1

179 13 1
                                    

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

*YESMEEN*
 
     *©Ummyn Yusrah*

_Wannan littafin gabadayanshi sadaukarwa ce ga ƙawata Yesmeen Tafisu, alkharin Allah ya isar miki a duk inda kike._

_Tsokaci_
_Wannan littafi mallaki na ne, ban yarda wani/wata ta juyamin koda kalma guda ne daga ciki ba, ba tare da amincewa ta ba, yin hakan laifi ne babba a gareni, fatan za a kiyaye._

_1_
          

Babbar motoce ɗauke da d'alibai, kowacce ka ganta cikin farin ciki take na murnar kammala makarantarsu ta Sakandare. Kallo ɗaya zaka yi wa motar ka ƙara tabbatar da cewar ta makaranta ce, sakamakon rubutun da aka yi a jikin motar kamar haka:  Gov't Girls College Bauchi (G.G.C.B).

Ɗalibai ne da yawa wanda suka fito daga wasu jahohin ƙasar nan, an daukosu ne don kai kowacce jaharta.

Duk da farin ciki da murnar da suke yi na kammala karatu, da murnar komawa gida, gefe guda kuma, baƙin cikin rabuwa da juna suke yi, domin kafin yanzu ba ƙaramin barnar hawaye aka yi ba, duk don nuna kewa da rabuwa da juna.

Rabuwa ce da ba  lallai a sake gamuwa da juna ba, wasu an rabu kenan har abada, wasu kuma sai dai labari.

Daga gabas motar ta doshi yammacin gari, don yi wa garin Jos tsinke. Dukkanin ɗaliban garin ba su wuce mutane bakwai ba.

Dukkanninsu tsoro da fargaba ne mamaye a zuciyarsu, tunaninsu wani hali zuwa yanzu garinsu yake ciki, yaya iyayensu, ƴan uwa, da dangi suke ciki a yanzu?

Matashiyar budurwa ce zaune a kujerar baya, kusa da taga, madadin taya ƴan uwa murna da waƙe-waƙe, damuwa ce fal! Fuskarta, tunda suka doshi garin na su na Jos gabanta ke ta tsananta faɗuwa. Tsoro sosai take ji, tunda labarin faɗar da ake yi a garin nasu ya riskesu, ta kasa samun natsuwa.

Duk wani bidiri da ake yi, ido kawai take bin ɗaliban da shi, har kawo yanzu.

Jin hayaniyar ya yi mata yawa ne, ya sanya ta sanya hannunta na haggu a jikin gilashin motar, ta kifa kanta a kai, yayin da zuciyarta ta ci gaba da yi mata saƙe-saƙe. A haka dai tafiyar su ta miƙa.

Tunda suka shigo garin, ba wani hayaniyar mutane, sai ƙonannun, gidaje, shaguna, da motoci.
Gari mai tarin jama'a da kasuwanci, a yau ya zama tamkar kufayi, garin da kana shigowa za ka fara arba da jama'a, yau sai ɗai-ɗaiku da tarin jami'an tsaro, tamkar barikin sojoji.

Tun daga nan fa jikin ɗaliban da a da suke shewa da waƙe-waƙe ya yi sanyi, tamkar waɗanda aka yi wa wanka da ruwan ƙanƙara.

Ba wani kuzari a tattare da ɗalibai mazauna garin, haka suka fito daga cikin motar, ƴan uwa na basu haƙuri da fatan samun ƴan uwa cikin ƙoshin lafiya.

Suna gama sauke kayansu, direba ya ja, suka lula, gudun kada tsautsayi ya ritsa da su suma.

Sunfi awa guda suna tsayuwar jiran abun hawa don kai su gidajensu, amma ba kowa. Gajiya suka yi da jira kowacce ta d'aura d'amarar takawa da kafafunta, duk da tazarar da ke tsakanin tashar da aka saukesu da gidajensu, hakan bai sa sun hango nisan ba, fatansu kawai su isa ga ƴan uwansu.

Haka suka rabu daga wajen ba tare da wani cikakken sallama ba. Yesmeen da tun a moto ba ta da wani kuzari haka ta kwashi kayanta ta yi gaba itama, tunda ta ɗau hanyar unguwarsu, ba ko gilmawar mutum ɗaya, sai tarin jami'an tsaro, suma tsabar tsoro, ta hangosu take boyewa, sai sun bace wa ganinta sannan ta fito. 

Tafiya mai nisa ta yi, kafin ta haɗu da wani mutumin, tsoro sosai ta ji, lokacin da taga ya doso inda take, sai dai ganin yanayin shigarshi ya sa, wata zuciyar ta yi mata nuni da ba mai cutar wa ba ne, ɗaya sashen kuma ya tunatar da ita cewar, 'Mugu bai da kama.'
Koda ya iso daf! Da ita ya  tambayeta, ina  ta fito? Ina kuma za ta je? Bayan ta sanar da shi ne, ya jinjina zancenta tare, da sanar da ita irin ta'adin da aka yi a unguwarsu ( Unguwar Rogo), kwana uku da suka wuce, cikin dare, faɗar kabilu ya tashi, inda aka yi ta banka wa gidajen musulman da ke unguwar wuta.

Tun tana fahimtar abin da yake cewa, har jinta ya ɗauke. Ba ta tsaya jin ƙarshen zancen ba, ta ɗau hanya.

Sauri take bata ma san inda take jefa k'afarta ba, burinta kawai Allah kaita gida lafiya.

Abin da ta gani ya mugun firgitata, gabaɗaya gidansu ya k'one, ba alamar wani abun amfani, ko rai mai motsi.  duk da gidan nasu tamkar unguwace guda don duk danginsu na cikin gidan sai k'alilan da suke wani garin,don mafi yawansu auren dangi suke kuma duk wanda zai yi aure cikin gidan yake zama. Sai matan da suka auri bare ne suke fita, suma kuma ba su fi mutum uku ba.

Duniyar ce ta shiga juya mata, gabaɗaya jiri ne ke ɗibanta.

_Ummyn Yusrah_
     _2020_

YESMEENWhere stories live. Discover now