Ko data shiga gida ta tararda mom a parlour Wanda duk hankalinta a tashe tana ganin Jidda tataso da wuri tace Jidda yaya kin kirani kuma kin katse na Kira kuma switch off Jidda tadanyi tsaki
tace mom wallahi motar ce ta lalace a hanya kuma na kiraki kenan wayar ta kashe ba charji wash
mom na gaji Bari nadan watsa ruwa Ina sahla mom tayi murmurshi tace nasan dalilin ki na
nemanta Baku rabuwa da kallon film murmurshi tayi ta Nufa hanyar dakinta
"Saida ta watsa ruwa tayi sallah magrib tayi daman olready bayan ta idar da sallah ta shafa amma
bata tashi daga kan sallayan ba sahla ta shigo sis kin dawo Jidda tace eh yau bazaki kalli film din
bane har an Kai rabi Jidda tace Kaina na ciwo idan kin kalla kya bani labari sahla tayi nodding Kai
ok har ta Kai bakin kofa tace yawwa sahla kice azumi ta kawo mun abincina sabon yar aikin da
suke dashi ta tabe baki tace tohm"
"Baifi 5mins ba Wanda ake kira da azumi ta shigo da tray din abinci ta ijiye kan stool dinda ke
dakin tace ga abincin ki Anty sunan da take kiran Jidda kenan jidda tayi nodding Kai ba tare da takalleta ba azumi na fita ta bude cooler taga friend rice ne da kaza sai kuma drink a gefe dama ita
idan zataci abinci dole saita sha drinkKadan ta deba a plate ta fara ci murmurshi tayi wanda ita kanta bata San dalili ba data gama ci
ne ta sha magani dan kanta wani Sara mata yakeyi Sannan ta Sami wuri ta kwanta duk da bawai
bacci takeyi ba amma ta rufe ido ko kanta zai rage ciwo
Ba abinda take tunani sai incident din tazu ita da jallal why ? Meyasa naji wani electric shock a jikina ni kadai nayi feeling ko harda shi sai ta girgiza Kai no I can't think about those stupid thought but still tana thinking a haka har wani bacci ya kwashe ta
Ko da sahla ta shigo dakinta ta tararda ita tayi bacci sai ta tafi parlour wurin mom dake zaune ta
zauna kusa da mom tace mom kinsan sis har tayi bacci tana kokari fa fita da wuri zuwa office
mom tace haka ne dole ta gaji sister ki tanada kokari sosai bata wasa da aikinta dan na lura yawanci idan ta dawo saita duba wasu takardu burina yanzu inga tayi Aure sahla tayi ajiyar zuciya
tace haka ne Nima na kosa Musha biki mom ja mata kumatu tayi kaji ki yanzu tashi kije ki kwanta no films yau kinsan kin kusa komawa skul ta tabe baki tace yeah good night mom ta tashi ta wuce dakinta
_*Washegari*_
Jidda ta tashi da wani irin matsanancin ciwon Kai daka ganta zakasan bata jindadi fuskan ta yayi looking pale mom ce ta shigo dakinta ta zauna gefen gado kusa da ita tace Jidda ya kan naki tace ya danyi sauki Bari na shirya na tafi office mom ta dakatar da ita aa Jidda keda Baki Jin dadi ya kamata ki dan huta mana na tabbata za'ayi taking care of the bank dakyar mom ta shawo kanta dan
Jidda akwai nachi a daki ta zauna ko parlour bata fito ba abinci ma kawo mata akayi a daki"
Jallal ne zaune a desk Dinsa yana attending to customers kamar daga sama yaji Mutanen kusa
da shi suna magana abokina kasan me na lura yau Madame batazo ba sai wurin ya dan Samu peace(wato idan tana nan babu peace ko 😀) Dayan da aka kira da abokina yace kwarai kuwa ko me ya hanata zuwa dan bata taba fashi ba Dayan yace dama a canza ta a kawo mana namiji dan wannan ta cika masifa
Jallal Wanda komai Suka fada a kunnen sa sai yana tunanin to me ya hanata zuwa office can wani zuciya ta cemasa why do you care Abunda ya hanata zuwa ya tabe baki ya cigaba da aikin da yakeyi ranar bai tafi gida ba da wuri "
Kwana biyu kenan Jidda bata zo office ba tana gida don mum ta sanarda dad yace ta huta kwana
biu a gda daka ga Jidda ta rame dan ciwon kwana biu amma kamar Wanda tayi ciwon one week
"Yau ma jallal ya lura cewan Jidda bata zo aiki ba wayansa ya ciro yayi dailing numban ta sai
kuma ya kashe yace why do I care can wani zuciya yace ya Kira ba wani Abu bane just his boss ne ya dau wayar yayi dailing number Jidda dake kwance bata ma sani ba dan a vibrate ta sa wayar
dan tasan za'a Kira daga office kamar kar tayi picking amma kuma ta dauka duba wayar taga jallal
saida wayar ta kusa katsewa tayi picking batayi magana ba jallal yace hello am I speaking to
Madame tace yes yadda yaji muryan ta ransa ya Bada cewan bata jindadi yace umm.... Daman
akwai wasu files da zakiyi signing kuma zamuyi amfani dashi jiya baki zo ba yau ma naji shiru shine nace Bari na Kira baki ta tabe tace banajin dadi ne amma gobe insha Allah zanzo nayi signing duka batasan meyasa tace masa batajin dadi ba jallal yace ok Allah kaimu ta katse wayarta wurgar gefe daya ta fada a ranta Wato saboda wasu so called files ya Kira ko
**
Hello readers yau page din ba yawa sakamakon dan aiki da yamin yawa amma insha Allah next page I will try and make it up to you. hope you'll bear with me thank you 🙏🏻
YOU ARE READING
Jidda Da Jallal
RomanceJidda 'yar shekara 25, wacce ta fito daga gidan masu kudi. Abinda takeso shi takeyi ba'a mata abu ta kyale. Me zai faru da babanta ya sata a matsayin manager a company shi kuma tayi crossing part da Jallal, Daya daga cikin ma'aikatan company wanda b...