*SO NE SANADI*
_Na_
*Rahma Kabir*
(Mrs MG)11 ~ 12
A cikin mota Yaya Muhsin yana tuk'i a hankali Nana na gefensa ta fad'a cikin dogon tunani, Yaya Muhsin ya waigo ya kalleta yaga tayi nisa cikin tunani, sai ya samu wuri yayi parking, Nana bata ma san yayi parking ba, Yaya Muhsin ya shafa gefen fuskanta, ta farka firgigit, cikin damuwa yace
"Nana me yake damunki? kar dai zurfin da kika yi a soyayya ya sanyaki tunani, dan d'azu Umma ta sanar dani komai"
Nana tayi murmushi.
"Yaya Muhsin soyayya ba zai sani damuwa ba insha Allah""To Allah yasa, dan gaskiya bazan jure ganinki a damuwa ba."
"Dagaske Yayana?"
"Kwarai kuwa kanwata, kullun burina in ganki cikin farin ciki"
"Dan Allah Yaya zaka min wata alfarma da zai sani farin ciki?"
"Tame fa Nana"
"Yaya Muhsin ina sonka kuma bana burin sanya ka a damuwa, in har kamin wannan alfarman to ka gama min komai a duniya"
Ta k'arasa maganar cikin damuwa, Yaya Muhsin ya jinjina kalamunta.
"K'anwata insha Allah in baifi k'arfina ba zan miki ko miye, yanzu gaya min ina jinki"
Nana ta runtse ido sai ga kwalla ya zubo mata, ai nan hankalin Yaya Muhsin ya k'ara tashi ya san lallai abu ne mai girma ke damun Nana, wanda yake zargin shine ya jefata a damuwa har tayi ciwo jiya.
"Nana kin tayar min da hankali ki gaya min damuwarki zan miki maganinta insha Allah"
Sai ta nisa.
"Yaya Muhsin so nake ka auri k'awata Fadila"Wani irin zabura Yaya Muhsin yayi yaco burki saura kadan motar dake bayansu ya buga motarsu, da yake driver kwararre ne saiya kauce musu ya wuce su, Yaya Muhsin yayi parking gefen hanya kafin ya maido da hankalinsa kan Nana ya daura fuska.
"Nana anya kina da hankali kuwa? kin san me kike fad'a kuwa? Ke da kanki kin san babu tsarin k'ara aure a rayuwata, ki yi maza-maza ki sauya tunanin ki, dan ba zan iya miki wannan taimakon ba"
Nana ta fashe da kuka.
"Dama nasan zai yi wuya ka amince, ka sani wallahi bawai dan bana son Anty Fati bane zanyi haka, ko kad'an bana burin in jefaka a damuwa, zanyi ne dan na taimakawa Fadila ta fita daga halin da take ciki"
Sai ta share hawayenta ta soma ba shi labarin Fadila, jikin Yaya Muhsin yayi mugun sanyi, yace a zuciyarsa.
'Tabbas labari ne mai kashe zuciya da tausayi, amma shi in da yana da halin taimakonta zai yi amma banda zancen aure'
Sai yayi ajiyar zuciya ya ce a fili.
"Nana kiyi hakuri, tabbas abin a taimaka mata ne amma bazan iya taimakonta ta hangar da kika b'ullo ba, sai dai zan taya ta da Addu'a Allah ya bata mafita"
Nana ta dago jajayen idonta.
"Yaya Muhsin wallahi zaka iya kuma Kaine kad'ai wanda zai iya wannan jahadin, zuciyata na gaya min kaine zaka aure ta"
Jikinsa ne ya mutu da furucin ta ya saukar da murya cikin lallashi.
"Nana ki yi hakuri ba zan iya ba, kuma daga yanzu na rufe wannan maganar"
Sai ya tada mota ya cigaba da tafiya, sunyi shuru kamar kurame ba mai yiwa wani magana sai zancen zuci da suke yi har suka isa makarantar, ya ciro kud'i ya bata.
YOU ARE READING
SO NE SANADI
Short StoryShort Love Story... labari ne akan zazzafar soyayya, yaudara, son duniya, kazafi, cin amana. Soyayyar gaskiya.