04

67 6 2
                                    

*SO NE SANADI*

_Na_

*Rahma Kabir*
    (Mrs MG)

7 ~ 8

*Bayan Mako Guda*

Fadila shuru bata ba labarinta, tun Nana na b'oye damuwarta har Umma ta gano ta, saida ta matsa mata kana take gaya mata damuwarta, Umma tace

"Yau in kun tashi makaranta kisa Habu ya kai ki gidansu tunda kince ta tab'a miki kwatance"

"shikenan Umma zanje insha Allah"

Nan tayi mata sallama ta wuce part d'in Anty Fati tayi musu sallama ta wuce.

A kamaranta Nana tana ta Allah Allah a k'are musu lectures ta wuce gidansu Fadila, bayan sun fito k'arfe sha biyu ta samu wuri ta tsaya ta kira Deeni ta gaya masa inda take, bai wuce minti goma ba sai ga shi, suka gaisa kana Nana ta ce zata je gidansu Fadila ne dan baza ta iya jiran sai an tashi ba.

"Ok muje na kai ki ai  nasan gidansu"

Nan suka rankaya suka shiga mota, suna hiran masoya sai dai Nana tana cikin damuwa rashin zuwan Fadila makaranta, Deeni da yaga bata son magana sai ya sanya wak'ar Umar M Sarif a radio mota *zan rayu dake zan mutu dake abadan dani dake zamu zaunaa* Nana ta juwo da fuskarta wajen Deeni suka had'a ido Deeni ya kanne mata ido d'aya, ita kuma ta lumshe ta bud'e tare da jefa masa wani kallo mai wuyar fassarawa, Deeni ya girgiza kai kana ya sakar mata murmushi, Nana ta gyara zamanta tare da jingina bayanta jikin Motan tana sauraren wak'ar, shima Deeni maida kansa yayi kan hanya tare da tuk'i a hankali, a haka har suka isa k'ofar gidansu Fadila. Yayi parking.

"Gimbiyata mun iso"

"To sadauki na"

kana ta fita ta tsaya a k'ofar gidan ta juyo ta kanne ma Deeni ido kana ta murgurda masa baki ta shige, dariya yayi sosai haryana dukan sitiyari.

"Nana ba kyaji, komai kika yi kyau yake miki, ina sonki"

Tana shiga ta tadda gidan rakwacam da tarkacen kaya, katuwar kwata ce daya ratsa tsakiyan gidan, sai d'akuna sun kai guda goma duk ciki d'ai-d'ai, simintin dake tsakar gidan duk ya farfashe, ta k'arewa gidan kallo tace a ranta.

'allai wannan gidan suna buk'atar taimako'

Yaran gidan ne suka bita da kallo suna wasan k'asa, tsayawa tayi ta rasa ina zata bi domin gidan a hautsine yake, wani yaro ne ya taso mai d'an wayo yace.

"Hajiya wa kike nima?"

Nana tad'an murmusa tace masa.

"Fadila na nan?"

Yaron ya washe baki
"Eh tana nan zo in kai ki d'akinta"

Sai tabi bayan yaron, da kyar ta iya tsallaka kwatan gidan, sun kai gabda d'akin sai ga Fadila da d'aurin kinji ta fito daga wanka, Nana ta bita da kallo tama kasa mata magana saboda yanda taga Fadila ta rame, Fadila cike da murna ta isa wajen Nana.

"laaa ukti waye ya kawo ki gidanmu? hala Yaya Deeni ne?"

Nana dai ba tace komai ba, Fadila ta kamo hannunta suka shiga cikin d'akinta. Fadila tace.

"Ukti ya naga kinyi shuru sai kallona kike yi?"

Kwalla ne ya kawowa Nana tace
"Ukti kin sani a damuwa, yau kwana bakwai kenan baki zo makaranta ba, inna kira wayarki a kashe"

Fadila ta washe baki tana dariyar yake.

"afwan Ukti rashin lafiya nayi shiyasa, kuma wayar bata hannuna ne, ki yi hak'uri kinji"

"shikenan Ukti ba damuwa, ya jikin da fatan kin samu sauki? dan naga har kin rame"

"Naji sauki sosai, ina sanya rai gobe Insha Allah zan zo makaranta..."

SO NE SANADIWhere stories live. Discover now