"Yau ta kasance Monday Jidda ta shirya cikin Kayanta na office bata wani ci abinci ba sosai tea
Tasha tea ma Rabin cup yau batajin driving so driver ne yakaita data shiga kowa sai gaida ta
yakeyi sai ta leka desk din jallal taga empty ta ta'be baki ta wuce office d'inta takardun ta baza kan
desk d'inta tana dubawa wani guntun tsaki tayi tashi tayi ta d'auko drink a dan madaidaicin fridge d'inta ta zuba a cup tadanyi sipping.
Bayan jallal ya gama sallama da kakarsu cewan zashi Zaria d'aurin auren wani abokinsu ta masa Allah kiyaye hanya tare da Yusuf sukaje da motan haya.
Bayan ta gama Shan drink d'in tana Danna laptop dinta sai Taji 'kamar hayania a farko ta watsar
amma da taga hayaniyar yayi yawa sai ta tashi taje dubawaWata mata ta gani tana zagin cikin ma aikatan shi kuma dan bai San matsala a aikinsa sai bai
kulata ba illa hakuri da yake bata ido ta kafe su dashi saida ta bari matar ta gama masifarta sannan tayi magana. "Meke faruwa ne nakejin hayaniya"
Matar ta kalli Jidda daga sama har kasa tace "ke kuma wacece" Jidda tayi murmurshi ta gefen baki tace
"nice manager bank dinnan" ido Matan ta zaro a farko bata yadda ba amma dataji ance Madame ta juyo ta Kara kallon Jidda da ke magana da mutumin tace fad'a mun abinda ya faru take masifa
yace
um..daman wai kudi zatasa a account d'inta kuma jallal bai zo ba ga system 'Dina baida network shine nace tad'an jira anjima kafinnan network din ya dawo shine take masifa wai bansan aikina ba
Jidda ta juyo ta kalli matar Wanda har yanzu mamaki takeyi wai Jidda ce manager Jidda tace hajia kiyi hakuri Mai yin aikin ne baya nan amma karki damu yanzu za'ayi attending dinki dakyar ta shawo kan matar dan wai ma zata bar bank din tama guy din sign da ido alamar ya sake trying
aka ko ci sa'a yayi wannan Karan yayi signing Jidda ta Kara bata ha'kuri ta rakata har ta fita. Badan batajin maganaba da saita nuna ma matar. dawo Wa tayi office d"inta tana tunani wani tafiya ne yafi aikinsa muhimmaci wani ciwon Kai taji ya kamata "mtsw...duk shi yaja I will deduct from his salary."
Bayan ta tashi daga office ta biya gidansu Maryam tayi parking a bakin gate 'Dinsu ta 'Kira Maryam a waya cewan gata 'kofar gidansu baifi 3mins ba Maryam ta fito tace Jidda yau Kece a gidanmu Yaushe Rabon kizo gidanmu Jidda ta harareta ai gashi nazo yau Maryam tace mushiga ciki mana.
Maman Maryam ce zaune a parlour Jidda ta gaida ta "Ina yini umma" da far'anta ta amsa "lahia lau Jidda ya mutan gda" "duk kalau suke" Sannan Suka tafi d'akin Maryam, Maryam tace me zan kawo maki Jidda tace ba Komi a koshe nake wallahi tace ok sunsha hira sosai ba ita ta bar gidan ba sai kusan magrib kullum Suka had'u da maryam sai sunyi hira dan tana debe mata kewa tun kafin Jidda ta tafi abroad suke 'kawance
Bayan ta tafi gda ta gaida mom dake zaune a couch Sannan ta nufi d'akinta ta watsa ruwa Mai
dumi Sannan ta saka shigan baccin ta sahla ce ta shigo d'akinta tace sis an fara programme din fa
Jidda tace ok ganinan zuwa ta d'au wayanta dake kan gado ta sau'ko ta zauna kusa da mom Suka fara kallo gaba daya concentration d'inta a kan film din mom ko tashi tayi ta tafi d'akinta wai bazata iya bata idonta da kallo ba saida Suka kalla program din tas.
ba su Suka gama kallon ba sai 11 Sannan kowa ya yi hanyar d'akinsa.
*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~
"At office
"Yau Jidda ta makara bata tashi ba da wuri so bata zo office ba da wuri data shigo direct idon ta
jallal ya hango daidai lokacin Shima ya dago fuskan sa ji tayi girjinta ya buga saurin dauke idonta tayi.
wucewa tazoyi Anata mata good morning Madam. kamar daga sama Taji muryar jallal wai good morning Madam
mamaki ne ya cikata don jallal bai taba gaidata ba idan ta shigo saidai sauran su gaidata without
any thinking Taji tace morning hadda murmurshi sai daga baya tayi realizing Abunda tayi sai
kawai ta juya ta tafi office d'intatelephone line dake desk din tayi dialing "Come to my office now." Abinda ta fada kenan ta katse line din
Jim kad'an jallal yashigo fuskar sa a hade.
"Ranar ka fad'a mun bazaka zo office ba amma Baka fad'a mun dalili ba." Ta fada ba tareda ta kalli inda yake ba.
"I can't tell you saboda it's my personal matter." ta'be baki tayi "oh I see shikenan you can go daman abinda na kiraka in tambaye ka kenan kuma tunda kace personal matter 'Dinka ne no problem you can go." ya bude baki kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya tafi .
"Da wannan masifa nashi wa zai sosi kullum mutum sai hade rai."
Lokacin tashin office yayi kowa na hada kayansa na tafiya gida.
Bayan Jidda ta gama aikinta ta d'au Jakarta ta fice ko kallon wurin jallal batayi ba tana cikin tafia
har ta Kai Rabin hanya sai Taji motar na wani sound sai tayi parking wuri daya ta kashe motan kunnawan da zatayi mota yaki tashi ta sake murd'a key d'in still bai tashi ba ta d'auko wayarta a jaka tayi dailing numban mum har tayi picking tace hello taga ya katse duba wanta Ashe wayan ne ya mutu daman jiya batayi charji ba gashi kuma tayi chatting dashi tsaki tayi ta fita daga motan ta
fara dube dube tana tsaida motoci amma ba Wanda ya tsaya saboda lokacin yamma ta kusa kowa
na hanyar zuwa gida wani mota tayi sa'a ya tsaya tace mallam dan Allah inason kadan duba min motan nan ne ya'ki tashi ne mutumin yace kiyi ha'kuri sauri nakeyi duk motar data tsaida basu tsayawa gashi ba shago kusa balle ta Sami mutane don taimako
Jallal ne kan mashin 'Dinsa yana tu'ki cikin natsuwa juya wan da zaiyi ya hango wata kamar Jidda daya matso kusa sai yaga he's not mistaken ita d'ince toh me takeyi har yanzu bata tafi ba?
"Har zai tafi sai kuma ya tsaya yace me yafaru ne kika tsaya kan titi baki tafi taso yin banza dashi
amma sai taga idan tayi haka kanta zata cuta sai tace motan ce Ta'ki tashi tana magana tana wani fusgar iska
parking mashin dinsa yayiYa bude gaban motan ya tattaba wani Abu sai kuma ya rufe yace motan naki ya Sami matsala sai kin kaita gyara. Zai tashi idan kin kunna amma bazakiyi nisa ba zai Kara mutuwa.
yanzu dai ki nemi mota ki tafi gida daganan sai ki nemi Mai gyara dan ba Mai gyara nan kusa bata cemasa Komi ba taje gefe tana dube dube ko zata Samu Wanda zai mata lift jallal har tad'an bashi tausayi yadda ya ganta kamar zatayi kuka yace idan bazaki damu ba sai in saukeki ta fusgar da
iska tace aa ba damuwa. A ranta tace ni in hau mashin on top of that mashin din wannan low class guy din.
Yadda yaga fuskan nan nata yasan baza ta so spending wasu minute ba a lokacin amma saboda ego bazata iya cewa ya rage mata hanya ba yace toh shikenan har ya Juya zai tafi tace tsaya dan tasan idan ya tafi da wuya ta Sami lift tace muje kaji ta yau ne first time d'inta na hawan mashin
yadda ta hau mashin din har dariya yaso ya Kama jallal
Ya tada mashin d"in Suka fara tafiya yadda ta zauna a mashin din kamar zata fad'i sunzo wurin
traffic ya taka Burki ta kusan fadi da sauri ta riko rigarsa ba ita kad'ai Taji shock ba hatta shi jallal din da sauri ta sake ba Wanda yayi magana har Suka isa layinsu ya sauke ta ta juya kenan zata shige ta juyo tace thank you a takaice ta shige murmurshi jallal yayi ya tada mashin Dinsa ya tafi.
YOU ARE READING
Jidda Da Jallal
RomanceJidda 'yar shekara 25, wacce ta fito daga gidan masu kudi. Abinda takeso shi takeyi ba'a mata abu ta kyale. Me zai faru da babanta ya sata a matsayin manager a company shi kuma tayi crossing part da Jallal, Daya daga cikin ma'aikatan company wanda b...