Chapter 12

153 33 0
                                    


Saida tadanyi shiru na dan lokaci saboda she's quite shocked da abinda dad ya fada kallon sa tayi
tace

"Dad tunda na Warke kuma inashan magani ai ba damuwa zan... " Dad ya dakatar da ita

"Aa Jidda nasan baki ji dadin hakan ba amma ki sani lafiyarki mukeso ke kanki kin sani ga Asma ki kuma Nariga na Yanke shawara and my decision is final" kafin ta bude bakin yin wani magana Dad ya mike ya Nufa hanyar dakinsa

Tashi tayi ta koma dakinta ta kwanta kan gado tunani fal a ranta yanzu shikenan ta daina aiki yanzu bazata sake ganin jallal ba tsaki tayi a wannan situation din aiki na ya kamata nayi tunani instead Ina tunanin wani what's wrong with me tsaki tayi taja bargo sai bacci

Jallal ne ke shirin tafiya office baisan meyasa ba ya tsince Kansa da murmurshi da baisan dalili ba. fitarsa dakinsa ya tadda kakarsa tana hada wuta ya gaidata ta amsa masa cikin far'a ta lura da yanayin sa tace "Ah ah jallal yana ganka sai wani murmurshi kakeyi ko an biya albashi me" yadan sosa keya

"Aa ai wata bai kareba" ya rasa amsar da zai bata yasa ya Chanza topic "kaka Bari na wuce kar nayi latti"

"bazaka tsaya ka Haryana" ya sake duba agogon hannunsa "Aa kaka zanyi latti ki dafa mun favourite dina"

"Toh Allah Bada sa'a"

Jallal gidan abokinsa Yusuf yaje kasancewan acan yake parking mashin Dinsa tunda gidansu ba wani fili bane balle yayi parking ya tada mashin dinsa ya tafi

Bayan ya isa office din ya nufi mazauninsa ya zauna ya fara aikinsa daman shi Bai bata lokaci in yana aiki yana aiki amma ko wani minute sai ya kalli wurin shigowa agogonsa ya duba yace

haryanzu bata Zo ba yana cikin aikinsa dagowan da zai sakeyi ya ga wani dattijo da wani dan matashi suna tafia su kazo Suka wuce su gani yayi an bude office din Jidda sai wani tunani ya zo

masa toh su waye wannan? guy dinda ke kusa dashi ya tambaya abinda bayayi shi yayi yau yace

"su waye wadannan mutanen da Suka shiga office din Madame"

Wanda ya tambaya yace "Baka sani ba?" Jallal cikin rashin fahimta yace "ban San me ba?"

"hmm wannan dakake gani Mahaifin  madam ne dayan kuma shine sabon manager jiya naji Nima wai an Chanza manager. Nama ji dadi da aka Chanza da ganin wannan baida matsala amma Madame Dincan sai masifa"

Jallal duk Surutan da yakeyi baiji ba illa cemasa da yayi an Chanza manager din ji yayi jikinsa yayi weak yana tunani taya aka Chanza manager yasan da dalili ko dai akwai abinda ya sameta ne sai yaga duk ya damu

Tashi yayi yaje gefe yayi dailing numban ta ya Kira sau daya no answer ya sake Kira same
hankalinsa ya sake tashi shi kanshi bai San meyasa ya damu ba duk wani tunanin fadan su baiyi ba

what matters to him shine yasan ko she's fine

Sake trying yayi yaci sa'a tayi picking

"Assalamu alaikum  jallal ke magana"

ta bangaren Jidda kuma day tayi picking call dinsan Taji kirjinta na bugawa  "Eh na sani ya akayi me"

"Daman naga bakizo office bane" sai ya nuna kamar baisan an Chanza manager ba yanaso yaji daga bakinta. Jidda tayi ajiyar zuciya "Eh an Chanza manager Ina hutawa ne for sometime"

baisan sanda yace "bakida lafia me?" tabe baki tayi  "ba Komi just resting thanks for the concern"

"sai anjima" bai jira wata magana ba ya katse wayar

Saida ya tsaya nan tsawon wasu lokuta yana tunani Wanda shi kaina bansan tunanin me yakeyi ba iska ya fuzar ya wuce aiki ya keyi amma kwata kwata baiyin concentrating illa tunanin
Jidda da yakeyi yadda Suka hadu da fadarsu wani murmurshi yayi mutumin kusa da shi ya taba shi "yane naga kanata wani murmurshi ne" jallal sai ya hade rai ya masa wani
kallo baice masa Komi ba ya cigaba da abinda yakeyi

Jidda ke zaune take a parlour tana Shan ice cream tana latsa waya ji tayi anyi sallama ta amsada

"wa alaikum Salam" Maryam ce kawar ta murmurshi ta saki tareda karasowa inda Jidda ke zaune

"kawas ya jiki? Jiya ne na hadu da sahla ta fada mun wai bakijin dadi ko ki kirani ki fada mun ko"

Jidda ta tabe baki "Sorry dear abubuwan ne sai a hankali"

Maryam ta taba jikinta "to ya jikin?"

"Da sauki fa naji sauki" daidai nan ne mom ta fito "Aa yau Maryam ce a gidanmu" Maryam ta gaida ta "ya gida yasu mamanki"

"duk suna lafia"

Jidda ta tashi tace "muje dakina akwai maganar danakeson fada maki" haka ko akayi Suka tafi dakin Jidda

Bayan sun zauna kan gado ne Maryam take tambayarta  "Me kikeson fada min" Jidda ta sauke ajiyar zuciya

"Hmm Maryam jiya ne dad ya fada mun wai in huta in daina zuwa office zai saka sabon manager"

Maryam dai ido ta zuba mata "Gaskia ya fada ke kanki kinsan bai kamata kina stressing kanki ba kinsan ciwon ki dole zakiyi hakuri kibi decision dinshi"

Jidda tayi magana cikin murya kasa kasa "Maryam in tambayeki idan mutum ya tabaka kaji wani
shock kuma duk sanda kaga wannan sai kaji kirjinka na bugawa me wannan yake nufi"

Maryam ta gyara zama "Toh fa Jidda wannan tambaya fa Akan was?" Jidda tadan Harare ta.

"kidai fadamin in kuma bazaki
fada mun ba shikenan"  Maryam tadanyi dariya

"Umm..ni a tunani na idan ta Gansa tanajin kirjinta na
bugawa to yana iya yiwuwa tanada wani feelings mashi ko.."

Kafin ta karasa maganar Jidda ta
katseta hadda masifa "Ba wani nan" Maryam ta kalleta tace "hanya Jidda i suspect something is fishy tambayan nan dakika mun Akan keda jallal ne tambayan?"  Jidda ta harareta Maryam tayi dariya

"Na ganeki"

Maryam ta sake gyara zama ta riko hannun ta "Jidda yadda naga kin tambayeni maganar nan nasan da wani Abu ki fada mun gaskia nasan you feel something for him amma bakison kiyi admitting ne"

"bawani gaskia nothing is between us" ta fada a takaice.

Maryam shiru tayi ta kyaleta don batason tayi forcing dinta amma ita tasan Jidda na son jallal sai
dai ego dinta bazai barta tayi admitting ba sunsha hirarsu sai bayan la'asar Maryam ta wuce

Ta bangaren jallal bayan ya tashi a office ya wuce gda ya gaida kakarsa ya zauna yaci abinci sa sai ya koma dakinsa yana zaune yayi ajiyar zuciya yana tunanin rayuwa ya tuno abinda mahaifinsa yayi musu a baya Kansa ya girgiza yana tunanin maganarda mahaifinsa ya fada cewan ya yafe masa ajiyar zuciya yayi sai ya tsince Kansa da tunanin Jidda murmurshi ya sakar ma Kansa. Ya rasa meyasa barinta office bai masa dadi ba.












**
Assalamu Alaikum,

First of all, inason na bada hakuri kasancewar na dade banyi updating ba hakan ya faru ne sakamakon dayan account dina da nake managing wanda nake rubuta books na turanci. Insha Allah zanyi kokari na dinga updating frequently idan har zakuyi supporting dina. Na lura baa voting, so please idan kun karanta don't forget to click the star button Nagode. I hope after reading this chapter zakuyi commenting opinions dinku.

Zaku iya checking books dina na dayar account din.

Username: Zaynab10_

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now