ANA YIWA IYALI NA WANKAN JEGO, KO YA HALATTA?

10 0 0
                                    


9. ANA YIWA IYALI NA WANKAN JEGO, KO YA HALATTA?
Tambaya:

Salam malam don Allah ka taimaka min ka amsa tambaya
ta. ni dai malam gaskiya hankali na ya ki kwantawa
sakamakon al'adar wankan jego da ake yi a kasar hausa.
iyalina ta haihu an kawo wata tana yi mata wanka, to malam
ya hukuncin ya ke duba ga haramcin nuna tsaraici ga wani,
don Allah malam ka daure ka Amsa don hankali na ba'a
kwance yake ba.
Amsa:
To malam akwai hanyoyin na zamani wadanda za'a iya
amfani da su ba tare da an yi wankan jego ba, kamar amfani
da kwayoyi na asibiti, saidai idan ya zama babu makawa sai
an yi wankan na jego kuma wata ce za ta yi mata, kamar ya
zama haihuwar fari ce kuma babu halin da za'a iya sayen
kwayoyi saboda talauci, to hukuncin wannan zai yi daidai da
hukuncin likitan da take kula da lalurar mata, saboda shi ma
wankan jego ana yinsa ne saboda magani. A shari'ance ya
wajaba ga likita ya yi taka-tsantsan wajan kallon al'aurar
mara lafiya ta yadda ba zai kalli wani bangare na al'aurar
mara lafiya ba sai gwargwadon lalura, domin daga cikin
ka'idojin shari'a shi ne duk abin da ya halatta saboda lalura,
to ya wajaba a tsaya gwargwadon lalurar, wannan ya sa idan
da zai kalli sama da haka, sai ya zama mai laifi a wajan Allah.
Al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace tana farawa ne daga
cibiya zuwa guiwa a zance mafi inganci, don haka mai
wankan jego za ta kalli gwargwadon abin da ya wajaba ta
kalla don tabbatar da lafiyar mai jego, idan kuma akwai hanyar da za ta bi ta yi mata wankan ba tare da kallon
al'aurar ta ba, to wannan shi ne ya wajaba.
Duba kwatankwacin wannan mas'alar a Alkawa'idul kulliya na
Usman Shabirr shafi na : 222
Allah ne mafi sani
14-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now