YA YAGA TAKARDAR SAKIN KAFIN MATAR SA TA GANI

9 0 0
                                    

6. YA YAGA TAKARDAR SAKIN KAFIN MATARSA TA GANI
Tambaya: Assalamu alaikum, malam shin idan mutum ya
rubuta takardar saki ya aje, sai wani ya gani shin matar ta
shi tasaku?
Amsa:
Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya
kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta
saku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi : "Allah ya yafewa al'umata abin da ta riya a zuciyar ta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata" ka ga kuma
rubutu aiki ne. Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta
hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja kenan. Wannan shi ne
mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi'i mafi
inganci. Duba Al-mugni : 7\486 Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/1/2014

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now