*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*YESMEEN*
*© Ummyn Yusrah*
2
Salati kawai take, tare da zagaye dukkanin ƙonannun sassan gidan, ba wani ɗan adam mai rai, sai ma ƙonannun gawarwakinsu. A hankali take tafiya da baya-baya, ji ta yi ta yi karo da wani abu, madadin tsoro ya ziyarci zuciyarta sai fatan Allah ya sa mutuwar ta ce ta zo saukarwa. Rintse idanunta mai tsiyayar da ruwan hawaye ta yi, jin shiru na ɗan lokaci, ya sa ta juya, arba ta yi da ƙonannen motar mahaifinta, take ta sanya wani irin kuka mai tsuma zuciya, lokacin da ta tuno yadda suke rige-rigen shiga gaban motan, da ƴan uwanta idan za a kai su makaranta ko zuwa wani waje. Ganin abun take kamar yanzu yake faruwa. Babu Abba, babu sauran yara, gwangwamin motar da wuta ya gama cinyeta. Gefe kuma, mashin ɗin yayan babanta ne, shi ma da ya sha wuta duk ya k'one. Wani sabon kuka ne ya sake kwace mata, da gudu ta koma cikin gidan.
Sassa kusan goma ne cikin gidan, amma duk angama da su,wasu sassan da wuta bai kama suba, jini ne kwance a wajen ya bushe. Kura wa jinin idanu ta yi, tana nunanin wannan duk jinin ƴan uwanta ne. da gudu ta juya tabar wajen, ta nufi sassansu, ba wani abu cikin shi, komai ya ƙone. Cike da mamaki ta nufi lokar da suke ajiye littattafan da ya shafi addini da alƙur'ani, duk sun ƙone, sai dai ƙur anan da ke ciki ba abun da ya samesu, sai ɗan gefen da ba rubutu.
A hankali ta motsa laɓɓan bakinta, ta na mai kalmar shahada. Sai ta kuma sanya kuka, wajen ta d'urk'ushe rungume da ƙur'anan.
Ji take kawai ina ma azo a sake cinna wa gidan wuta, ko ita ma su yi gunduwa-gunduwa da ita ta huta, don a yanzu ba ta ga amfanin cigaba da rayuwartaba.
"Na rasa, yaushe garinmu zai sami zaman lafiya?
Yaushe za daina irin wannan kashe-kashen?
Yaushe za a daina mai da mata zaurawa?
Yaushe hankulan magidanta zai kwanta, su rayu cikin iyalansu, su daina gudu jeji suna kwana?
Yaushe za a daina mai da yara marayu? Marasa yanci, da galihu? Ba mai kula da su, sai dai aɗebe su a kai su gidan marayu a jibgesu, ba mai kuma waiwayensu, bamai ba su wadataccen ci, sha, sutura, uwa uba Ilmi.
Yaushe za su rayu su zama manyan gobe da ake yi musu ikirari da shi?
Ina masu faɗa aji, da hukumomi? Haka rayuwarmu za ta ƙare, sai bayan an gama yi mana illa, sannan jami'an tsaro su zo?
Saboda rashin kayan aiki, har ƴan ta da zaune tsaye sun fi hukuma makamai? Wannan wacce irin rayuwa ce ya Allah? Allah ka dubemu, ka kawo mana dauki badon halayyarmu ba, domin darajar fiyayyen halitta."Maganganu kawai take ita kaɗa tare da tarin tambayoyon da ba su da amsa.
Lokaci maitsawo ta ɗauka durƙushe a wajen, tana tunanin wani irin rayuwa zata yi a yanzun? idan ta ce Bauchi za ta koma wajen k'anwar babanta wazai bata kuɗin moto? Ina za ta sami moton ta shiga? Tunda har yanzu ba wai an buɗe hanya sosai ba ne. Ko dai tazauna nan cikin dare ita ma cikin dare azo a kasheta ne?
Zama ta yi tare da ɗora kanta cikin cinyoyinta, ta cigaba da saƙe-saƙe. Daga nesa take jin maganganun mutane, idan kuma ba ƙarya kunnuwanta suka yi ba, kamar cikin gidan aka shigo, yadda take jin tafiyar manyan takalma, tasan masu ƙarasata ne, sai kuma ta ji duk jikinta ya yi sanyi, ko yatsar hannunta ba ta fatan ya motsa balle har ta je ga ɗago kanta ta ga yanayin halittar makasanta. can ta ji wani daga cikinsu ya ce "Ga ci can cege."
cikin wani irin gurb'atacciyar Hausa.Ƙara tura kanta ta yi cikin cinyoyinta, tare da ƙanƙame Ƙur'anan da ke hannunta bisa ƙirjinta mai barazanar faɗowa ƙasa don tsoro.
Madadin ta ji an ajiye bindigar da zai ragargaza kanta, hannu ta ji ya dafa ta, tare da rungumota, lokaci guda kuma sai kuka.
A hankali take ɗago kanta sai dai har yanzu idonta rufe yake, har ta gama ɗagokan, ba ta buɗe idon ba illa hawaye dake gangarowa bisa ƙuncinta, wacce ta rungumata ta ce,
"Yesmeen! buɗe idonki ni ce."*Ummyn Yusrah*
_2020_
