part 15 & 17 &18

2.3K 76 1
                                    

❤❤❤❤❤❤❤❤❤
                  *YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
                      Na
           Hapsat  Musa
           (Hapsy Baby)

Pure moment of life writes
P.m.l

146_150


Yazeed motarshi yashiga yanufi Gidansu yanashiga ya taradda da dady yauma bai fita parking d'in motarshi tayi yashiga ciki taradda su yayi A Falo

"Mimi morning
Dady morning."

"Yazeed Antashi lafiya.?"
"Lafiya lau Dady."
"Ya Muneera?."
Tana lafiya lau tana gaisheku."

"Muna Amsawa sosai."

Yazeed mik'ewa yayi zai tafi

Mimi ta mik'e ina zuwa Bari na d'auko maka d'an gidan muneera kakai Mata."

Mimi tashiga ciki ba'a jimaba sai Gata d'auke da wata K'aramar cooler
Taba Yazeed bankwana yayi dasu

B'angaren Kaka yashiga
"Tsohuwa mai ran K'arfe
Ina kwana."

"Yazeedu lafiya ya Jumallah kuma?"

"Kaka kidaina cewa Jumallah  Muneera zakice."
"Banacewa to itama tagaji tabari."

"Shikenan keda ita."

M'ikewa yayi zai tafi
"Natafi."
"Kagaidata Kajiko."
"Kozakiyimata zaman D'aki ne.?"

"A,a. Kuje can."
Haka Yazeed da Kaka sukai ta wasa da dariya Kamar ba yazeed ba lalai.

Haka yafito yashiga motarshi yakoma Gidanshi dake Unguwar Sarki.

Yana shiga yaji K'arar television Amma babu kowa
Falon Kashe Kallon yayi yajuya yanufi D'akinshi jiyayi yayi tuntube da Mutum.

Muneera yagani Kwance  tana bacci da Alamu Kuma bacci yayi Mata dad'i
Ga sanyi Ac yana Bugunta

Tsaye yayi yana Kallon Muneera gyaramata kwanciyar yayi ya aje cooler ya shiga D'akinshi

Kwanciya yayi  tare da runtse idanuwanshi Surar Muneera yake Kallon cikin idanuwanshi

Jiyake Kamar yajita jikinshi yanzu
Amma yasan tsanar da Muneera tayi mashi tayi Yawa yaushe zata Koyi sonshi.

Muneera tana Farkawa taga Kamar bayadda ta kwanta bata kawo ma ranta Komai ba ta Mik'e tanufi D'akinta
Toilet ta Koma ta K'ara watsama Jikinta Ruwa

Wando ne tasa Had'e dawata Riga  ta matse ta tumke Gashinta tayi bata d'aura d'an kwali ba tafito
Falon.
Kawai jitayi cikin yafara Kuka yunwa.

Yazeed fitowa yayi da ruwa jikinshi.

Numfashi shi Kusan D'aukewa yayi Ganin shigar da Muneera tayi
Tsaye yayi yana Kallon ta.

Hanyar kitchen tanufa domin ta Samar wa cikinta Abinchi.

Jitayi Anjawota kawai.
Yazeed rikecewa yayi yafara Kissing d'inta muneera ta ko Ina.

Wani Kuka tasaki
"Kasakeni mugu Azzalumi."

Bugu tafara Kaima Yazeed
Sakin tayi yayi idanuwanshi sun kad'a sunyi jawur Kamar garwashi
"Haba Muneera wai sai yaushe zaki manta da Abinda yafaru ne? ko Allah manayi mashi laifi yayemana Kisani. Kitausaya min pls."

Kallonnshi tayi Kawai ta watsar 
"Kamanta Bagidajiya yar Kauye ce. wadda Kace bazaka tab'a so Har Abada

Tayaya Kake zaton zaka samun soyayyata ne?"

"Sorry My Muneera."

"Nice taka lailai Kanada Aiki."

Juyowatayi tanufi Hanyar kitchen 
Indomie kawai ta D'ora Minti
Biyar ta dahu ta D'auko tafito
Tana zama idonta yahango
Mata  colooer mik'ewa ta d'aukota tana Bud'awa taga
Rice and Beans ne yaji Kayan Had'i yanata tashi.
K'amshi
"Wow fantastic."
Spoon tasa tafara cinshi
Saida taji babu wurin sannan
Nan tabar kayan tashige D'aki
Bud'a Firji tayi
Ta D'auki ruwa Tasha
Tayi Hamdallah
Takoma gado tacigaba da latsa wayanta

YazeedWhere stories live. Discover now