07

59 3 2
                                    

*SO NE SANADI*

_Na_

*Rahma Kabir*
    (Mrs MG)

13 ~ 14

Baba Yusuf yana fita ya hango Muhsin a mota, kasantuwar ya sauke gilas d'in mota, Baba Yusuf yad'an matso Kad'an yayi masa sallama, da sauri Yaya Muhsin ya amsa tare da fitowa, Baba ya mik'a masa hannu amma Yaya Muhsin soboda girmamawa sai ya nok'e hannu ya risina ya gaidashi cikin ladabi, Baba Yusuf ya juya yace.

"Mu k'arasa can inuwa ko"

Yaya Muhsin ya bi shi da kallon mamaki amma bai yi masa musu ba yabi bayansa, Baba ya zauna kan shinfid'an tabarmar da yayi, ya umarci Yaya Muhsin daya zauna, ba musu ya samu gefe ya zauna. Baba yace.

"Kaine Yayan Nana ko?"

Dam gaban Yaya Muhsin ya fad'i, ya amsa da.

"Eh Ni ne"

Baba ya cigaba da cewa.

"Nana ta gayamin komai yanzu da ta shiga, cewa kaine kake niman auren Fadila ko?"

Cike da tsoro Yaya Muhsin ya d'ago ya kalli Baba ya kuma sukuyar da kai k'asa, k'irjinsa na dukan uku-uku, yana tunanin wani amsa zai bawa wannan dattajon.

Baba yace
"Shurunka ya shaida hakane kenan, ka saki jiki dani ni ba irin sirikan nan bane masu d'aukan girma, ka d'auke ni tamkar mahaifinka kaji"

Yaya Muhsin girgiza kai kawai yayi domin cikinsa ne yake k'ugi alamar firgita da yayi, Baba yace.

"Ya sunanka? da mahaifinka kuma a ina kuke?"

Cikin dishewar murya yace.
"sunana Muhsin, sunan mahaifinmu Alhaji Aliyu, Allah yayi masa rasuwa shekarun da suka shud'e"

Nan Muhsin ya bashi tarihinsu a takaice, Baba Yusuf ya jinjina yace.

"Masha Allah, Allah ya jikansa, gaskiya nayi farin ciki sosai, domin daga ganinka d'an gidan mutunci ne, ni dai bana son yaudara, k'arya, ko cin Amana, ga Fadila nan na aminci maka ka cigaba da nema, sannan na baka nan da sati biyu ka gayawa magabatanka da suzo ayi maganar aure, dan bana son a d'auki lokaci"

Zufa ne yake ketowa Yaya Muhsin na tashin hankali, Yaya Muhsin baida abincewa domin Nana ta riga ta gama daure shi, sai yace.

"To Baba nagode Allah ya saka da alkhairi"

"To yaro Allah yayi muku Albarka, bari na kira k'anwarka saiku tafi"

Nan Baba ya mik'e ya shiga gida, a lokacin ne Yaya Muhsin ya samu damar sauke wani ajiyan zuciya da k'arfi, duk iskan dake kad'awa a wurin baya ji sai wani zafi da yake ji ta ko ina, zuciyansa ya takure da kyar yake fidda numfashi, haka ya mik'e jiki ba k'arfi yana taku kamar kwai ya fashe masa a ciki, idanunsa sunyi jajir saboda tsananin b'acin rai da rud'ani, da kyar ya isa mota ya zauna a mazaunin kusa da driver ya kunna Ac motan ko zai ji sauk'in zafin da yakeji a jikinsa. Kwantar da sit d'in yayi kana ya kwanta rigin gine ya rufe idonsa ya dafe k'irjinsa, saboda irin bugun da ya keyi tamkar zai fito waje.

Nana tana cikin wannan yanayi Baba Yusuf ya sameta cike da fa'ara a fuskansa yace

"ke Nana zo ku tafi gida yamma tayi Allah ya muku Albarka"

Jikin Nana a sab'ule tace

"Baba kun gama maganan ne?"

"eh mun gama"

"to gani nan zuwa"

Baba ya wuce cikin murna hankalinsa ne yaji ya kwanta, yana son Fadila kuma yana son tayi karatu baida yanda zai yi ne ya dak'ile mata karatun saboda ya kare mutuncinsa. Dama kullun Addu'a yake yi Allah ya kawo hanya mai sauk'i da koma zai warware cikin lumana.

SO NE SANADIWhere stories live. Discover now