SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCIN SU

11 1 0
                                    

7. SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCIN SU
Tambaya:
Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan "KUDRA da kuma
SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.
Amsa:
To 'yar'uwa, wannan yana daga cikin mas'aloli masu
mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwaka game da
hakan:
Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan
ciwo, ya fito daga gabanta.
Kudra kuwa na nufin : ruwa ya ringa fitowa daga farjin
mace, wanda kalar sa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da
baki wato kamar ruwa gurbatacce,
Dangane da hukuncin su kuwa : idan daya daga cikinsu ya
kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila
kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan
kuma bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fadin Ummu
adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra bayan tsarki
a cikin haila) Abu Dawud ya rawaito shi da sanadi mai
inganci, A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin da suke
sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan
da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi
gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, ta yadda za mu yi
amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki,
ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila
ba, hadisin A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana
cikin haila ta yadda za ta kirga da su. Don neman karin
bayani duba: Dima'uddabi'iy a shafi na: 8
Allah ne mafi sani
6.12.2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now