14. INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME?

4 0 0
                                    

14. INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA
YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME?
Tambaya :
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura
kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome,
amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki,
ko kuma na kyale shi na yi aurena? saboda gaskiya ina son
wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia ?
Amsa :
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa
kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta :228, a
suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi
mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan
ta, amma zai iya shiga cikin manema. Idan ya yi da'awar
cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba,
sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar
hakan. Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da
za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake
kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan
yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi,
idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta . Saidai
wasu malaman suna cewa : idan har matar ta gaskata shi, to
ya isa, ko da bai kawo shaidu ba . Duba: Al-mabsud 2\23 da
Mawahibul-jalil 5/408
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25-12-2014

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now