ABUBUWAN DA AKE SO MIJI YA FI MATAR SA DA SU

10 1 0
                                    

11. ABUBUWAN DA AKE SO MIJI YA FI MATAR SA DA SU
Tambaya: Assalamu alaikum, malam da fatan kana lafiya,
wasu tambayoyi nake rokon Malam daya taimakamin da
amsoshin su in Allah yasa malam yasansu, shin malam wai
akwai wasu abubuwa uku da ake so mace tafi mijin da za ta
aura da su, sannan shima akwai abu guda uku da akeso ya
fita da su?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka
akansu, da fatan malam ya sansu, kuma za'a taimakamin da
su, nagode.
Amsa :
To dan'unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa,
ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta
fi shi kananan shekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake
sonta . Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta
kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta Ana so su hadu a abubuwa
uku : ya zama akwai yaran da yake hada su, ya zama
addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan
aka samu wadannan uku-ukun, to za'a samu jin dadin aure.
don neman karin bayani ka nemi shirin minbarin malamai
da na yi a freedom radio Kano na ranar : 3 ga Ramadhan
1434 A.H
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now