Chapter 5

270 23 0
                                    

da sassafe jalal ya tashi ya shirya kasancewan yau zai fara aiki ya shirya cikin kaftan dinsan ya sa
hula yayi kyau sosai zuwa dakin kakarsa yayi ya ganta a kwance hankalinsa a tashe ya matso
kusada ita cikin kulawa yace

"kaka baki jin dadi ne?  da kyar take iya magana tace "ulcer na ne ya tashi amma idan na sha magani shikenan bude drawer na zakaga magani ka miko min"

da sauri jalal ya tashi ya bude drawer amma me maganin ta kare ya ce "kaka ai maganin ta kare"

"laa na manta cewan jiya na shanye sauran" jallal ne ya mike yace bari "inje in siyo maki yanzu in dawo"

kaka tace "aa jallal da ka barshi zan aiki noor ta siyo mun karkayi latti aiki" yace "aa kaka tunda akwai mashin ba wani dadewa zanyi ba"

"tohm shikenan Allah maka albarka" yace "Ameen"

mashin dinsa ya dauka ya tafi shiyo ma kakarsa magani ko dayaje ma shagunan duk basu budeba

saida yayi tafiya mai nisa kamin ya sami wani shago ya shiya maganin a hanyarsa na dawowa yahadu da trafic jam sbd wata babar truck data fadi saida yayi spending kusan 1hr kafin ya iso da sauri ya kawo ma kakarsa da ruwa tasha sannan ta kwanta noor ya kira yace "ki kula da kaka kada kije ko ina kinaj"
ta gyada masa kai

agogonsa ya duba yaga 9;30 kansa ya taba oh am late da sauri yama kakarsa sallama ya tafi bai kai ba sai goma da kwata daya shiga bank din kowa sai kallonsa yakeyi wani mutumi ne ya matso
yana fada masa "kaine jallal?" ya gyada masa kai alaman eh mutumin yace "lallai tun dazu aka kira sunanka zaa baka post dinka amma bakanan hmm kaje yanzu kafin ran madam ya sake baci"

office dinta yayi knocking shiru ba amsa budewa yayi nan ma bata nan wasu ma aikantan dake
wurin ya tambaya sukace tana meeting room anan sauran new maaikatan suke nan ya juya ya nufi meeting room din knocking yayi tareda bude kofar cikin tsawa jidda tace "excuse mr man can you excuse us as you can see we're having a meeting here"

tana masa alama da hannu cewa ya fita a hankali ya fita cike da bacin rai wani corridor ya samu ya zauna yana tunani wayarsa ya dauka yayi dailing no noor ringing biu ta dauka cikin ladabi ta gaida yayanta yace "ya jikin kaka" tace

"taji sauki dan gata tana linke kaya" jallal yace "meyasa kika barta tana linke kaya"

"nayi nayi ta barshi tace ita dai zata linke shine na barta"

"Tohm shikenan saina dawo"

"Toh yaya"

wani dan matashi ne ya nufo wajensa yace kaine jallal ya gyada kai alamar eh matashin yace

"madam ne ke kiranka" matashin ya juya ya tafi abinsa mikewa jallal yayi ta tafi office
dinta knocking yayi tace come in a hankali ya shiga tace

"have a seat" zama yayi fuska a hade gyaran murya tayi tace

"mallam jallal i'm very sure cewa kasan rules&regulations din bank dinnan bana tolerating late coming musamman ga maza so i will lyk it idan bazaka sake repeating abinda kayi ba"

kallan takaici jallal ya mata yace "amma ya kamata ace kinsan cewa mutum bazaiyi latti ba
idan bada uzuri ba ya kamata ki tambayi reason din mutum kafin kiyi wata magana ko ki dau wata
mataki ina fatan kin gane"

Hannu Ta daga masa alamar ya isa murmushin yake tayi tace "

"ina ganin bakasan dawa kake
magana ba ya kamata in sanar maka cewa nan bank din na babana ne and i'm the manager here so if you mess up zaka iya rasa aikin ka saboda haka ka kiyaye"

Ranshi ne ya sake baci yace "Toh sai me idan kece manager i don't
care da kike braging about bank din babanki ne ni nama dauka ke kika ginashi da kanki and ni
bana jin tsoron komi if you like kiyi firing dina akwai wuraren aiki diyawa a garin nan"

nan ya tashi yace "Excuse me" yana fita yayi banging kofar

jidda kasa magana tayi sai mamaki irin yadda jallal ya tsaya so confident yana fada mata
wadannan maganganu lallai zata gyara masa zama komawa tayi kan aikin da takeyi shiko jallal yaje post dinda aka sashi part din masu kulada da harkan wata information da problems din bank din wurin na kusada office din jidda zama yayi a wurinsa da system akan table din computer ya fara tabawa yana shigarda necessary details din har sallar azahar tayi ya tashi yaje
massalacin dake kusa yayi sallah ya dawo ya cigaba da aikinsa jidda ce ta fito rike da jakarta harta wuce ta kuma dawowa baya tace

"um mr jallal" kansa ya dago ya kalleta tace

"please dauko mun phone dina a office  na manta dashi"

abin yaba jallal haushi amma kasancewar akwai ma aikata a wurin
ya tashi inba dan haka ba bata isa tasa ya dauko ba shiga office din yayi ya duba kan desk dinta
babu saida ya duba drawer sannan ya gani koda ya fito bata wurin wani daga cikin su ne yace

"Tace ka sameta a waje"

ransa a bace yace me wannan yarinyar ta maidani fita yayi ya ganta cikin mota wining class din
tayi ta miko masa hannu shiko ganin zata raina masa wayo yasa ya tsaya ganin ikon Allah jidda
ganin ba alaman waya yasa tace

"mr jallal ina wayan?" iska ya fuzar yace.

"aw na dauka bazakiyi magana bane ki tsaya yanga"

kalamansa sun bata haushi amma tayi pretending tayi dan murmushi tace mr jallal as you can see muna wurin aiki ne kuma I'm your boss so talk with due manners ta mika masa hannu baice da ita komi ba ya mika mata wayar ta daga glass dinta taja motarta ta wuce jallal ransa ya mugun baci ya
fada in low tune you'll see ya fice komawa yayi wurinsa yacigba da abinda yakeyi wani dake
kusada shi ne yace jallal kayi hankali da madam dan naji she's hot tempered zata iya firing
mutum without hesitation jallal ne yai tsaki toh ni me ya dameni if she's hot temper toh ni na fita
dan bana karban raini ya juya ya tattara files ya sa a drawer yayi locking yace toh nina tafi sai
Allah ya kaimu gobe guy dindai baki bude yace kai zaaga show. Ya tafi tun time baiyi ba.

Jidda data isa gda tayi horn shiru tsaki taja tace wannan gateman din baisan aikinsa ba fitowa tayi
daga motar ta shigo cikin direct dakin gateman ta shiga ganinsa tayi a kwance yana sharara bacci
bugasa tayi ta kafarta saida ya firgita yace sannu hajia yaushe kika shigo tsaki tayi bansani ba abinda nakeso dakai shine before gobe ka tattara inaka ka bar gdan nan dan na lura baka san aikinka ba inata horn tun tuni amma kananan kana bacci

"hajia ayi hakuri bansan sanda bacci ya daukeni ba"

"Rufe mun baki banasan jin komi ka tattara kayanka ka bar gdan nan haka ya dinga bata hakuri sbd baisan ya rabu da aikinsa dashi yake samun ciyar da iyalensa da kyar ta hakura nan ma last warning ta basa cewa kar ya sake ta wurga masa key tace gashi ka ba driver na ya shigo da motan

ta wuce gateman din yace lallai zanso inga mijin da zaki aura da hot temper nan naki shigan parlour taga mom da sahla suna kallo sannunku da gda tace sannan tace akawo mata
abincinta dakinta ta haura dakinta gado ta fada tace wash am tired voice din sahla taji tace sis dole ki gaji mana tunda baki saba aiki mai yawa haka ba jidda tace kedai bari sahla ina abincin nawa dan inajin yunwa sosai bata gama rufe baki ba sukaji sallama mai aiki ta ajiye kan bedside ta fita abinta ta sauri jidda ta bude coler jollof din talia ne tunda ta saka fork ta fara ci bata tsaya ba saida ta tadar duka ta kora da drink sahla tace lallai sis kinajin yunwa kam me yasa baki tafia da abinci ko ki siya a can hmm kawai tace wani abu ta tuno tayi tsaki sahla tace me ya faru kuma dan

smilling tayi tace ba komi bari in dan kwanta in huta kinji tohm tace ta fita

**

jallal kam daya je gda dakin kakarsa ya shiga direct ya ganta zaune garau kamar ba wanda yayi ciwo dazu ba yace kaka kin warke ko tace eh mana na warke banajin komi tace ya aikin yace

"alhamdulilah" kaka tace ba wata matsala ko eh ba matsala ina noor

"Tana makaranta  abincinka na
dakinka kai kaka baki taba mantawa da abincina yana murmushi yace bari inje harya kai bakin kofa kaka tace yawwa jallal na manta in fada maka dazu jafar ya kirani nan take idon jallal suka chanza kala baice komi ba ya fita dakin..

**
Kuyi hakuri abubuwa sunmin yawane kwana biyu shiyasa banyi updating ba.

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now