🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)Alk'alamin
JANNAH JAY
Wattpad @jannahjay8Marubuciyar
A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin KishiShafi na Bakwai
Bayan an gama gwaje-gwaje aka tabbatar masa da Zee tana d'auke da juna biyu, hakan ba k'aramin farin ciki yaji ba, dama abunda tayi niyyar sanar masa kenan weekend din daya gabata, tayi gwaji da gishiri ta tabbatar da canji, amma yanzun da taji daga asibitin hakan ya bata tabbacin tana d'auke da juna biyun, cike da farin ciki suka dawo gida, ita kuwa duk da farin cikin da take ciki bai hana ta d'aure masa ba, dagaske take so ta nuna masa kuskuren da yake aikatawa, shi kuwa sai lallab'ata yake, burinsa d'aya ta sauko daga fushin da take.
Kasancewar bai koma Asibiti ba zama yayi dan kula da ita, tamabayarta yayi me take son ci ya girka mata ko ya sayo mata, rai a had'e tace " Bana buk'atar komai" sai da yasa fuskar tausayi yace " Haba Halaly, ya zakice bakison komai, nasan kinaso kice har yanzu hucewa ne baki yiba,naga jiya na miki alk'awarin daina kawosu kullum gidan kodan privacy d'inmu, kinsan sabon da akai tun k'uruciya shiyasa kika ga banson suji a ransu don mace na wofintar dasu" kallonshi tayi tace " Ba fad'a ta bane, ma'aiki ne ya sanar mana girman laifin wanda ke tona asirin iyalinsa, hake fayyace rayuwarsu ta aure t.. " jan tsaki yayi yace " Ya isa naga tuntuni mukai wannan maganar, na fad'a maki ai don neman shawara kika ga na fayyace wa Idris maganar nan, kuma ko su Ja'afar hirar da nayi dasu don na kwad'aita musu aurene su maida kai suyi, karki manta duka sun haura shekara talatin, kullum iyayensu na nuna mana mu jasu suyi aure, tunda mune mafi kusa dasu, kamar Innar Hamza duk sanda nayi waya da ita wallahi k'orafinta kenan" wani takaicine ya taso mata meyasa bazai gane ba, ai hanyar da ya biyo ba ita ta dace ba " Inaso ka sani bance laifine ka nuna musu k'ima da tagomashin aure ba, sai dai hanyar da ka biyo bata dace ba sam, ta sab'awa koyarwar addini ka nemi wata hanyar, shawarace" ta k'arasa fad'a tare da rufe fuskarta da duka hannayenta don tuni wasu hawaye ke neman zubowa a kumatunta, shiga lallashinta yayi yace " Yanzu dai ai magana ta wuce nace zan kiyaye, me kikeso kici? Me zan sayo miki" batace dashi komai ba sai idonta da ta zuba masa, sai ya shiga irgo abubuwan da yasan tanaso taita girgiza kai k'arshe fita yayi kurum don ya sayo abubuwa yasan dole a ciki za'a samu wanda ya mata.
Tunda ya fita take nazari, ta sak'a ta wara yafi ba adadi, dawa yakamata tayi shawarane, abun ya fara wuce tunanin ta, duk yanda take daukarshi a sauki ashe ya wuce nan, tasan ya sami ilmin addini shiyasa take ganin daga ta fada masa zai gane kuskuren, amma kash da alama kwata-kwata shi bai daukeshi akan kuskure ba balle tasa rai zai gyara, tabbas Sulaiman yana kan b'ata, ya zatayi ne, k'ira ne ya shigo a wayarta Salma ce, sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta shiga waya da ita, sun jima suna hira sannan ta kashe, ba'a jima ba Innar Sulaiman ta k'irata cike da ladabi ta gaisheta sannan ta duba jikin nata, har kunya taji ta kamata don tasan dole Sulaiman ya sanar mata maganar cikinta, aikuwa Inna tayi ta jadda da mata take kula banda garaje da yawo ko aikin wahala, tace mata Insha Allah za'a kiyaye.
Da kaya da yawa yazo abubuwan bazasu fad'uba, yaci sa'a tana ganin ledar kilishi taji kwadayinsa, aikuwa taci sosai ogan sai washe baki yake, amma tana gamawa tayi shirinta na bacci ta bashi k'eya, ko hira bata bari sun tab'a ba, kama baki yayi matsalar masu shiru-shiru kenan basu iya fushi ba, tana jinsa yanda yajima yana jingine a jikin gado kafin ya kwanta a hankali ya d'an janyo bayanta yana kokarin rungumeta ta matsa can gefe, abunda ta rik'a sai yaji bazaike fallasasu ba zata cigaba da bashi jikinta.
Washegari ta tashi garau take jinta sai dan rashin k'arfin jiki, Baba tazo ta mata shara, tana sanye da boubou a gabanta da bowl a mai d'auke da fruit a ciki ya fito da shirin fita Asibiti, gaishe dashi tayi tare da d'an basarwa kallon gefe yayi yaga Baba ta nufi kitchen, yayi hamdala ya zauna kusa da ita yace " Haba Halaly kwana wajan biyar ko kiss bakimin, baki hugging d'ina ba wani contacts tsakanina dake, ki duba ki gani har fad'awa nayi, please ki yafewa Babynki mana " zuba masa idonta tayi a yangance sannan tace " Ni na yafe maka ai tuntuni, kawai dai inaso karka sake bankad'a masu sirrunmu ne" dan murmushi tayi hakan ya bashi damar rungumeta tare da sakin ajiyar zuciya, sai kuma ya dago ya kalli fuskarta bakinta ya rik'e na wasu mintuna sannan ya saki " Kaman kar na tafi nakeji" murmushi tayi tace " Kaga jiya bakaje ba yakamata kaje, kodan taimakon Al'umma" mik'ewa yayi " Kowane lokaci kina iya ganina, ban iya jiran la'asar gaskiya" peck ya mata ya fita.
![](https://img.wattpad.com/cover/214543556-288-k01cf9d.jpg)
YOU ARE READING
RASHIN SIRRU (sharrin abokai)
General FictionYana shigowa yaji wayar matar tasa tana ringing sai dai kafin ya iso kan gado inda take tuni wayar ta tsinke, basarwa yayi ya isa kan gadon yazauna tare da furta "wash" ya zare hular dake kansa, karar shigowar message wayar tayi da same number da ta...