jidda ce zaune office dinta tana duba wasu files wayanta ne ya dau ringing tana dubawa tagafriend dinta maryam picking call din tayi da sallama jidda ya kike kalau fa maryam inama office
ne maryam tace ok akwai inda zani zan biyo ta office dinki ok tohm Allah kawoki
knocking akayi tace come in wani dan ma aikaci ne ya kawo mata file tayi signing tace ka dawo
anjima as you can see am busy girgiza kansa yayi kawai zai juya ta kirasa tace ka kiramun mr
jallal yace ok ya fitada ya koma desk dinsa yaga jallal yana aikinsa saboda akwai mutane da sukeson su saka kudi a bank din daman aikinsa kenan wadanda zasu saka kudi a bank wanda aka aika yace jallal
madamme na kiranka kuma kaje da wuri da daganinta yau fuskarta ba walwala tsaki jallal yayi ya fada can kasa kasa
to ina ruwana sai na gama aikin da nakeyi zanje haka ko akayi saida jallal ya kamala aikindayakeyi ya tabata ya gama attending to customer din sannan ya tashi
knocking yayi tace come in ba tareda ta daga kai daga abinda takeyi ba shiga yayi ya tsaya dayaga
tayi shiru yace "uhm.. Ance kina nema na daga kanta tayi ta kalleshi sai taji gabanta ya fadi ganin yadda ya hade rai sai ta dauke kanta daman so nake ka mika ma usman wannan file din danayi signing bai ce mata komi
ba ya karba ya juya ya fice hannu tasa ta bigi kanta ganin yadda ta kasa aiwatar da abinda tayi niyyar yi masa. karan wayanta ne ya dawo da ita daga thought dinta maryam ce ta kira"hello maryam kin iso ne" "eh inane office dinki" ta fada mata room din bai fi 5mins ba maryam ta shigo
jidda ta kawo mata drink dake fridge daman tanada fridge a office saboda baki "kawa ya kike
kwana diyawa tun ranar da kikayi fada da guy din nan rabo na da ganinki." tsaki jidda tayi kedai maryam daga zuwanki kin fara min maganan wani dan Allah karki bata min rai maryam ta tabe baki tace Allah baki hakuri ni banga wani laifi da guy din yayi ba da zaki dinga jin haushin sawani kallo jidda ta watsa mata tayi shiru.
Ai tunda ko ya wulakanta ta itama tayi alkawarin saita nuna masa.
Suna cikin hirarsu ne sukaji knocking tace come in dataga jallal sai taja wani tsaki wani haushin sa taji ya dasu a ranta.
maryam sannu cikin far'an sa sannan ya hade rai ya juyo kan jidda yace daman akwai takardun dana kawo maki jiya kuma bakiyi signing ba tabe baki tayi tace kaje ka dawo anjima yanzu inada bakowa jallal ranshi ya fara bacci yace inason amfani dashi ne don in tafi da wuri maryam dake
zaune ido ta zuba musu kawai tana kallon ikon Allah.
Ina fatan baka manta wacece boss a nan ba a iya sanina sai 5 yayi ake tashi kuma yanzu its just 4 ta fadi tana duba agogon hannu ta. So bana ganin you have the right to leave the office by this time, inba so kake in baka query ba.
Wani abu yaji ya daki zuciyarsa yaso maida mata magana amma ganin maryam a nan sai yayi shiru harararta yayi ya fita saida ya rufe kofar da karfi.
maryam da har yanzu mamaki takeyi tace jidda wannan ba guy dinnan bane na ranar jidda tace
kwarai kuwa coincedence ne don nima nayi mamakin ganinsa a nan abinda yasa banyi firing dinsa ba saboda na rama abinda yamin kinsan i have the right ko
maryam ta tabe baki tace jidda ke dai baki manta magana abinda ya rigada ya wuce bazaki hakura. Ai naga yadda kikamai yanxu ga guy din ba ruwansa.
jidda tai tsaki tace ke kika san wannan nidai sainayi fulfilling promise din Dana dauka. sun sha hirarsu kafin maryam
tama Jidda sallama rakata tajeyi fitowansu daga office din ne jidda ta fara waige waige ko
me take dubawa oho maryam tace me ya faru kike waige waige sai ta basar aa ba komi suka fita
anan ne suga tararda jallal yana kokarin tada mashin dinsa maryam ce tayi magana tace jallal sai ina haka?
yayi dan murmushi yace "wallahi yanxu aka kirani wai kakata ba lafiya shine Zan tafi kaita asibiti. Wannan maganar fadi yayi bawai gaskia bace kawai so yake ya tafi gda. Istigifari yayita nanatawa a ransa akan Allah ya yafe masa.
maryam ta tambayesa ko zai bi ta layinsu tako ci saa zaibi tanan tace yadan rage mata hanya dan
batazo da mota ba yace ba komi duk maganar nan a kunne jidda tana jinsu tai shiru ba abinda take
jin a lokacin sai haushin jallal wata hadda dariya amma idan yazo office dinta yayita hade rai.
"Toh Kai haka kake aiki zaka fita baka tambayi permission ba. Inaso ka sani Mr jallal daga maka kafa nakeyi amma naga kamar kanaso kasa job dinka at stake if you don't feel like working here you're free to resign tana gama fadin haka tama maryam salama ta fice.
Daga maryam har jallal babu wanda ya furta komi. Ita maryam matsalarta daya da jidda bata manta abu idan ka mata abu tofa zaitayi yadda zatayi ta rama.
~*~*~*~*~*~*~
bayan jallal ya sauke maryam ya tafi gida dakin kakarsa ya fara shiga suka dan taba
hira anan ma yaci abincinsa kaka ina noor kakar tace ka manta ne ta tafi school yace au na manta
fa kakar tace naga alamar ka gaji kaje kadan kwanta ka huta murmushi yayi yace kaka kina ji dani fa tace ba dole ba ku kadai kuka ragen munbayan ya tashi yaje massalaci yayi sallah ya dawo dakinsa ya nufa 1 single room da dan katifarsa
ya kwanta idonsa ya rufe karan wayansa yaji yana ringing yayi tsaki yace wake kirana yanzu
kuma mutum bazai huta ba yana dubawa yaga arrogant boss daman da sunan daya saving kenanranar data kirasa saida wayar ya kusa katsewa sannan ya amsa da assalamu alaikum ta bangaren ta
ta amsa da wa alaika salam bata sake magana ba yace mallama lafia kin kirani a waya kuma
kinyi shiru tace daman ba wani abu bane wannan file din na dazu ina yake don na duba ban gani
ba yama kwatance cewan ta duba drawer na biyu sannan ta gani bata jira wani magana ba ta katse
tsaki tayi tace ya dauka zan kirasa haka nan ne mtsww ta koma office dinta ta cigaba da abinda takeyi
ta bangaren jallal kuma jefa wayan yayi gefe daya ya kwanta
*****
Har fa mun gama breakfast ki tashi da ta tashi ta shiga tayi wanka ta shirya cikin atampar riga da skirt tayi makeup tayi matukar kyausosai ta sauko ta gaida mum da dad dinta yace jidda ya aiki i hope everything is going smoothly
tace komai alhamdulilah dad a ranta tace saidai wannan jallal din dake bata mun abu dinning ta nufa Already anyi mata frying irish kuma komai a ajiye yake hadawa tayi ta fara ci a hankali takeci kamar wanda aka sa dole da ta gama ci ne ta tashi ta tafi dakinta laptop dinta ta kunna tana wasu aiki a ciki. Ta bangaren jallal kuma sun gama cin breakfast ne dashi da noor da kakarsa suna jindadi zamansu
abokinsa yusuf ya kirasa a waya yace kaka ina zuwa ya fita yaje ya sami abokinsa yusuf yake ce
masa ya ara masa kudi jallal kuma baida matsala indai zai taimaki abokinsa duk bawai yanada shi
ba yace tohm jira ni bari na kawo maka ya shiga dakinsa ya dauko kudi har zai wuce sai yaji kamar muryan mutum a dakin kakarsa budan curtain din da yayi mutuwar tsaye yayi idonsa suka kada sukayi jaa
**
toh readers anan zan dakata sai kunjini to fa waye wannan da jallal ya gani haka sai ku biyoniDon't forget to Vote|Comment
YOU ARE READING
Jidda Da Jallal
RomansaJidda 'yar shekara 25, wacce ta fito daga gidan masu kudi. Abinda takeso shi takeyi ba'a mata abu ta kyale. Me zai faru da babanta ya sata a matsayin manager a company shi kuma tayi crossing part da Jallal, Daya daga cikin ma'aikatan company wanda b...