❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
Hapsat Musa
Hapsy Baby*Pure moment of life* *writers*
*P M L*176_180
Kitchen d'in yashiga A Hankali Ganin yadda tamaida hankali tana girki Ahankali ya lallabo ta bayanta ya rufemata idanuwa murmushi tayi kawai domin K'amshi tureren shi kawai yasanar da ita,
"Yaya Yazeed har kadawo?"
Dawowa yayi Gabanta ya tsaya
"Ya akayi kikasan nine?""Yaya Yazeed nasan baka wuce Kai ne kuma..."
"Kuma me?"
"Babu komai."
"Uhumm uhum nisai kinfad'aman"
"Babu komai fa."
Matsowa yayi daf da ita kowa yanajin Numfashi kowa."Fad'aman"
"Nafad'a maka Bari na ida girkina kar yak'one"
"Ina tsaye kina girki Dani za"ayi barikiga ma mezan miki yanzu?"
"Yaya Yazeed yanzu kadawo fa kabari na ida kingin Kad'an fa"Duk dahakan sai natayaki fa
NaK'i wayonki yarinya"Haka Yazeed ya ida taya Muneera girki Har suka Gama cikin Nishad'i
Shiga D'akinshi yayi yacanza wasu Kayan
Fitowa yayi,
Muneera kuma tana shirya Abinci A dinning"Nidai natafi masallachi sai nadawo"
"Yaya yazeed sai kayi sallar isha'i sannan zaka dawo?"
"Eh mana"
"Shikenan 'A dawo lafiya"
Bataji tahowarshiba jitayi Ansakarmata kiss A kunci kawai.
"Sai nadawo."
Binshi tayi da ido har yafita
"Tafiyar shima Abin Kallo ce jiyadda yake yinta cikin natsuwa."Bisa Kujerar dinning d'in tazauna tagumi tayi
"Meyasa kwana biyu nan in inatare da Yaya Yazeed nakejin wani Abu yanayiman yawo?
Inkuma bayanan sai Naji babu D'adi?"
Haka Muneera tai tunani jitayi Antada sallah yasa itama mik'ewa tashiga ciki tayi watsa Ruwa tayi tafito da Alwalla tada sallah,
Itama tanagama tanufi wajen kayanta wata rigar Atamfa ce ta d'auko
Tasa Rigar babu D'ankwali kawai ta d'aura bisa K'anta,Turaruka tadau'ko ta feshe jikinta dasu dawo palour tayi tazauna Ta kunna Kallo
kafin Afara sallar isha'i
tana zaune taji Ankira sallar isha'i,Kashe Kallon tayi tashiga ciki dama da Alwallar ta
Tadawa kawai tayi,Bayan tagama ne ta linke Carpet D'in sallar tare da Hijab D'in datayi sallar takaisu ma'ajinsu,
Takomo palour tazauna bata dad'e dazama taji K'arar Bud'e Kyaure tasan Yazeed ne Amma bata d'ago Fuska jitayi bai karasoba
D'aga idanuwanta tayi taga ko ya shiga D'aki ne
Taganshi tsaye
"Yaya Yazeed menene zakayi tsaye Bakin k'ofa?"
"Bakece Baki taso kika tarbeni ba."
Gwalo Fuska tayi Almar mamaki
"Kai Yaya Yazeed yanzu sai nataso na tarbeka?"
"Eh mana"
YOU ARE READING
Yazeed
Mystery / ThrillerYa taso miskili yakuma tsani duk macen da bata wayewa kwatsam..saigashi za'a hadashi Aure da yar kawunshi ko ya hakan zai kasance kubiyoni..