Chapter 13

149 32 0
                                    

Bayan Jidda ta raka Maryam ta dawo ta zauna parlour tana kallon zee world sahla ce ta fito da luggage dinta daman yau zata koma skul Jidda ta kalleta  "har kin shirts?"

"eh fa sis amma kinsan zanyi missing dinki sosai ko" Jidda tayi murmurshi

"Nima zanyi missing dinki" mom ta fito tace

"Jidda bazaki rakata Airport din bane" kamar tace aa amma sai tace "tohm mom"

Sallama sahla tayi da mom Sannan Suka fita ta saka trolley ta a booth Sannan Suka shiga motan

Jidda a baya sahla a gaba don ita Jidda bata fiya son zaman gaban mota ba

Suna tafian su suna dan hira sama sama Jidda gaba daya tunani ya tafi da hankalinta batasan Sanda Suka iso airport din ba kamar karsu rabu. don sahla ce ke debe mata kewa amma yanzu ta tafi she will be lonely haka sukayi sallama Jiddah hadda dan hawayenta

A hanyar dawowansu ne Jidda tace driver ya biya da ita mall zata shiya wasu abubuwa sunkai
mall din ne yayi parking ta fito ta shiga mall din tayi shiyayan abinda take Bukata su turare da
cosmetics dai tana fitowa ne wayarta yadau ringing ta ciro wayar tana duba Wanda ke kiranta taci karo da mutum harta fara masifa juyo wan da zatayi wa zata gani jallal tayi mamaki amma saita boye

Ta Nuna shi da yatsa Kai Shima ita yake kallo tace "me kakeyi anan ba office ba"  baisan lokacin da bakinsa ya furta nazo shiyan wani Abu ne sun tsaya suna staring juna na wasu minutes maganar driver ne ya dawo dasu from staring at each other yace "hajia kin gama ne" Jidda tayi gyaran murya

"eh ganinan zuwa" Kara kallon jallal tayi wanda har yanzu ita yake kallo bata ce Komi ba ta
juya ta wuce tana shiga mota tayi ajiyar zuciya ta taba kirjinta dake bugawa tace "meyasa duk sanda na gansa gabana na faduwa" bata sake kallon waje ba har driver ya tada mota

Jallal kam sai da motan su Jidda ya wuce kafin ya dauke idon sa Shima yana fadin meyasa Dana
ganta sai nakejin dadi haka. Bai taba faruwa dani ba toh meyasa hakan (duk wannan maganar naka Kai zaka bamu amsa mr jallal) girgiza Kansa yayi ya shiga mall din

Jidda kuwa tunda taje gida ba abinda takeyi sai tunanin jallal tana tunanin abinda ya faru a mall

duk inda ta juya furkarsa take gani ta rasa dalilin da yasa taketa tunaninsa sai ta fada a ranta ko dai I'm in love with him kamar yadda Maryam tace amma if haka ne does he feels the same too

Wayarta ta dauko tayi dailing numban Maryam ringing biyu Ta amsa "Hello kawas gobe zanzo
gidanku akwai maganar da nakeson tattaunawa dake"

Maryam tace "hope dai ba abinda ya faru"

dan yadda Taji muryan Jidda ba wasa cikinta Jidda tayi murmurshi "ba Komi in nazo zaki sani"

"tohm shikenan sai kinzo ta katse wayar"

Washegari misalin karfe 4:00 na rana Jidda ta shirya domin zuwa gidan kawarta Maryam bayan ta
ci abinci tama mom Sallama Sannan ta fita parking lot taje ta zabi motar da zata fita dashi 4matic black Mai gadi ya hango ta tun kafin tayi horn ya bude gate ta fita

Tana tukinta cikin natsuwa har ta isa unguwarsu Maryam horn tayi aka bude mata gate ta shiga tai parking sallama tayi bai wani jima ba Maryam ta bude mata "kawas harkin iso Suka shiga ciki

A parlour ma Suka zaune kasance war umman Maryam bata nan maryam tace "me zan kawo maki ne"

Jidda tayi murmurshi "Aa maryam ba sai kin kawo wani abinci ba ruwa Mai sanyi ya isa" 

Maryam ta hade rai "kawas kullum idan nace zan kawo maki Abu sai kice aa ko drink ne ki Bari na kawo maki"

Tashi tayi ta shiga kitchen ta kawo mata drink me sanyi ta zuba mata a glass cup Sannan ta gyara zama  "yawwa kince kinada maganar da kikeson fada mun"

Saida Jidda tadanyi sipping drink din Sannan tace "Maryam Ina ganin maganar da kika fada gaskia ne" cikin rashin fahimta Maryam tace "wani magana kuma" Jidda ta cigaba

"jiya na hadu da jallal danaje shopping Dana Gansa sai naji kirjina na bugawa kuma Koda naje gida na kasa cire
tunaninsa a Raina kwata kwata ban San meyasa ba"

Maryam ce tayi ajiyar zuciya ta fada straight forward "Jidda kinason jallal amma bakison kiyi
admitting na gane hakan tun sanda naje office dinki yadda kikeyi nasan da wani Abu"

Hannun Maryam ta riko tace "amma ke kina ganin he feels the same toward me" maryam tayi ajiyar zuciya tace "wannan kuma ban sani ba but zai iya yiwuwa he feels something for you don na lura yadda yake kallonki" Kara rike hannun Maryam tayi tace "idan baya sona fa ya zanyi?"

Maryam tace "karki damu insha Allah zaa dace" sun sha hira sai kusan magrib Jidda ta koma gida

Ta bangaren jallal kuma tun ranar dayaga Jidda a mall yake tunanin ta office ma inyaje baya

jindadi yayi missing masifan ta he missed her face, her voice a lokacin ne ya tabbatar da cewan
he feels something for her  amma tunaninsa daya taya zaiyi ya furta mata and what if she doesn't feels the same way. Rufe idonsa yayi kamar Mai bacci alhalin ba bacci yakeyi ba

Tashi yayi ya shiga bayi ya watsa ruwa ya saka shirt da wando ya shiga dakin kakarsa a zaune ya tadda ta itada Noor

"Yaushe ka dawo ne"

"dazu nadan watsa ruwa ne
shiyasa baki ji daga gareni ba"

"Allah maka albarka jallal" sun yi hira har magrib yayi jallal yaje
masallaci yayi sallah ya dawo bai biya shagon abokinsa ba kasancewar yayi tafiya dakin kakarsa ya dawo Suka cigaba da hirarsu cikin natsuwa saida kaka ta fara gyangyadi

"Bari na barki kiyi bacci" harya tashi zai tafi kakarsa ta dakatar dashi "na manta in fada maka dazu mahaifinku ya Kira
wai yanata kiran wayarka Baka dauka ba" sai yayi karya yace "inaga na saka ta a silent ne" Alhalin yana sane da Moran

"saida safe kaka"

Dakinsa ya Nufa ya zaune kan dan madaidaicin katifarsa wayarsa ya ciro yaga almost 6missed call da babansu yayi hannu yasa a goshi contact Dinsa ya shiga dubo numban Yusuf yana cikin rolling ya tunkari numban Jidda da yayi saving as arrogant boss wani murmurshi ya saki yana tuno yadda

take hade rai sai yaji wani iska na shiga ko wani ilahirin jikinshi ( Niko nace toh fa jallal anyi nisa )








**

Toh masu karatu kun dai Ji jidda ta fada kogin soyayya. Shima dai jallal na fama da nashi. Me kuke ganin zai faru a shafi na gaba?

Don't forget to Vote| Comment sai kun jini😉

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now