09

56 3 4
                                    

*SO NE SANADI*

_Na_

*Rahma Kabir*
    (Mrs MG)

17 ~ 18

*Bayan wata biyu*

Su Nana sun soma shirin yin exam. Deeni shuru ya daina zuwa wurinta ko ta kira shi a waya baya shiga, tun abin baya damunta harya soma, kusan sati biyu kenan ba Deeni ba labarinsa, hakan ba k'aramin tada hankalin Nana yayi ba.
Ranar Friday bayan sun koma gida daga makaranta, Nana ta wuce d'aki fuska ba annuri, Umma ta kalli Fadila.

"Wai lafiya naga Nana haka?"

"Wallahi Umma na rasa me ya ke damunta tun kusan kwana biyar kenan take a cikin wannan yanayin, kuma na tambayeta tace bakomai"

"Allah ya kyauta, tashi ki shiga kicin ki duba min miya sannan ki zuba muku abinci kuje kuci"

Fadila cikin hanzari ta mik'e ta nufi kicin, tafiyarta kenan Yaya Muhsin ya shigo ya gaishe da Umma kana ya zauna yana cewa.

"Su Nana sun dawo kuwa?"

"Eh sun dawo"

Kafin ta rufe baki Fadila ta fito rik'e da plate d'in abinci kallo d'aya Yaya Muhsin yayi mata ya kauda kai, ta risina ta gaida shi ya amsa a dak'ile, kana ta ajiye plate d'in abincin ta koma kicin, goran ruwa ta d'auko da kofi ta nufi wurin da Yaya Muhsin ya zauna ta dire masa, sai ta bud'e ta zuba sannan ta d'ago ta mik'a matasa, caraf suka had'a ido, Fadila ta sakar masa murmushi mai cike da ma'anoni, kana tayi fari da ido, duk wannan abin da take yi Umma hankalinta nakan TV, jiki a sanyaye ya amsa tare da tamke fuska, yana amsa ta wuce d'akin Nana ta sameta a k'udundune cikin bargo, sai kuma sautin kukanta da yake fita a hankali, da sauri Fadila ta aje plate d'in abincin, ta nufi saman gadon tare da yaye bargon da Nana ta rufa da shi, ganin halin da take ciki ne yasa Fadila durowa da sauri ta nufi falo, cikin kid'ima take gayawa su Umma halin da Nana take ciki, ai kan ta rufe baki sun d'unguma zuwa d'akin su duka, Umma ta tallabota tana tofa mata Addu'a, yaya Muhsin yace.

"Umma Ku fito da ita muje asibiti"

Ba musu Umma ta d'agota Fadila ta kamata suka rik'eta har zuwa mota.

A asibiti likita ya auna ta ya gano tana da maleria, nan take aka d'aurata kan magani.

Abu kamar wasa kwanan su biyu a Asibiti babu wani sauk'i, saboda tsananin ciwon kai da Nana ke fama dashi ko idonta bata iya bud'ewa, hakan ya k'ara tada hankalin su Umma likita yazo ya ce su bashi wuri, haka suka fita ya rage daga Nana sai likita, gwajin hawan jini yayi mata, gwajin farko ya nuna jininta ya hau kusan d'ari da sittin, hakan ya bawa likita mamaki, yarinyar da ko 20 bata rufe ba ta samu hawan jini, sassauta muryansa yayi yace.

" 'yan mata me yake damunki wanda har ya saki a tunani da damuwa haka? ki daure ki gaya min"

Nana ta runtsa ido cikin muryan kuka tace bakomai.

"Ki gayamin gaskiya abinda ya saki a damuwa wanda yake bara zanar sanya ki cikin wani hali, kinga yanzu gashi jininki ya hau"

Da sauri Nana ta dafe kirji.

"Na shiga uku likita hawan jini?"

"Yes hawan jini shiyasa kike fama da ciwon kai sosai, amma bai hau sosai ba, ina so ki kwantar da hankalinki ki cire damuwa komai zai yi dai-dai insha Allah"

Hawaye mai zafi ya sauka a k'uncinta.

"Dan Allah likita karka bari 'yan uwa suji halin dana ke ciki insha Allah zan daina damuwa"

"Shikenan ba zan gaya musu ba amma fa sai kin daina damuwa, in baki daina ba to zan gaya musu kila su ki gaya musu damuwarki"

Da sauri tace
"Insha Allah na bari ba zan yi damuwa ba karka gaya"

SO NE SANADIWhere stories live. Discover now