komai a gabansu, sai dai shi tun jiya ya kasa samun natsuwa da haka hankalinsa yaki kwanciya dasu Najwa, haka ya dawo gida jiki a sabule ya shiga jero Addu'an Allah yasa ba yan yankan kai bane suke son cutar da Antynsu.

Mutanan unguwa kuwa ba karamin mamaki suka sha ba ganin NEPA sunzo takanas dansu mayar da wutan su Safna, nan take suka fara gasgata rade radin zargin da akewa Safna akan ta fara bin maza, Wanda jiya ma akan idan wasu ta sauka a motarsu Najwa, nan fa hira ta barke a unguwa, Matan dake cikin gida suma labari ya ishe su, kowa dai yana fadar albarkacin bakinsa, wasu ma cewa suke maraici babu abinda baisawa, sannan su da aka bar musu tabiyyar kansu a hannunsu babu mai kwabawa ai dole hakan ya faru, sun gama kokarin safnar da tuntuni bata balle da iskancin ba sai yanzu. Maganganu dai marasa tushe, ranar watan maganar su Safna ya kama a unguwar, d'ai d'ai kun mutane ne masu fadan abin kirki akansu da yabon halinta.

****       ****

Haj. Hauwa tun jiya ta zo Kaduna ta sauka a shahara hotel dake cikin malali, dan ta yarda da tsaftarsu duk zuwa a nan take sauka. Cikin sauri ta kammala shirinta, sanye take cikin doguwar rigar leshi dinkin buba saita tane kanta da gyale ta sanya farin tabarau fuskar nan sai keshi take ta dauki hand back dinta ta fito rike da key din dakin, ta samu drivern daya tukota tunda Abuja tace yaje ya huta ta amsa key motar tayi gaba abinta, unguwar Abakwa ra nufa gidan Malam, bata dauki dogon lokaci ba ta isa tare da yin parking ta sauko, sai wani cuna hanci take saboda warin kwatan dake kofar gida daya noshi hancinta, haka dai ta daure ta shiga, Halima tana ganinta ta washe baki tana yi mata lale, fuska ba yabo ba fallasa ta amsa tare da tambayar ko malam na nan.

ƘADDARARREN AL'AMARIWhere stories live. Discover now