Chapter 14

172 28 2
                                    


Jallal zaune a wajen aikinsa yana attending to customers ringing din handline dake desk Dinsa yaji dauka yayi ya sa a kunnensa yace "hello sir" Wanda aka kira da sir "yace kawomin wadannan files din office"

"Ok sir" yace Sannan ya aje wayar

Drawer sa ya bude ya ciro wasu file guda biyu iri daya ya tashi ya Nufa office din knocking yayi
akace come in shiga yayi yace sir ga files din Wanda aka Kira sir din ya karba ya fara duduba files
din

Jallal kallon desk din Wanda aka rubuta sunan mutumin Haidar tunanin Jidda ya farayi baisan
manager nasu ya gama signing ba har yana miko masa files saida mutumin yayi magana Sannan

yace "sorry sir" ya karba files din ya fita

Ko da ya koma desk Dinsa kasa aikata Komi yayi illa tunani da ya cika ransa sai yaji kwata kwata
zaman ya isheshi.  Ya Yanke shawaran ya tunkareta ya Sanar da ita amma bai San taya zaiyi ba

Wayarsa ya dauka yayi dialing number Yusuf daman yace masa yau zai dawo ringing daya Yusuf

yayi picking yace "Yusuf ya ka dawo ne" ta bangaren Yusuf yace "eh saukata kenan yanzu zan shiga gida jallal yace ok sai mun hadu bayan ya gama magana dashi ya katse wayar.

Jidda na zaune parlour tana kallon wani comedy film tana dariya mom dake kitchen Taji ta

"Jidda wannan dariyan fa" cigabawa tayi da dariyan "mom film din ne akwai comedy diyawa in kin kalla zakiji dadi shi" mom ta tabe baki "ki kalla ke kadai ita daman mom bata cika damuwa da kallo ba

Mai aikinsu azumi na jera abinci kan dinning Jidda tama umurnin ta debo mata drink a fridge kitchen taje ta debo mata a glass cup ta kawo mata tana mika mata Ashe Jidda bata rike cup Dinba dakyau duk hankalin ta Akan TV sai ya zube a jikinta

Wani ihu tama Mai aikin hakuri ta shiga bata "Anty kiyi hakuri Bada sani na bane" tsaki Jidda taja "ke bakida hankali ne zaki kawo ma mutum Abu bazakiyi a hankali ba kinsan nawa ne Kayan nan kuwa" hakuri ta cigaba da bata hadda dan hawayenta dan tasan halin
Jidda da masifa tace "Anty ki cire zan wanke maki"

Wani tsaya tayi mata "An Gaya maki zai fita ne ga rigar white" mom dataji hayania ta fito "me ya farune"  Jidda tace "ba wannan Mara hankalin bace daga ta kawo mun drink ta zuba mun a jiki kuma mom kinsan tsadan kayannan ai yanzu bazai fita ba kuma"

Mom tace "azumi ke ya akayi kika zuba mata drink din" azumi cikin muryan kuka tace "hajia ba da gangan nayi ba na miko mata drink din ashe bata rike ba dakyau"  "Dalla can rufe ma
mutane baki nizan maki karya ne" mom ta katseta tace "ya Isa Jidda jeki cire Kayan ke kuma azumi jeki cigaba da aikin ki" hararan ta tayi ta tafi dakinta sai tsaki takeyi cire Kayan tayi ta wurga a Kayan datti sai ta saka simple gown bata koma parlour ba dan rigar ta daya baci yasa film din ya fita a ranta

Bayan jallal ya tashi a office dayaje gida ya watsa ruwa ya zura jallabiyan sa dakin kakarsa ya je don ya Saba duk sanda ya dawo office kafin ya fita sai yaje wurin kakarsa sunyi hira

Sun dan taba hira da kakarsa Noor na makaranta shagon abokinsa Yusuf yaje ya tadda shi a zaune Suka gaisa jallal yace ya hanya Yusuf yace ba gajia fa sunyi Hiran abin duniya

Jallal yace Yusuf inason tambayan ka Kara gyara zama Yusuf yayi yana sauraron abinda jallal zaice

jallal yace "Daman wani ne a wajen aikina ka gane akwai wata dayake so amma bai San yadda zaiyi ya fada mata ba shine nakeson ko kanada dan advice haka kasan ne bawai nasan abubuwa kan relationship ba (hhhh jallal me yayi zafi haka just tell the truth why are you lying )

Yusuf ne yayi hmm "amma ita macen tana son abokin naka" jallal ya cije labe "gaskiya ban sani ba"

Yusuf yace "nidai shawara ta shine yaje ya fada mata abinda ke zuciyar sa inma tanason sa Shima zai sani inma bata so zai sani"

Jallal yayi ajiyar zuciya ya fada a ransa I hope she feels the same sunyi hira sosai sai bayan magrib
jallal ya koma gidan sai wani murmurshi yake yi zama yayi yana tunani ta yadda zaiyi ma Jidda magana kiranta zaiyi ko text zai mata

Numban ta ya Kira ita ko kamar jira takeyi ta amsa sa wayan ta sa a kunne batayi magana ba jallal

"Assalamu Alaikum"

"Wa alaikum salam" ta amsa ta bangarenta harda dan murmushinta saida sukayi shiru nadan wani lokaci

Sannan yace "daman akwai maganar da nakeson muyi dake inkinada tym inason mu had"

tabe baki tayi tace "toh Ina zamu hadu" ya fada mata inda zasu hadu da tym din tohm kawai tace
ta katse wayar wani murmushi ta sakar ma kanta


_*Washegari*_

Jidda sanye da atampan ta super Riga da skirt tayi daurin dan kwalli tayi makeup tayi kyau sosai sai murmurshi takeyi duba wayarta tayi taga time dinda zasu hadu da jallal ya kusa

just less than one hour ta fesa turare sai wani kamshi takeyi key din motan ta tadauka ta fita mom dake zaune a parlour taga jidda taci kwaliya wanda bata saba yi ba sai zata wani occasion"Ina babyn nawa zata ne" murmurshi Jidda tayi  "zan mu fita da maryam ne akwai wata friend dinmu da take aure" half maganar gaskiace cus idan ta gama magana da shi jallal din zasu biki da maryam

"Toh adawo lafia"

Parking lot taje ta shiga range rover. Mai gadi ya bude mata gate ta fita tana tuki cikin natsuwa harta Kai inda zasu hadu wani restaurant bude kofar tayi ta shiga jallal Wanda already yana jiranta yaga ta shigo kyan da tamai yasa ya kasa daina kallonta Har ta iso inda yake murmurshi Suka sakar ma juna zama tayi opposite him

Drink Suka sa aka kawo masu Jidda ta danyi sipping taga jallal baiyi magana ba sai tace

"um..kace zaka mun magana"

Ajiyar zuciya jallal yayi yace Jidda yadda yea Kira sunanta sai Taji gabanta ya fadi ya Kara kiran sunanta yana kallonta itama shi take kallo

"Da farko dai bansan ta inda zan fara ba. There is a saying dayace Your heart doesn't choose who to fall in love with.  na dade inason na fada maki amma na kasa ni kaina na rasa taya akayi hakan yafaru na kamu da sonki cikin kankanin lokaci ba.  Jidda ya Kara kiran sunanta Ina sonki. I've never being in a relationship before but nasan what I feel for you is something strong. Allah yace ta yadda zamu hadu kenan. As our first meeting wasn't a pleasant one. ban tabbatar da hakan ba saida kika bar aiki" haryanzu kallonta yakeyi har cikin zuciyanta Taji dadi saboda jindadi ma she's speechless.

Jallal yace "kinyi shiru Jidda kiyi magana mana. Say something"/gaba daya hankalinsa bai kwanta ba da yaji shiru daga gareta. Magana daya ta iya furtawa

"zanyi tunani"

har suka bar wurin bata ce Komi ba tana tuki tana wani murmurshi. Koda sukaje Biki ita hankalinta ma baya wurin biki maganar jallal kawai ke yawo a kwakwalwarta. She also can't believe it. They are destined to meet and through those circumstances. Data fada ma Maryam ta bata shawara kan she should not give her answer right away, tayi tunani dakyau before making a decision.

Da ta Kai gida tayi horn dukda Mai gadi bai bude mata ba da wuri batayi masifa ba saboda tana cikin farin ciki parking tayi tana shiga parlour taga dad da mom a zaune murmurshi ta saki

"Sannu da dawowa dad"

"yawwa Sannu Jidda" har ta sa kafa zatayi dakinta daji dad yace

"Zo Jidda akwai Wanda nake son kiyi meeting" sai a lokacin Jidda ta San cewa akwai mutum a wurin

murmurshi da takeyi yayi fading tsayawa tayi tana kallon mutumin da akace tayi meeting a ranta ta fada to waye wannan da dad keson nayi meeting ?















**
Toh masu karatu Jallal fa yayi confessing love dinshi ma jidda. Amsarta kawai yake Jira.

shin wanene wannan guy din da Jidda zatayi meeting if you're curious Ku biyoni a next chapter don sanin wanene wannan guy din.

Don't forget to Vote| Comment. Idan nayi receiving votes and comments I'll update early 🤗

Jidda Da JallalWhere stories live. Discover now