*SO NE SANADI*
Na
*Rahma Kabir*
Mrs MGBismillahir Rahmanir Rahim.
Short love story.
Gargadi.
Banyarda a juya min labari zuwa wata fuska ba.1 ~ 2
Alhaji Aliyu babban d'an kasuwa ne, yana sarar da dilan takalma da jakukuna ga kananan 'yan kasuwa, ya shahara sosai ya kan fita k'asasen kewaye dan kawo kaya, yanada mata d'aya Haj. Amina, yaransu biyu Muhsin ne babba sai Nana Aisha ita ce k'arama suna kiranta da Nana, suna zaune a Dala da gauran dutse, duk danginsu suna cikin kano da wasu kauyaku dake kewayan kano. Abba da Umma anyi musu auren had'in zumunci ne, dan wa da 'yar k'ani.
Alh. Aliyu ya rasuwa sakamon gajeriyar rashin lafiya da ya yi, wanda Yaya Muhsin shine ya cigaba da kasuwancin mahaifinsu, yayi aure sunan matar Fatima, Allah ya azurtasu da yaro namiji suka sanya masa sunan mahaifinsu wato Aliyu suna kiransa da Walid.
Nana Aisha takasance yar shekara sha takwas ta kammala secondary school dinta, Yaya Muhsin ya samo mata Admission a BUK in da zata karanta Islamic Studies.
Gidan marigayi Alh. Aliyu babbane domin a nan Yaya Muhsin yake zama da matarsa a wani part dake cikin gidan, Umma tana zaman lafiya da sirikarta, Anty Fati tana yiwa Umma biyayya sosai, tana kuma son Nana domin duk kan abinda ya shafeta ta sansu, Asalinsu Fulani ne mazauna cikin garin Kano.
****** *****
30/3/2018
*Ranar Monday*Ranar ce da Nana zata fara zuwa makaranta, ta shirya cikin goduwar bak'ar riga mai kwalliyan purple, ta sanya takalmi da jaka purple, tayi rolin da dankwalin abayan bak'i, ta d'aura a gogo a hannunta mai kalar bak'i da purple, tayi matuk'ar kyau koda fuskarta ba wani makeup, ta kammala shirinta ta kalli kanta a madubi ta saki wani lallausar murmushi ita kanta ta yaba da shigarta, ta d'auki jaka da wasu takardunta ta nufi d'akin Umma, ta samu ta idar da Sallan walaha ta risina tace cikin natsuwa.
"Umma zan tafi makaranta ki min Addu'a"
"Nana kullun cikin yi muku Addu'a nake, Allah ya sanya albarka yasa kin fara karatu a sa'a, da fatan kin rik'e hud'ubar da Yayanki ya yi miki, banda tarkacen kawaye, kiyi abinda ya kai ki"
"Umma insha Allah zan kiyaye"
"To shikenan tashi ki wuce kar kiyi latti"
Suka yi sallama ta fito ta nufi Part d'in Yaya Muhsin, ta samu Anty Fati da Walid suna breakfast.
"Laa Anty sai yanzu kuke karyawa?"
Anty Fati ta kalleta da murmushi.
"Eh mana kin san mu manya ne ai"
"uhum su manya an jijiki"
Anty Fati ta galla mata hararen wasa.
"zaki soma ko?"
"To mai da wuk'ar, ni yau ba ranar fad'a bace a guna, dama na zo yi muku sallama ne zan wuce school"
"To ba sabamba, shiyasa naga sai wani washe baki kike yi kamar an biya mini makka"
"kai Anty banda sharri"
Yaya Muhsin ne ya fito ya taddasu yaja daya daga kujerar dinning ya zauna.
"Autan Umma har an shirya kenan?"
"Eh Yaya yanzu zan tafi, ina kwana?"
"lafiya lau, dazu ai na lek'a wurin Umma na tambayaki tace kina can kina barci"
YOU ARE READING
SO NE SANADI
Short StoryShort Love Story... labari ne akan zazzafar soyayya, yaudara, son duniya, kazafi, cin amana. Soyayyar gaskiya.