13

317 32 2
                                    

*ƘADDARARREN AL'AMARI*

© *Rahma Kabir*
         Mrs MG

Wattpad @Rahmakabir.

13

Washe gari

Tun misalin karfe shida na safe tun gari bai gama haske ba safna ta gama hada plan din guduwa, toilet ta shiga ta duba window bata san lokacin da murmushin nasara ya kubuce mata ba, windon bayin glass ne da aka jera sai net da aka manna ta baya, tun tsakiyan Daren jiya Safna ta gama cire glass din ta yage net din. Safna ta runtse ido ta karanto Addu'an samun nasara kana tayi bisimilla ta bude abin tuntun kashi ta dare samanta ta taka tuntun da ruwa ke taruwa da ake flushing sai ta kama karfen dake rike gilss din windon ta zura kafarta na dama shima na hagun ta zura shi sai ta rika jan jikinta har Allah ya bata dabar direwa, ta waiga tana kallon tsukukun windon da Allah ya bata sa'an fita, sai ta saki murmushi ta gyara mazaunin dankwalinta dan bata daukar musu hijab ba daga ita sai kayan jikinta, ta nufi gate cike da zullumi, ta samu mai gadi zaune yana sauraren labaren BBC na karfe shida a radio, cikin dakiya da karanto Addu'a a ranta ta tunkareshi, gate man din yayi mamakin ganinta dan bai san da ita a gidan ba tace.

Baba Anty ta aikeni na siyo mata bread

Ok yace bai musa mata ba ganin yanayin ta tayi kama da yar aiki, amma yayi mamakin siyan bread din domin yasan Haj. Najwa komai tana oder ne a kawo mata har gida. Ya bude mata gate ta fita ya maida ya rufe tana jin ya rufe ta ruga a guje tana waige waige sai da ta shanye layin kana ta kutsa kai wani layi sai ta sausauta gudunta tana haki, hawaye ne ya soma kwaranya a kuncinta tana waige waige, ga unguwar ba kowa ihunka banza barinka hofi, bata san ko a ina take ba dan ba sanin manyan unguwanni tayi ba, haka tayi ta tafiya kafa babu takalmi, tayi mamaki ma da mai gadin mai gane ba, koda yake rigar jikinta dugowa ce kuma ta sauka har kasa ta rufe mata kafa, sosai take tafiya tana shiga layi ka ga unguwannin duk titi ne tsoranta karta kara maida kanta layin data fito, sosai take kuka tare da adduan Allah ya kawo mai taikamonta a wannan lokacin.

Haj. Hauwa sai yau ta shirya komawa Abuja, kwana biyu da suka wuce tana ta zarya akan ko zata samu nasarar dauka ka kara akan batun Seema, amma abin yaci tura karshe haka ta hakura ta yanke shawarar komawa Abuja dan cigaba da harkokinta, amma fa Akran yana kahon zuciyarta ta kuma tanadar masa irin mugun hukuncin da zata yi masa. Sanye take da doguwar riga na atamfa sai ta yi dauri da dan kwalinta, ta sanya gyale babba ta yafa a kai sai farin gilashi sisiri data sanya, daka ganta kasan ruwa ya bigi dan zakara har wata yar natsuwa tayi, tayi ramar fargaba sai ta kara haske, sun fito daga hotel din da ta sauka wanda yake a nan malali tana zaune a baya driver yana janta so take su isa Abuja akan lokaci shiyasa suka yi fitan sassafe. Motansu ce tazo ta wuce Safna da gudu ta matsa gefe da sauri dan ta tsorata, kuka sosai take yi domin ta soma sarewa da dogon tafiyar da tayi sai a lokacin yunwa ya taso mata gadan dagan, jikinta ya zama babu karfi sai dai sauri da take yi dan ta samu ta shiga cikin jama'a, Haj. Hauwa ta hango safna ta madubi bayan sun gota ta tana nazarinta duk da bata ga fuskarta ba, har sun yi nisa sai tayi saurin cewa driver.

Kayi ribas mu koma gurin wancen yarinyar

To yace ya soma yin ribas har suka cimmata, Safna tana ganin haka ta tsandara ihu tana niman fecewa a guje, a tunanin ta ko su Najwa ne suka zo sake dauketa, ganin an zuge gilas din baya taga wata mata ta sayo kai waje yasa ta tsaya tana kuka sosai.

Ke meya sameki kike kuka? Kuma daga ina kike da sassafen nan?

Sace ni wasu yan mata suka yi suka kawo ni nan anguwar, kwana na biyu a gunsu shine Allah ya bani sa'a na samu na gudo, to bansan ko ina nake ba tun dazu nake tafi kuma na gaji sannan ina jin yunwa.

Ayya sannu ko Allah ya kyauta gaba, ina ne unguwarku?

Badarawa nake

Ok ai ba nisa sosai tunda nan malali ne, duk da muna sauri amma shigo mu rage miki hanya sai mu kai ki gida ko

ƘADDARARREN AL'AMARIWhere stories live. Discover now