15. IDDAR MATAR DA AKA SAKA SHIKA NA UKU

4 0 0
                                    

15. IDDAR MATAR DA AKA SAKA SHIKA NA
UKU
Tambaya :
Sheik shin dole ga matar da mijinta ya yi mata shika uku sai
ta yi jini uku, ko idan ta yi jini daya ya yi, tun da babu kome?
Amsa :
To dan'uwa Mazhabar dukkan manyan malaman fiqhu shi ne
za ta yi jini uku ne, ko tsarki uku, saboda fadin Allah a cikin
suratul Bakara aya ta : 228 "Kuma matan aka saka, to za su
jira tsawon jinane uku", wannan ayar ba ta bambance
tsakanin matar aka saka shika daya ba, da wacce aka saka
saki uku, don haka sai hukuncin ya zama daya, Jassas yana
cewa babu sabani a cikin hakan.
Saidai Ibnu Taimiyya ya hakaito wani kauli wanda yake cewa:
za ta yi jini daya ne tun da babu kome, saboda an shar'anta
yin jini uku ne don tsawaitawa miji lokacin yin kome, tun da
kubutar mahaifa tana tabbata da yin jini daya. Wannan kaulin
ya sabawa zahirin ayar da ta gabata, sannan kasancewar
iddar matar da mijinta ya mutu wata hudu da kwana goma,
yana nuna cewa, ba saboda tsawaita lokacin kome kawai aka
shar'anta idda ba, tun da ita babu wanda zai mata kome.
Don neman karin bayani duba: Ahkamul-qur'an na Jassas
2/67, da kuma Ahkamul-qur'an na Ibunl-araby 1/185 da
Majmu'ul fatawaa 32\342.
29-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

FATAWOYIN DR.JAMILU ZAREWA NA MUSULUNCI.Where stories live. Discover now