05

57 5 3
                                    

*SO NE SANADI*

_Na_

*Rahma Kabir*
    (Mrs MG)

9 ~ 10

Nana tana shiga gida ta wuce d'akinta direct, tunani ya cika mata zuciya da damuwar halin da Fadila take ciki, wanka tayi ta zira doguwar riga ta wuce d'akin Umma, ta sameta zaune tana karanta wani littafi ta gaisheta ta samu wuri ta zauna tare da rafka ta gumi, cikin kulawa Umma ta kalleta tace.

"Nana meke damunki?"

Hawaye ne suka kawo idonta.

"Umma naje gidansu Fadila wallahi tana cikin matsala"

Nan ta kwashe komai ta gayawa Umma, Umma ta jinjina lamarin tayi mata Addu'a tare da cewa

"ki daina damuwa jarabawa ce, Allah yasa ta ci"

"Ameen"

Sai suka cigaba da hira.

Da dare Deeni ya kira ta a waya suka sha soyayya, sai da suka raba dare suna hira a waya daga bisani suka yi wa juna saida safe, Nana ta gyara kwanciya ta lumshe ido tana tuno irin hiran da suka yi da Deeni, k'aran shigowar massage shi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula, ta d'auko wayar ta duba, sai taga text d'in Deeni ne ta bud'e ta karanta kamar haka.

"Ke ta dabance Nana, ko sunanki naji sai na waiwaya, Wallahi ALLAH ina Sonki kuma babu wasa a cikin maganata. Urs Zahraddeen Abdullahi"

Nana ta maimaita sak'on ya kai sau goma tana yi tana murmushi, hawaye ne ya sauka kuncinta na farin ciki sai ta rubuta masa.

"Deeni sonka shi ne Sanadin Farin ciki na, nima ina Sonka ba adadi, da kai nake so na rayu"

ta tura masa bata jira amsar sa ba ta sanya wayar silent ta kwanta barci.

*********

*Washe gari*

Nana ta tafi makaranta da tunanin iri-iri akan ta wace hanya zata bi dan ta taimakawa Fadila ta cigaba da karatunta domin makiya suji kunya. Bayan sun fito lectures ta kira wayar Deeni amma a kashe duka layinsa baya Shiga, nan take taji faduwar gaba, cikin damuwa ta yini a makarantar, ba wanda ta saba da shi sai Deeni, ba tada k'awar da ta shak'u da ita sai Fadila yau gasu duka basa tare da ita, haka ta koma gida da damuwa.

Wasa gaske zazzabi ya rufe Nana, tun da ta dawo ta makale a d'aki bata fito ba, ganin hakane Umma ta sameta a d'aki kwance sharkaf cikin bargo, da sauri Umma ta isa wajenta.

"Nana lafiya?"

Tare da dafa goshinta taji zafi rau, da sauri ta ambaci.

"subhanallahi, Nana ba ki da lafiya shine zaki shuru baki fada min ba, kin zo d'aki kin kwanta kamar wata karamar yarinya, wannan ai shirme ne"

Sai ta d'agota taga tana fidda hawaye mai zafi, Umma ta k'ara rikicewa, da sauri ta fita a d'akin, ta d'auko wayarta ta kira Muhsin, bugu biyu ya d'auka, bata jira mai zaice ba tace.

"kazo yanzu Nana ba lafiya"

Ta kashe wayar. Da ya ke ya dawo yana part d'insu, da sauri ya fito Anty Fati na biye da shi, suka isa d'akin cikin tashin hankali, nan suka samesu Umma na rungume da ita. Anty Fati da Umma suka kamata aka wuce da ita asibiti. Taimakon gaggawa aka bata ta samu barci, likitan yace.

"Munyi bincike gaskiya akwai damuwa a tattare da ita wanda shine ya haifar mata da matsanancin ciwon kai, yanzu dai ta samu barci inta tashi komai zai yi dai-dai insha Allah"

Umma tayi shuru tana tuna labarin da Nana ta bata na halin da Fadila take ciki, sai ta alakanta damuwar ne ya jefa Nana cikin wannan hali, bata gayawa kowa ba ta cigaba da zancen zuci.

SO NE SANADIWhere stories live. Discover now