Thriller

278 20 6
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.




              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            (Kᴡᴀʀɪ)
                           

Nᴀ
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

'''Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.'''

*THRILLER..*

     •••Ƙaddara tamkar yanda igiyar ruwa ke kaɗa teku duk girmansa,a wani lokaci kuma za mu iya kiranta da guguwa mai ƙarfin gaske,ko yanda hamada ke kwararowa,haka take bayyana a cikin shafin rayuwarmu,sai kuma ta ɓace lokaci guda kamar walƙiya da haskenta ke disashewa a cikin daƙiƙu,yayin da take tafiyar ruwa da farin cikin dake tattare cikin rayuwar mutum,ba tare da tausayi ko imani ba,haka za tayi fatali da komai tayi wucewarta,ba tare da waiwayen baya ta gano irin ɓarnar data tafkawa da yawan al'umma ba. Kamar hakane ƙaddara ta kutso cikin rayuwar FANNAH,yayin da tata ƙaddarar tai mata dirar mikiya a lokacin da bata gama sanin wace ce ita ba. While a gefe ɗaya kuma tai wasan kura da HAMDIYYA inda ta rasa duk wani abu da take tunanin ta fi ƙarfinsa,ta kuma yi juyin wainar masa da ABDULMUTALLAB lokacin da ya nemi FANNAH cikin rayuwarsa ya rasa.. Shin mene yake faruwa cikin rayuwar waɗannan mutanen da suke zaune a mabanbantan gurare,mene ne kuma zai haɗa su? Sannan wane al'amari ne yake gindayawa tsakani ya raba su?

'''ƊANƊANO..'''

        •••Hawaye sosai suke saukowa idonta da wani irin Baby voice tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya dake kusa da ita ta kalleta tace "ohh! Bari a kirasu sai kuyi sallama a gurguje kinga yanzu muna sauri ne kada dare yai mana,hanyar Abuja babu kyau kwanakin nan" ita dai bata sake cewa komai ba kuka kawai take kamar ranta zai fita,Hamdiyya ta sauke glasses ɗin gefenta ta kalli Baffa dake tsaye tace "Baba tana son yin sallama da su Aalima wai" Baffa ya kalleta ji yake kamar zai daketa,ya daure yace "ahh tou! Ta jira a nan bari su fito suyi sallamar daga nan" da wani irin sauri yana kaɗa babbar rigarsa ya koma cikin gidan ya kira ƴan uwanta da sukayi cirko² a tsakar gidan sunyi tunda Baffa suka ga fitarsu,yana shiga gidan ya kallesu yace "kuzo kuyi sallama da su" da sauri duk suka biyoshi su uku,Aalima tana kuka tun bata ji abunda yake faruwa ba,amma ganin yanda Baffa ya ɗauki kayan ƴar uwar tasu ya tabbatar mata da wani wajen za'a tafi da ita,ta kusa da gefen Hamdiyya duk suka tsaya,a hankali ta ɗago tana kallon su da tashin hankali tace "Yaa Adija dan Allah kice da Baffanmu ya barni a gurinku,ni ba na son binsu,na yarda yai min auren da yace,amma dan Allah kada ya rabani da ku,pleaseee" babbar cikinsu da ta kira Adija ta juya ta kalli Baffa hawaye suna cika mata idanu tace "Baffa ina za'a tafi da ita?" Yace "aiki za ta je idan ta gama za ta dawo" Adija tace "yaushe? Wane irin aiki ne Baffa? Me yasa sai *FANNAH* Baffa? Madadin ka turani ko Ashey,ko Aalima.." Wani irin tsawa Baffa yayi mata yace "kuyi sallama za su tafi,ba abunda na kirawoku kuyi ba kenan ku tsare ni da tambayoyi marasa kan gado" Aalima tana kallonta tace "little i'm gonna missed u" sake fashewa da kuka Fannah tayi tace "Yaa Aalima dan Allah ku roƙi Baffa ya barni tare da ku" Baffa ya kallesu ganin za su dama masa lissafi yace "tou maza ku wuce ku koma gida sai na shigo" yanda yake kaɗa su kamar awakai dole yasa duka suka juya,Ashey kam ta kasa magana jikinta sai rawa yake,sosai ta shiga damuwa da tashin hankali,suna waigen ƙanwarsu dake kuka itama tana kallonsu har suka shiga soron gidansu,Baffa ya matsa yana yiwa su Hamdiyya addu'ar sauka lafiya suna amsawa da farin ciki,sanda Malam Ado ya juya kan motar suka nufi hanyar fita daga line sannan ya juya ya nufi gida yana murmusawa,Fannah tana ganin sun fita line gidansu ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,duk cikin kasu sauraron kukanta Hamdiyya kawai ta iya lallashinta,Mummy Shafa'atu kam taɓe baki tayi tace "za ki gaji ki bari,dan na ga alama tunda mahaifinki ya karɓi kwangilar nan ba zai dawo da kuɗin aikin ba.." Duk abunda suke yana gaba yana jinsu amma bai ko ce uffan ba hasalima idanunsa a lumshe suke kamar mai bacci,sanda suka ɗauki hanyar barin Kano suna ta sharar gudu kan coalter,a hankali kuma tai shiru dan kanta tana sauke ajiyar zuciya,kafin suyi nisa wani irin bacci ya fara ɗaukanta,Malam Ado dake ta driving shima ko tari baiba gudu kawai yake akan titi yana murmusawa...

     Waiii³! Wannan alƙalamin daban yake,ku dai kada ku bari ayi babu ku,labari ne dake ɗauke da mabanbantan al'amura masu rikitarwa,tausayi,ƙalubale,zazzafar ƙaddara,tare da wani irin salon soyayya mai tsayawa a rai. Idan baki taɓa karanta littafinaba babu lallai ki iya gane yaren da nake ƴar uwa,amma a wannan karon ina sanar maku cewa duk wanda bai shigo anyi da shi ba,tabbas za'a barshi a baya...😎  ‍🔥رومانسيه of a special kind awaits u in this novel of CIWO A JIKIN WANI.. Don't missed it out. قريبا...🚴🏻‍♀️ Stay tuned.🥰 Ku dai ku biyo alƙalamina a wannan lokacin domin samun gamsasshiyar amsarku game da abubuwan da za su faru,in sha Allah littafin zai fara zuwa maku ranar Saturday 1st/Oct,2022.



#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now