Bayan magrib jidda ta shiga toilet tayi wanka. wadrobe d'inta ta bude ta ciro wata yar skinny jeans da top fitted wanda ke kama jiki ta saka duk sun matse ta sosai sannan tayi rolling da yar karamar gyele tasaka abaya ah kaiTachi makeup sosai tayi kyau ta fesa perfume wanda idan mutum yazo wucewa kusada ita sai ya ji
kamshinta handbag d'inta mai tsada da phones d'inta ta d'auka mum ta tadda ah parlour
"Jidda ina zaki haka da kika chi uban makeup" cikin shagwaba ta amsa
"mum zani gdan wata friend d'ita zamu fita da ita"
"hmm toh adawo lfya munyi waya da dad d'inki wai gobe zai dawo kuma sahla zuwa nextweek zasuyi hutu ta dawo" cewar mum
"Okay mum bari in wuce"
yau ba da driver zata ba ita kad'ai zata sai ta kar'bi makullin motan ah hannunsa.
Da B.M.W zata fita dashi gateman ne ya bude mata gate ta fita wani speed ta saka kamar meh tsere.
layinsu frnd d'inta tajeh dake Nyanya a garin Abuja bata maa shiga gidan ba ah bakin gate
d'in gidan tayi parking ta 'kirata a waya bata fi minti 5min ba ta fito sanya da wata bakar gown.
Ta shiga mota jidda ce tayi tsaki "Haba Maryam kina abu kamar baki waye ba" Maryam ta kalleta cikin rashin fahimta.
"Kamar ya?"
mtsww ranta ya baci kawai taja motanta sukayi gaba sai uban sharara gudu takeyi a titi kamar ita kad'ai ce a titin.
Gudu takeyi Maryam na ce mata "Jidda yi a hankali ga fa motoci"
amma ina kara speed ma takeyi
wani kara taji da alamu karo sukayi nan ta tsaida motan cikin hot temper ta fito dan duba dawa
sukayi karo wani matashi ta gani da mashin dinsa ta fara masifa kai malam baka gani ne ko bakada kwakwalwa ne da zaka zo ka shigemun gaba inaga iyayenka basu koya ma tarbiyya ba. cikin haushi matashin nan ya daga hannu ya mareta, idonshi sun kada sunyi jaa. Hannu ta sa a kumatunta.
"Ni ka mara"
"An mareki, me zaki yi"
"Kin zageni na kyaleki amma kada ki kuskura ki zagi iyayena. inaga kece iyayenki basu koyamaki tarbiyya ba saboda daa kinsan da darajarsu daa bazaki zagi na wani ba har zai tafi ya tsaya
kuma magana ta karshe I Think hankali bai isheki ba better go and learn how to respect others"
yana kaiwa nan ya ja tsohuwar jincheng dinsa ya wuce.
jidda kuma kankarewa tayi ta kasa magana ba abinda take nanatawa sai inda yace better go and learn how to respect others lebenta ta ciza "i will surely teach this rascal a lesson, he will regret slapping me" ta shige mota kallon Maryam tayi wanda komai ya faru kan idonta
"kina jin abunda this low class yace mun how dare him slap me yaa san ni wacece kuwa" ita dai Maryam hakuri ta ba Jidda dan gaskiya fault d'inta ne dan ta fad'a mata ta rage speed ta 'ki.
Jidda tayi tsaki "Yayi spoiling mood dina, i can't go to the party mu koma gida kawai" Maryam shiru tayi batace mata komi ba har suka kai gidansu, don tasan idan tayi wata magana zasu samu matsala da ita ta sauke ta tayi sannan ta wuce gida rai a bace.
Wacece Jidda?
Jidda 'yar 25 years tanada tsayi siririya fara. Itace first born a wurin iyayenta Alhaji Abdullahi da hajiya muhibbat babanta mai kudi ne
yana da kamfanoni da gidaje yana yin contract da yawa yana da bank.
mum dinta ma ba laifi tana kudi. lokacin da sukayi aure da alhaji abdullahi 7 years sukayi kafin Allah ya albarkacesu da jidda wanda ko me takeso suna bata
Ko laifi tayi basu mata fad'a ah haka har ta girma sai abunda takeso ake mata. Bayan jidda ta kamalla shiga secondary Allah ya kara ba hajiya muhibbat ciki aka haifi Sahla. Jidd tayi nursery da secondary d'inta a Abuja da ta kammala ne daddyn ta ya tura ta Canada anan ta karasa karatunta banking.
jidda tanada hot temper abu kad'an zaka mata taji haushi gashi ta sha wulakanta mutane
yawancin ma'aikatan gidansu ita kesa a jore su da tama wasu rashin kunya suka dan bugeta sai
tasa mum d'inta tayi firing d'insu sistanta sahla dai ba tada matsala bata fiye magana ba she's 14 years tana ss1 yanzu a boarding ita kwata kwata
komi aka girka kuma aka bada bata cika complaining ba amma jidda idan anyi girki ma sai tace
yayi kaza gashi ba ta ji sai zuwa chasu yau ah wannan club din gobe a wanchan idan Maryam tana fad'a mata se tace ta barta taci duniyarta da tsinke.
**
horn ta dinga yi da sauri meh gadi ya bud'e gate yace hajiya "lfya kike ta horn haka"
hararansa tayi "ina ruwanka kayi aikinka ba wai ka tsaya kana shiga matters din wassu ba mara hankali kawai"
baki bude mai gadi yace Allah ya huci zuciyarki wataran zaki had'u da dai dai ke wannan maganar bayan ta tafi ne. ya fad'a ne bayan ta wuce bata mayi parking a parking lot ba
fitowa tayi ta fara kwad'a ma driver 'kira sai da ta kira kusan sau uku ya fito cikin fushi.
"Kai bakada hankali ne bakaga ina kiranka bane"
"Ayi hakuri banji bane da wuri"
"Ai daman bazaka jiba ka tsaya kana shashanci" watsa mashi key tayi "ka kai gyara yadanyi scratch" ta wuce ciki.
Bata ma lurada mum dake parlour saboda bacin rai ta haura sama ta rufe kofar mum ganin jidda ta wuce batayi
magana ba yasa hankalinta ya tashi itama haurawa sama tayi tana murde kofan jidda taji a kulle
knocking ta farayi taji shiru hankalinta ya tashi tayi tunanin ko Asma jidda ne ya tashi.
Knocking ta sakeyi daga baya jidda ta bude mum cikin rud'ewa tace "me ya faru jidda badai abinda ya same kiko"
ta rungumeta jidda tace "Mum ba abinda ya sameni na shiga wanka ne don't worry" Ajiyar zuciya Mum ta saki
"Yi maza ki sauko kichi abinci toh mum ina fatan favorite dina aka girka"
nodding kai tayi alaman eh jidda ta koma ciki don shiryawa incident din d'azu ya fadu mata a rai a fili ta fada tace i will surely teach this low class a lesson baisan JIDDA ba murmushin yake tayi.
YOU ARE READING
Jidda Da Jallal
RomanceJidda 'yar shekara 25, wacce ta fito daga gidan masu kudi. Abinda takeso shi takeyi ba'a mata abu ta kyale. Me zai faru da babanta ya sata a matsayin manager a company shi kuma tayi crossing part da Jallal, Daya daga cikin ma'aikatan company wanda b...