14

348 41 7
                                    

*ƘADDARARREN AL'AMARI*

© *Rahma Kabir*
         Mrs MG

Wattpad @Rahmakabir.

14

Abuja

Su Safna sun isa Abuja lafiya suka isa gidan Haj. Hauwa driver yayi parking a harabar gidan suka fito gaba daya, Haj. Hauwa tayi gaba Safna tana biye da ita a baya har suka shiga babban falo, hajiya ta kai ta wani daki mai dauke da gado mirror da Waldrop komai tsaf, sai ta kalli Safna da take ta kama jiki saboda ba kunta ta ce.

Mu shiga bayi na nuna miki yadda zaki yi amfani da shi sai kiyi wanka.

To tace tabi bayanta suka shiga, hajiya ta kwatanta mata yadda zata hada ruwan wanka kana ta fito, safna ta shiga kallon kyawun toilet din. Hajiya ta haura sama ta shiga dakin Seema ta samowa Safna wasu kaya riga da siket yan kanti ta sauko ta kai mata kayan ta ajiye kan gado, ta bude murya yadda Safna zata ji ta.

In kin fito ga kaya nan ki sanya ina zuwa

Sai fice ta nufi dakinta itama wankan tayi cikin sauri ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga ash color saita yane kanta da gyalen rigar, bata tsaya yi kwalliya ba turare kawai ta shafa saboda tana sauri. Ta zo ta samu Safna ta shirya itama siket din ya dameta dan pelcil ne kuma na roba ga shegen tsagu har kaurinta yana bitowa, a ido kamar ba zai shigeta ba amma da yake na roba ne ya zauna daram a jikinta, rigar kuma mai guntun hannu ne tayi sa'ar bai kamata sosai ba, hajiya Hauwa ta kare mata kallo ta saki murmushi domin tayi mata kyau, kayan kamar dan ita aka yi su don duk surar jikinta sun bayyana, danma babu wani kulawa sosai data samu ta san zuwa nan gaba kadan in ta wanke mata dattin talauci ta sha ac sosai komai nata zai dawo na ajebota. Ta zo ta kama hannunta ta isa da ita jikin mirror ta warware mata gashinta da yake tufke ta dauki kum ta taje shi sosai, ganin ma gashin tsaf yake ba datti sai ta daure mata da rebom ta kitse mata jelar gashin, Safna ta fito ras kamar wata yar tsana.

Ya kika ganki kinyi kyau ko? Duk da ba ki yi makeup ba

Murmushi kawai Safna ta saki bata ce komai ba, hajiyar ma bata kuma magana ba taja hannunta suka fice har zuwa jikin motarta ta bude gefen driver ta sanya Safna a ciki ita kuma ta zauna mazaunin driver ta sa key, Safna ta kalleta cike mamaki ganin zata fita da ita haka kai ba dan kwali.

Ummm hajiya bari na dauko dan kwalina

Hajiyar ta waigo ta kalleta cike da kulawa

Haka zamu tafi tunda cikin mota muke, sannan ba kida wasu dan kwali ko hula da zaki using dan ba zaki sake sanya wancen kodaddun kayan ba, yanzu kasuwa zamu zan miki siyayyar kaya. Bana son musu da kardama duk abinda nace shi za kiyi

Safna ta gyada mata kai alamar to saita kwantar da bayanta jikin seat tana nazarin irin sabon rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, addu'ar tsari kawai take jerowa a cikin ranta, har suka isa babban wani super market na boutique suka yi parking suka fito Safna sai kama jikinta take kamar tana jin sanyi gani take kamar ita kadai ake kallo, hajiya da ta ga haka sai ta kama mata hannu suka shiga ciki, Hajiya ta shiga kwasar mata kaya, English wears, dogayen riguna ready made, gyale, takalma, kayan kwalliya, turaruka, dan kunnaye passion da abin hannu, ta kashe mata kudi kimanin dubu dari da hamsin, Safna tsoro ya gama cikata sai hakan ya tuna mata da Haj. Uwale yadda ta dinga kashe mata kudi ashe da walakin goro a miya, ta shiga tunanin kar dai itama wannan hajiyar hanyar banza zata daura ta, ita da tazo aiki me yasa zata siya mata kaya irin wannan. Haka suka dawo gida da kaya niki niki, hajiyar tasa mai aikinta ta gyarawa Safna kayan ta jerasu a Waldrop ta kuma bata umarnin ta jera musu abinci a dinning, ta amsa da to ta fice.

******      ******
Washe gari

Safna ta kwana bisa lallausan gado, tayi barcin da bata taba yin irinsa ba, duk da tayi aiki a gidan masu kudi da dama amma bata taba samun wurin kwana mai kyau da aka karrama ta irin haka ba, har saida ta makara wajen tashi sallar asubahi sai misalin karfe bakwai na safe ta farka. Bayan ta idar da sallah sai ta shiga ta hadawa kanta ruwan wanka kamar yadda hajiya Hauwa ta karanta mata jiya, ta fito ta samu wata doguwar riga maroon ta sanya sai ta daura dan kwalin, ta shafa mai ta koma ta kwanta, sai ga mai aikin gidan ta shigo tare da gaya mata hajiya tana jiranta a dinning. Haka ta fito ta samu hajiyar ta tsuguna ta gaisheta ta amsa fuska sake kana tayi mata umarnin ta zauna su karya da sauri dan fita za suyi.

ƘADDARARREN AL'AMARIWhere stories live. Discover now